Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada

0
408

Da yawa mata idan sun fara al’ada, kunya suke ji su bayyana, wasu da dama basa iya faɗa wa iyayensu ko kuma wasu manya ko kuma makusanta.

A wannan shafin namu, zamu bayyana yadda zaki cire kunya, ki faɗa wa iyayen ki; ko wasu manya da zasu baki shawara dangane da yadda zaki fuskanci matsalar.

Ga kaɗan daga cikin irin tambayoyi da amsoshin su:

1. Wa zan tunkara dangane da canjin da na fara fuskanta a jiki na?

Yanayin da kike fuskanta dangane da canjin jikin ki ba abu bane mawuyaci. Idan kina da tambayoyi akan canjin jikin ki, ko yanayin al’adarki; yana da matuƙar muhimmanci ki fito ki bayyanawa mahaifiyyar ki ko yayyan ki ko malamai; kokuma wasu manya da kika sani, don su ɗora ki akan hanyar da ta fi dacewa da ke.

Duk wacce kika gani ta wuce shekarun ki, to tabbas ta ɗanɗana irin abinda kike fuskanta a yanzu; kuma koda ace basu sani ba, zasu ɗora ki akan tafarkin da zaki fahimta, ko kuma suhaɗa ki da waɗanda suka sani.

2. Ya zan yi idan na kasa tunkarar iyaye na?

Jin kunya wajen tattauna maganar da ta danganci al’ada ga iyaye, ba abu bane maiwuya. Yawancin mutane sun fuskanci irin haka, kuma suna son ki; kuma suna son su taimake ki. Su kansu iyaye; zasu ji daɗi idan kika fuskance su da irin wannan maganar. A lokacin zasu ƙara baki kulawar da kike buƙata, su ƙara nusar dake me rayuwar ta ƙunsa.

Wasu lokutan yana da muhimmanci ki tanadi tambayoyin da zaki yi musu, don ki samu amsoshin su a lokaci ɗaya.

Gakaɗan daga cikin yadda zaki iya fara tattaunawar:

  • Zaki iya yin alama da ido, ko kuma zirga-zirga a gaban su, don su fuskanci kina da magana; daga nan su da kansu zasu tambaya, su ce, “LAFIYA”; a nan zaki matsa kusa dasu, sai ki fayyace musu abin da ke birnin zuciyarki baki ɗaya.
  • Idan kin san sun riga da sun sani; zaki iya zuwa gurin su, kice kina jin ba daɗi ne, shi ne kike son ki tattauna matsalar dasu ko akwai mafita.
  • Kiyi tunanin tambayoyin da kike son yi, ki rubata su a takarda, ki tabbata babu wasu-wasi a zuciyarki; sai ki basu takardar, su zasu neme ki.
  • Idan kuma baza ki iya yi wa iyaye magana ba, zaki iya samun yayar ki, ko kaka ko malaman islamiyya ko manya a jihar, ko kuma ki ziyarci asibiti.

3. Ta yaya zan san lokacin da ya kamata na ziyarci asibiti?

Lokuta da dama, yana da wuya a tattance in kina da lafiya ko akasin haka; ta yaya zaki san ya kamata ki tattauna da likita?

Muhimmiyar hanya ita ce, ki fara tattaunawa da iyaye ko kuma yayyan ki ko manya da kika yarda dasu. Sun ɗanɗana dayawa daga cikin abubuwan da kike fuskanta yanzu, don haka, zasu baki shawarar da takamata.

Idan baki da likita, zaki iya zuwa ɗaya daga cikin asibitocin da ke kusa da ke (ƙwararru), kuma karki manta asibiti basa son tambayoyi marasa ma’ana, don aikinsu shine; su taimaka wa al’umma.

Babu wanda ya kai likita riƙe sirri, don haka, kar ki ji kunyar faɗa musu abubuwan da ke damunki, don su zasu taimaka miki sosai.

Bin ƙa’idojina da matuƙar muhimmanci, don su za su taimaka wajen ƙara koyar da ke abubuwan da ya shafi jikinki.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Jinin Haila (Jinin Al’ada) danna nan.

Don shiga WhatsApp Group ɗinmu na Tsaftar Mata, ku danna nan.

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke Hana Karɓar Gaskiya
Labarin na GabaYadda Al’ada (Jinin Haila) Yake
Zainab Muhammad
Sunana Zainab Muhammad, nayi karatun firamari a Bennie International School Kano, sannan nayi secondary a Sheik Bashir El-Rayya school complex kano, yanzu ina yin digiri dina a jami'ar Federal University Dutse dake Jigawa, ina mataki na uku.