Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction)

1
68

Ma’aurata kunsan ciwon sanyi da rashin  tsafta suna matukar sa rashin sha’awan jima’i kuwa? Suna hana jituwa tsakanin mata da miji. Kuma komi iya kwanciyarki da cushecushen kayan mata inbaki magance infection ba akwai matsala. 

Irin wannan infection din yana hana jin dadin jima’i,yana hana daukar ciki,yana kuma cutar da maigida ya cutar da abokiyar zama ma inba ke kadai bace.

Domin akan sami amarya me tsafta, yayin da uwargida kuma ƙazama, ko kuma uwargida me tsafta yayin da amarya kuma me ƙarancin tsafta… wanda illar infection shine idan mijin zaijewa waccan me ƙarancin tsaftar kuma kema yazo miki toh duk ƙoƙarinki tsaftarki bazaki tsira ba sai dai abun yai miki da sauki.

Alamomin Sun Hada Da
  • Ɗaurewar mara akai akai ba lokacin period ba
  • Jin motsi kamar wani abu na tafiya acikin farji
  • Jin zafi yayin fitsari
  • Jin zafi yayin saduwa
  • Ganin fitar farin ruwa me kauri
  • Ganin fitar abu kamar dusa-dusa daga farji
  • Jin discharge na fita da karni kamar karnin kifi ko ɗoyi
  • Kai kayin gaba
  • Gani kurji ko kumburi a gaba.

Al’amarine me nauyi amma kar ai kunyar zuwa ga likita neman lfy,wasu na dashi amma sam basusan menene ba sai daga baya in abun yayi yawa,wasu kuma basa ganin discharge din komi saide ciwon mara…. shima maganin dinsa daban. shi yasa ko yaushe nake cewa aje  ƙwararrun jami’an lfy.

Ga jami’an lafiya musamman ƙananu kusani vaginal infection ya kasu iri da yawa akwai viral,bacterial,fungus da parasitic don haka wajibi ne ka fahimci meke jawosa kafin dora mutum a magani,ba duk infection ne ake bada antibiotics ba,akwai infections din da inka ba mace antibiotics ka kara haukatashi ne.

Sannan kuskure ne dora mutum akan babban antibiotics wato broad spectrum antibiotics akan ƙaramin abunda bai kai ya kawo ba,hakan kuma kan jawowa jikinsu yai developing antibiotics resistant ta yadda zaima ki aiki nan gaba in wata cutar ta samesu,a kiyaye narrow spectrum sune first line ko yaushe na antibiotics. 

Don haka wajibinku ne ku fahimci abunda ya jawo infection din da kyau kafin bada magani,shi yasa manyan asibitoci wasu sai mun dau sample na discharge din mun turawa masanan kimiyya wato medical lab scientists sun tantance mana domin dora mutum kan maganin da ya dace dashi.

Sannan yana da kyau jami’in lafiya yasan waɗanne irin tambayoyi ya dace yai da kuma sanin dalilin yin su,karkurum mace tazo da complain, kai kuma ka saki layi ka tafi wata tambayar can mara mahimmanci  da  bata da alaqa da matsalarta… daga lokacin bazata kuma dawowa gurinka ba domin zata fahimci kaima din bakasan komi ba. 

Sannan ku dai na jin haushi don an muku tambaya kusani ayanzu ƴancin mara lafiyar da yazo gabanka ne.. ya tambayeka daya bayan daya game da maganin daka rubutamasa, kai masa bayani kuma har sai ya gamsu, sannan yana da hakkin ka sanar dashi damuwarsa matuƙar akwai buƙatar hakan domin yasan abunda zai kiyaye…. Don haka batun wani harden rubutu a likitanci yanzu bashi. Kai rubutun magani straight and clear shine sanin aiki.

Don haka jami’in lfy a duk sanda mace ta zoma da korafi na alamun infection ne ke damunta baya ga magani karku mance da bata wadannan shawarwarin da zan lissafo; sune ginshikin cin nasara wajen magancesa. Ku sanar da ita cewa;

1. Zaifi kyau ki riƙa sanya pant na cotton bana roba ba. Sannan a rika canza pant din sau 2, 3 zuwa 4 a rana a irin wannan yanayin. Dalilin shine farji ba gurine da iska ke ratsawa ba ko yaushe sanya panta na roba karawa gurin danshi zaiyi… danshi ko yanayi ne da irin wadannan kwayoyin cutar keso. 

2. Duk sanda zaki wanke unders dinki kike amfani da ruwan dumi kina wankewa dashi, inkuma ruwan na sanyine to a zuba gishiri aruwan wankin kadan domin kashe wasu ƙwayoyin cutar koda akwaisu ajiki. Sannan idan da  hali ake shanyasu acikin daki ko ida akasan ƙurar ƙasa bazatake tasowa tana badesu ba kafin su bushe.

3. Sannan akiyaye kai hannu wajan farji,  yana dakyau hannu ya zamto anwankeshi kafin a shiga bayan gida koda babu datti da kuma bayan anfito.

4. Kar kike tura sabulu yayin wanke farji zuwa ciki, inda hali ma sam babu buƙatar sabulu wajen wankesa domin gurine dake wanke kansa da kansa, shyasa wani lokacin kina zaune kurum sai kiga abu me yauki na fita. 

Sannan ake aske gaban fes duk bayan sati 4 ko 6. Amma akeyi sama-sama, sannan ba direct ba, ko yaushe kafin ki askin ki sami ruwan duminki ki zuba a roba kikai bandaki inkinje ki zauna aciki na minti 5 zuw 10 tukun kafin fara shaving din saboda yin hakan zai hana kuraje da kaikayi…. bama sai me infection ba ga dukkan maza da mata ya dace kuyi hakan. Idan da hali a sa gishiri cikin ruwan dumin kafin azauna ciki.

5. A tabbatar da tsafta bandakuna pls, Ake kaɗa ruwa da gishiri ko da Omo ana watsawa acikin bandakin ana wankesa, ko ta hanyar amfani da sauran maganin kashe kwayoyin cuta na ruwa.

6. Ake tsarki da ruwan dumi zaki iya dumamawa ki zuba a cikin flask duk sanda zaki kama ruwa sai ki tsiyaya in kina gida. sannan anaso ake sa gishiri daidai misali a ruwan dumin da za’ake tsarkin. A daina tsarki da ruwan sanyi sam idan da hali amma inba yadda Za’ai to shima asa gishiri kadan ciki. Ko namiji inda hali inkana gida ka jimanci tsarki da ruwan dumi.

7. kike canza fant yayin period akalla Sau 3, xuwa 4 a rana, insun Jima koda basu ɓaci da jini ba. Saboda jinin al’ada. ne me kyau dake ba ƙwayoyin cuta damar rayuwa…

8. Matsayinki name fama da infection Idan da hali inke kadai ke kwanciya adakinki ki rika cire pant dinki inzaki kwanta ki bar iya siket yadda iska zatake ratsawa zuwa wayewar gari ki rika haka kullum har matsalar ta tafi.

9. Karka mance duk matar auren da tazo da Infection wajibi ne mijinta ma adorasa a magani daidai da irin nata, hakama insu 2 ko 4 ne wajen mijin kaf dinsu sai sunsha maganin daidai da nata.

Inde an kiyaye wannan Insha Allah za’a samu sassauci akan kari, magani kadai babu counseling a infection baya aiki… abun dadin ma yawancin magungunan infection ma wani sha sau 1 ne shikenan wani kuma sau 2 anjima anayi kwana 5 saide in ansami treatment failure. Fatan harma wadanda basu dashi sun ilmantu.

Domin karanta bayani akan sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i Danna nan

labarin da ya wuceSanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i
Labarin na GabaCiwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure)

SHARHI ƊAYA