Mene Ne Taifud (TYPHOID)

0
3661

Cutar Typhoid na ɗaya daga cikin cututtukan da suke haddasa zazzaɓi mai tsanani. A sani cewa, kamuwa da cutar Typhoid ya yi ƙaranci sosai a yanzu, musamman idan aka kwatanta da cutar malaria. Kuma ana warkewa daga cutar gaba ɗaya.

  • Typhoid ba cuta ce da take tashi daga lokaci zuwa lolaci ba
  • Typhoid daban, sannan Malaria ma daban.
  • Ma’ana dai, idan kana da cutar typhoid ba shi yake nufin kana da malaria ba.

Yadda ake kamuwa da Typhoid

Ana kamuwa da cutar typhoid ta hanyar ƙwayar cuta (bacteria) wadda ake kiranta da suna Salmonella typhi da kuma Salmonella paratyphi.

Ita wannan ƙwayar cutar, tana yaɗuwa ne tsakanin mutane (daga mutum zuwa wani mutum) ta hanyar kashi (bayan gida).

Idan mai cutar Typhoid ya je yin kashi (bayan gida), ƙwayar cutar typhoid ɗin tana iya fita daga kashin nasa. Idan wannan kashin (wanda yake ɗauke da kwayar cutar) ya taɓa abinci ko abin sha, sannan kuma aka ci ko aka sha wannan abincin ko abin shan, to za a iya ɗaukar cutar typhoid.

Amma dai yanzu mutane suna ɗan yi ƙoƙari wajen yin tsafta, shi ya sa kamuwa da cutar typhoid ya yi ƙaranci.

A taƙaice, duk wanda ya kamu da cutar typhoid, to ya ci, ko kuma ya sha kashi.

Alamomin cutar Typhoid
  • Zazzaɓi mai tsananin gaske. Zazzaɓin ba ya raguwa sai dai ƙaruwa, musamman idan ba a sha magani ba.
  • Ciwon ciki
  • Gudawa, wani zubin ma har da jini
  • Kasala
  • Ciwon kai
Idan typhoid ya yi tsanani, zai iya janyo:
  • Tsinkewar hanji da ciwon ciki mai tsanani
  • Suma
Hanyoyi kariya daga cutar.

Kamar yadda aka faɗa a baya, duk wanda ya kamu da cutar typhoid, to ya ci kashi, ko ya sani, ko bai sani ba.

Idan mutum yana son kariya, to dole ne ya yi iya ƙoƙarinsa domin kada ya ci kashi ta hanyoyi kamar haka:

  • A wanke kayan abinci sosai kafin a yi amfani da su, musamman ‘ya’yan itaciya da kuma kayan lambu.
  • A wanke hannu da sabulu sosai, bayan an fito daga banɗaki (kashi).
  •  Mutane su daina yin kashi a buɗaɗɗen waje, musamman gonaki.

Wasu abubuwa masu mahimmanci
  • Akwai wani gwajin jini (test) da ake ce masa ‘WIDAL TEST’. Ya kamata a sani cewa, shi wannan gwajin an daina yin amfani da shi wajen gano cutar typhoid. Saboda ba ya bayar da sakamako ingantacce.
  • Allurar jijiya da ake yi a matsayin maganin typhoid, a shagunan da ake sayar da magani, kuskure ne, kuma idan da tsautsayi, mutum zai iya cutuwa. A kiyayi allurar jijiya saboda tana da haɗari ƙwarai da gaske.
  • Typhoid da malaria ba abu ɗaya ba ne. Don kana da typhoid, ba shi yake nufin kana da malaria ba. Kowanne matsayinsa daban, kuma maganinsa daban.
  • Cutar typhoid ta yi ƙaranci a cikin al’umarmu kwarai da gaske, saboda mutane suna ƙara wayewa musamman wajen tsafta.
Kammalawa

Cutar typhoid, akwai ta a cikin al’ummarmu, amma fa ta yi ƙaranci sosai da sosai musamman idan aka kwatanta ta da malaria. Kuma ana warkewa. Idan aka sha magani.

A kiyayi yin allurar jijiya da zarar ana zazzaɓi.

Danna koren rubutun domin karanta mene ne zazzaɓin ciwon sauro ko yadda ake kare kai daga ciwon sanyi (Toilet Infection)

 

labarin da ya wuceMene Ne Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
Labarin na GabaMene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa