Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa da shi ne ta hanyar jima’i wato. Mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu’amala da wasu mazan. Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yana da mata sama da ɗaya ko kuma idan yana neman mata.
Namiji ba kasaifai yake ganewa yana da wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana dashi.
Amma Idan Anyi Sa’a Ya bayannana Cikin Namiji Akwai Alamomin Kamar Haka;
- Jin zafi wajen fitsari
- Jin zafi bayan fitan maniyyi
- Fitar farin ruwa kaɗan
- Ƙaiƙayin gaba
Alamomin a Jikin Mata
- Ƙaiƙayin gaba
- Jin zafi wajen fitsari
- Warin gaba
- Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass.
- Kwailewar farji
Amma akwai wasu ɗabi’un da mata keyi hakan na jawo shi wannan ciwo na sanyi wato (infection)
-
Yanayin tsaftace farji:
Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shi ne dai dai. Kaninfari da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami,medicated soaps da sauransu.
Wanann ba tsaftaceki za suyi ba, hasalima kina ƙara ɓata halittar farjinki. Kaman yadda mukayi bayani a baya ga me da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka er uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.
-
Yanayin wanke dubura bayan:
kinyi bayan gida: Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shi ne ki fara daga gaba zuwa baya, ma’ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka suke yi. Wannan ɗabi’ar sam bata da ce ba. Idan kika fara daga baya kina ɗebo ƙwayoyin cutar da ke cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba. Shi farji baya san baƙon abu a tattare dashi.
Domin karanta Larurar Sanyin Gaba Wato Genital Infaction Ko Ciwon Hanta danna koren rubutun nan