Ciwon Hanta (Hepatitis B)

0
841

Hanta, ɗaya ce daga cikin sassan jikin ɗan adam. Kuma jigo ce wajen kula da tafiyar da jikin ɗan adam. Mutum ba zai iya rayuwa babu hanta ba. Abubuwa da dama suna iya janyo ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.

Akwai ciwon hanta mai tsanani da mara tsanani. Akwai mai dogon zango da mai gajeran zango. Kuma kowanne daga cikin nau’o’in ciwon hanta zai iya kashe mutum.

Amfanin Hanta

Amfanin hanta yana da yawa a jiki, amma ga kaɗan daga cikin su:

1. Sarrafa abinci: Hanta tana kula da daidaituwar abinci a jiki. Misali, idan mutum ya ci shinkafa mai yawa, hanta ce take sarrafa abincin domin a ajiye shi zuwa wani lokaci.

2. Sarrafa magunguna: Hanta tana taka rawar gaske wajen kula da shige da ficen magungunan a jikin ɗan adam.

3. Samar da sinadarai: Hanta tana samar da sinadaran da jiki yake buƙata wajen yaƙar cututtuka da kuma samar da zaman lafiyar jiki. Sinadaran sun haɗa da: bile, plasma proteins, clotting factors da sauransu.

4. Fitar da datti; Cututtuka da sinadarai marasa amfani daga jiki kamar su ammonia, billurubin da sauran su.

Abubuwan da suke janyo ciwon hanta

1. Ƙwayar cutar Virus: Kamar Hepatitis (A, B, C, D da E) virus, cytomegalovirus (CMV), Epstein-Barr virus da sauransu.

2. Shan giya: Giya tana janyo cututtuka iri daban daban a jikin ɗan adam, daga ciki har da ciwon hanta.

3. Shan magunguna barkatai: Wasu daga cikin magungunan da muke amfani da su, suna iya janyo ciwon hanta musamman idan ana shan su ba bisa ƙa’ida ba.

Abubuwan da suke janyo ciwon hanta suna da yawa. Amma zan yi bayani a kan ciwon hanta wanda ƙwayar virus ta Hepatitis B take janyowa.

Ciwon hanta na Virus ɗin Hepatitis B:

Mutane da dama a Nigeria suna ɗauke da wannan ƙwayar cutar. Wasu sun san suna da ita, da yawa ba su san suna da ita ba. Virus ɗin Hepatitis B tana iya lalata wa mutum hanta, tana janyo ciwon hanta mai tsanani kuma tana iya janyo cutar dajin hanta (cancer).

Yadda ake ɗaukar ƙwayar cutar Hepatitis B Virus

Virus ɗin Hepatitis B tana shiga jikin mutum ne ta hanyar cakuɗuwar jinin mai ɗauke da virus din da jinin wanda ba shi da cutar. Misali:

1. Yankewa: Idan wanda yake ɗauke da ƙwayar cutar Hepatitis ya yanke da abu mai kaifi (kamar reza, wuƙa, aska, almakashi da sauransu), to duk wanda ya yi amfani da wannan abu mai kaifin, kuma shi ma ya yanke, to virus ɗin za ta iya shiga jikinsa.

2. Ƙarin jini: Idan aka ƙara wa mutum jini mai Hepatitis, to zai iya ɗaukar virus ɗin.

3. Jima’i: Wanda yake da Hepatitis B Virus zai iya shafawa wanda ba shi da ita a lokacin jima’i.

Yadda ake samun kariya daga cutar Hepatitis B virus

1. Rigakafi: Akwai allura da ake yi domin samun kariya daga kamuwa da cutar Hepatitis B virus. Ana yin allurar ne sau uku, a tsawon wata shida. Idan aka yi wa mutum rigakafin, zai samu kariya mai yawan gaske.

2. Kaucewa amfani da abu mai kaifi: A yi ƙoƙari wajen kaucewa amfani da duk wani abun da zai iya yankar mutum. idan kuma lallai sai anyi amfani da abu mai kaifi kamar lokacin yanke farce ko aski da sauransu, to kowa ya yi amfani da nasa shi kaɗai. A daina yi wa mutane aski ko yankan farce da abu guda ɗaya.

3. Gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus: Yana da kyau mutum ya je a yi masa gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus domin ya san ko yana da ita ko ba shi da ita. Idan ba shi da ita, sai ya je a yi masa allurar rigakafi. Idan kuma yana da ita, sai ya yi ƙoƙari wajen kaucewa yaɗa ta.

4. Kaucewa taɓa jinin mutum: Taɓa jinin wanda yake ɗauke da virus ɗin Hepatitis B ba tare da safar hannu ba, za iya janyowa a ɗauki cutar musamman idan akwai ciwo (komai ƙanƙantar sa) a hannun.

5. Tantance jini kafin ƙara wa mutum: Masu aiki a ɗakin gwaje-gwaje da ɗaukar jini, su tabbata sun yi gwajin Virus ɗin Hepatitis B da ma wasu cututtukan kafin su ɗauki jinin mutum.

Alamomin ciwon hanta na Hepatitis B virus

Idan virus ɗin Hepatitis B ta shiga jikin mutum, ba lallai ya ji wata alama ba, kuma ba lallai ya san ya ɗauki cutar ba. Amma wani lokacin, cutar hanta tana iya nuna waɗannan alamomi idan ta shiga jikin mutum;

• Zazzaɓi
• Kasala
• Ciwon ciki
• Canjawar ido zuwa launin rawaya (yellow) ko kore
• Ciwon jiki da sauransu
Bayan waɗannan alamomin na ɗan wani lokaci, virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum ba tare da ta janyo masa wani abu ba.

Rayuwar Hepatitis B Virus a jikin ɗan adam

Idan cutar Hepatitis B virus ta shiga jikin mutum, ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan za su faru:

1. Ƙwayar virus ɗin za ta iya janyo wa mutum ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.
2. Ƙwayar virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum na tsawon lokaci ba tare da ta janyo masa ciwon hanta mai tsanani ba, amma zai iya yaɗa cutar.
3. Ƙwayar virus ɗin za ta iya mutuwa da kanta ba tare da an sha mata wani magani ba.

Alamomin ciwon hanta mai tsanani sun haɗa da:

• Kumburin jiki, musamman ciki da ƙafa
• Aman jini
• Yin kashi baƙiƙƙirin kamar kwalta
• Ramewa
• Fita daga hayyaci

Maganin Hepatitis B virus

A likitance, babu magani guda ɗaya wanda yake kashe virus ɗin. Amma akwai wasu magunguna da ake ba wa mai cutar domin rage ƙarfin tasirin ta a jikinsa. Ba a bayar da maganin sai mai cutar ya cika wasu ƙa’idoji da sharuɗa.

Idan mutum bai cika waɗannan ƙa’idoji da sharuɗa ba, to ba za a rubuta masa maganin ba. Zai ci gaba da gudanar da rayuwar sa kamar yadda ya saba. Sai dai kawai zai dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci domin kula da ci gaban cutar.

Shawarwari ga masu ciwon Hepatitis B virus

• Za ka iya ci gaba da gudanar da rayuwarka cikin ƙoshin lafiya duk da cewa kana da Hepatitis B virus. Amma akwai buƙatar a dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci.

• A Kaucewa yaɗa cutar ta hanyar daina yin amfani da abubuwa masu kaifi na kowa da kowa kamar su almakashi da reza da abin yankan farce da sauransu.

Wasu abubuwa da ake alaƙanta su da ciwon hanta

1. Shan rake: Shan rake ba ya maganin ciwon hanta ko wane iri ne.

2. Sinadarin abinci mai gina jiki (Protein): Mai cutar Hepatitis B virus, zai ci abinci kamar yadda kowa yake ci. Babu abin da zai hana shi cin abinci mai gina jiki kamar su nama, kifi, ƙwai, gyaɗa, wake da sauransu.

Idan mutum yana da ciwon hantar da ya janyo masa rashin lafiya mai tsanani, ana buƙatar ya rage cin abinci mai gina jiki (protein) ya kuma yawaita cin abinci mai sa kuzari kamar su tuwo, shinkafa, doya da sauransu (Carbohydrate).

A kula sosai, ban ce a daina cin mai gina jiki ba, cewa na yi ya rage. Kuma ba a ce ya dinga shan rake ba, cewa aka yi abinci mai saka kuzari.

Wannan bayani an samo shi ne daga Hamisu Adam Abubakar.

Domin karanta Ciwon Suga (Diabetes) danna nan.

labarin da ya wuceDUNIYA MAKARANTA!
Labarin na GabaCikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa