Ciwon Suga (Diabetes)

0
516

Ciwon suga sinadari ne mai matuƙar amfani a jikin mutum. Ana samun sa daga abincin da muke ci da kuma abubuwan da muke sha.

Idan suga ya yi yawa, ko kuma ya yi kaɗan a jikin mutum, ana iya kamuwa da rashin lafiya wadda za ta iya sanadiyar mutuwar mutum idan ba a ɗau mataki ba.

Akwai wani sinadari da ake kira insulin a jikin ɗan Adam. Sinadarin insulin shi ne yake kula da daidaituwar sinadarin suga a cikin jini. Idan mutum ya ci abinci mai dauke da sinadarin suga (carbohydrate), sai sugan ya koma cikin jini bayan ya narke. 

Sai sinadarin insulin ya zo ya daidaita suga, domin kada sugan ya cutar da jiki. 

Ma’anar ciwon suga, cuta ce wadda take faruwa sanadiyyar ƙaruwar yawan sinadarin sikari (suga) a cikin jini na tsawon lokaci. Cutar tana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin, ko kuma insuin ɗin ya daina aiki gaba ɗaya.

Rabe-raben Ciwon Suga

Rabe-raben ciwon suga suna da yawa, amma za mu yi magana a kan guda uka kawai:

1. Type I Diabetes

Wannan nau’in ciwon sugan, yana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin.

Idan sugan  mai wannan nau’in ciwon sugan ya ƙaru, ba zai sauka ba, saboda babu insulin. Idan kuwa ana so ya sauka, to dole sai an yi allurar insulin.

Wannan nau’in  ya fi kama yara. Haƙiƙanin abin da yake janyo wannin  nau’in ciwon ba a san shi ba, amma dai an tabbatar da cewa ana iya gadon ciwon daga wurin mahaifa(iyaye)

2. Type 2 Diabetes

Wannan nau’in yana farawa ne idan sinadain insulin ya daina aiki, ko kuma aikinsa ya ragu. Idan sugan mai wannan nau’in ya ƙara, ba zai sauka ba, har sai an sha maganin da zai dawo da aikin insulin.

Wannan nau’in ya fi kama manya.

Abubawan da suke janyo haɗarin kamuwa da wannan nau’in sun haɗa da:

Ƙiba: Ƙiba mara misali, musamman wadda ta haura ma’aunin Body Mass Index (BMI) 3okg/M2.

Rashin kazar-kazar: Waɗanda ko yaushe a zaune suke, ba sa kai-kawo, ba sa aiki kuma ba sa son aiki.

Cin abincin da ba shi da inganci a likitance: Yawan cin abinci, musamman wanda yake ɗauke da sinadaran cholesterol, suga, fat masu yawa a cikin su. Misali butter, chees, lemukan roba da na gwangwani, Askirin (lce cream) da sauransu.

Shan giya

Gado: Idan mahaifi ko mahaifiya suna da ciwon suga.

3. Gestational Diabetes

Wannan nau’in ciwon suga yana faruwa ne ga masu juna biyu (ciki).

Yanayin su ɗaya da Type 2 Dm. Sai dai ana warkewa daga wannan nau’in bayan an haihu. Ana iya ba su magani su sha, ko kuma a yi musu allurar insulin idan ana so suga ya daidaita.

Alamomin ciwon suga

i. Yawan fitsari  fiye da misali.

ii. Yawan shan ruwa fiye da misali.

iii. Yawan cin abinci fiye da misali.

Illolin ciwon suga

Masu gajeren zango: Su ne waɗanda suke faruwa a ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma suna iya sanadiyyar mutuwar mutum nan take. Sun haɗa da:

a. Suga ya yi yawa sosai a jinin mutum, yawan da ya wuce hankali; irin wannan matsalar tana janyo mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma mutum ya rasa ransa a nan take.

b. Suga ya yi ƙasa; wannan idan mutum yana shan maganin suga ko allurar cutar suga (insulin) fiye da yadda jikinsa yake buƙata; yana iya janyowa mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma ya fita daga hayyacinsa.

Masu dogon zango: Su ne waɗanda suke faruwa bayan mutum ya daɗe da ciwon suga a jikinsa.

Misali:

Ciwon ƙoda.

Ciwo ko kuma gyambon ƙafa, wanda zai iya janyowa a yankewa mutum ƙafa.

Ciwon ido wanda zai iya janyowa mutum ya makance.

Ciwon zuciya.

Cutar shanyewa ɓarin jiki

Da sauransa.

Magani/Shawarwari

Magungunan ciwon suga, kala biyu ne. Akwai na ƙwaya da kuma allura.

Idan mutum yana da ciwon suga, yana da matuƙar muhimmanci ya dinga yin waɗannan ababuwan:

Shan magani ko yin allura a kan ƙa’ida.

Yawan duba sinadarin suga akai-akai.

Yawan motsa jiki a ƙalla san huɗu a sati kamar tafiyar ƙasa ta tsawon minti talatin.

Daina shan giya

Rage shan kayan zaƙi masamman lemukan gwangwani ko na roba.

Rage cika ciki da abinci mai sinadain sikar (carbohydrate) a ciki kamar shinkafa, tuwo, masara, doya da sauransu.

Yawaita cin ganyayyaki kamar su alayyahu, zogale, rama, ganyan salak da sauransu.

Kammalawa

Ciwon suga ciwon ne mai haɗarin gaske. Har yanza babu maganin da yake warkar da ciwon gaba ɗaya.

Amma ana iya shan magani ko ayi allura domin a zauna lafiya. Don haka shan magani da zuwa asibiti ya zama wajibi ga duk mai cutar.

Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE) danna nan.

labarin da ya wuceMafifitan Ayyukan Mai Azumi
Labarin na GabaAlamomin Tashin Ƙiyama
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa