Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)

0
4046

Akwai wani ma’auni da ake amfani da shi wajen kula da ƙarfin gudanar jini a cikin jijiyoyin jini. Wannan ma’auni ana kiransa da ‘Blood Pressure (BP)’.

Yadda ake so BP ɗin babban mutum ya kasance shi ne:

90 – 139/60 – 89 MMHg. ma’ana dai:

(1) Ma’aunin sama ya kasance daga 90 zuwa 139. Kar ya yi ƙasa da 90, kuma ka da ya yi sama da 139.

(2) Ma’aunin ƙasa ya kasance daga 60 zuwa 89. Kar  ya yi ƙasa da 60, kuma kada ya yi sama da 89.

Ma’anar Hawan jini

Hawan jini shi ne, BP ɗin mutum ya fi 139 (ma’aunin sama) ko kuma ya fi 89 (ma’aunin ƙasa)

Abubuwan da suke janyo hawan jini.

Hawan jini kala biyu ne:

(1) Primary hypertension.

(2) Secondary hypertension.

Abin da yake janyo primary hypertension.

Babu abu guda ɗaya, wanda bincike ya nuna cewa yana janyo irin wannan hawan jini. Amma dai akwai wasu abubuwan da suke da alaƙa mai ƙarfi da irin wannan hawan jinin. Waɗannan abubuwan sun haɗa da:

  • Gado: idan ɗaya daga cikin mahaifinka, ko mahaifiyarka ko kuma ɗan uwanka shaƙiƙi yana da hawan jini, to kai ma za ka iya kamuwa da hawan jini.
  • Shan giya: Idan mutum yana shan giya, to zai iya kamuwa
  • Shan taba sigari.
  • Jinsin baƙar fata: idan mutum shi baƙi ne (ɗan Afrika), to zai iya kamuwa da hawan jini.
  • Ciwon suga (diabetes)
  • Ƙiba.
  • Shekaru sama da 40.
Abin da yake janyo secondary hypertension.
  • Ciwon ƙoda
  • Juna biyu (pregnancy)
  • Ciwon zuciya
  • Shan giya
  • Shan wasu ƙwayoyi kamar ‘Steroids’ da sauransu
Alamomin hawan jini

A mafi yawanci lokaci, hawan jini ba ya nuna wasu alamomi sai dai idan ya haifar, ko kuma ya fara haifar da matsala. Wannan dalilin ne ya sa ake kiran hawan jini da ‘Silent Killer’

Matsaloli ko kuma illoli da hawan jini yake haifarwa
  • Cutar shanyewar ɓarin jiki (stroke)
  • Ciwon zuciya
  • Ciwon ƙoda
  • Matsalolin ido
  • Mutuwar farar ɗaya da sauransu
 Abubuwan Masu Muhimmanci

A sani cewa, lokacin da jinin mutum ya hau ko kuma yake hawa, ba lallai ne mutum ya ji wata alama ta rashin lafiya ba. Shi yasa ake cewa hawan jini ‘Silent Killer’ ma’ana ‘mai kisa ba tare da an sani ba‛

Don haka yana da kyau mutum ya dinga zuwa ana duba masa BP ɗinsa lokaci zuwa lokaci

Maganin hawan jini

A likitance, babu wani magani guda ɗaya wanda idan mutum ya yi amfani da shi zai warke daga hawan jini, musamman ‘primary hypertension‛.

Amma idan mutum yana da ‘secondary hypertension‛ to zai iya samun waraka idan aka yi maganin abin da ya janyo masa hawan jinin.

Magungunan hawan jini, suna daidaita ‘BP‛ ne amma ba sa warkar da hawan jinin. Shi yasa ake shan maganin a kowace rana muddun mutum yana da rai.

Idan mutum ya daina shan maganin ba tare da shawarar likita ba, to jinin nasa zai iya ci gaba da hawa kuma ya haddasa masa matsalolin da aka lissafa a baya.

Shawarwari
  • A rage gishiri a abinci: gishiri ya kasance ɗan kaɗan, sannan kuma a daina barbaɗa gishiri a abinci
  • A daina shan taba sigari
  • A daina shan giya
  • A rage amfani da kayan da suke ƙarawa miya zaƙi, sai wanda likita ya bada shawara. A daina shan magunguna barkatai ba tare da shawarar likita ba
  • A yawaita motsa jiki
  • A rage ƙiba ta hanyar motsa jiki da kula da abinci
  • A rika zuwa wurin likita lokaci zuwa lokaci domin duba BP
Kammalawa

Mutane masu hawan jini suna da yawa a cikin al’ummarmu, kuma yana janyo illoli da suke da wahalar magani. Idan mutum yana shan magani, kuma yana bin dokokin likita, to zai iya samun sauƙi ko kuma kariya daga Waɗannan matsaloli.

labarin da ya wuceMene Ne Taifud (TYPHOID)
Labarin na GabaYadda Ake Chips Da Sauce Na Ƙundun kaza
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa