Medical Check-Up

0
14

Matasa a duƙufa medical check up, duk mutuwa tana da sababi, inkaji ance wane ya yanke jiki ya faɗi ya dace ka fara tunanin meke haddasa irin haka? Mutuwar fuju’a ba’a bar so bace,

Saidai sau tari rashin sani kesa ai mata kallon fuju’a amma a zahiri jiki ya jima cikin jinya ƙin basa hakkinsa ake. Ina ƙara jan hankali don fa kana jinka lafiya hakan bai nuna lafiya kake har sai likita ya tabbatar ma.

Domin karanta yadda ake Tsayar Da Zubar Jini (Agajin Gaggawa) Danna nan 

Wanda ko yasan yana da wata larura da yake sake da sha mata magani,ya daure ya daina, ya rungumi magani tamkar abinci, sakaci da karamar cuta kesa ta girma tafi ƙarfin jiki tare da tattalin arziki…har sai an kai ga neman taimako.

Har ga Allah mu bakaken fata bama baiwa kula da lafiya wani muhimmanci, ina amfanin ka ƙare kuruciya neman kudi karshe ka karar da kudin wajen neman lafiya kuma bata samu ba antafi lahira a wahalce. Check up dinnan sau daya a shekara inkayi ya wadatar, inkana da wadata kuma kai sau biyu a shekara wato duk bayan wata shida.

Domin karanta bayani akan Nausea (Tashin Zuciya) Danna nan 

labarin da ya wuceNausea (Tashin Zuciya)
Labarin na GabaBayani Akan Tsarin Abinci Ga Masu Ciwon Suga (Diabetes Mellitus)