Yadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga

0
131

Kafin yarinya ta balaga tana iya fuskantar wasu canje-canje a bangarori na jikinta. kadan daga cikin hanyoyin da zata bi wajen kula da kanta 

Sune:

1.AMFANI DA TURARE

A lokacin da mace take wannan mataki idan ta lura zata yawaita yin gumi,hakan zaisa tana fitarda wasu sinadarai Wanda yake dauke da wari wani lokaci. Hakan yasa take bukatar turaren jiki (na hammata). Akwai turaruka dayawa a kasuwa zaki iya duba Wanda kamshinsa yayi Miki Kuma dai-dai aljihu da taimakon iyaye ko nagaba dake.

2.YIN WANKA AKAI-AKAI

Idan mace takai wannan matakin hatta gashin kanta kanta yakanyi gumi da wani maiko,hakan yasa Ana da bukatar wankeshi akai-akai da man wankin kai sannan ayi wanka a qalla Sau biyu.

Yana dakyau ku karanta bayani akan Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2)

3.MAGANCE KURAJEN FUSKA

yawancin Mata suna fuskantar canje-canje Wanda ya hadar da fitowar sabbin kurajen fuska (pimples)Hakan yasa a shawarce yarinya tana bukatar kula  da fuskarta da mayuka da Kuma sabulai masu inganci.

4.ASKE GASHI

Daga cikin babbar alama ta balagar mace shine fitowar gashi daga wasu bangarori na jikinta(Hammata,Gaba,sangalalin Hannu da Kafa). Wannan gashin ba abun gudu bane ko tsoro don kowwa Yana dashi idan mutum yakai matakin. Amma a shawarce anaso yakasance ana askeshi lokaci zuwa lokaci da rezar aski ko man askewa(shaving cream).Amma qalubalen shine bayan askin wasu suna fuskantar qaiqayi da kananun kuraje ko gurin da aka aske yayi duhu.Saboda haka Yana da kyau duk ‘yan matan da suke wannan mataki su dinga neman shawarar iyayensu ko nagaba dasu.

Domin karanta Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada Danna nan 

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Tara: Hematology (Jini da Abubuwan da ya ƙunsa )
Labarin na GabaYadda Ake Alwala
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.