Rafkanuwa A Sallar Nafila

0
35

Ana yin ‘sujudus sahwi’ a sallar nafila, kamar yadda ake yin ta a farilla, sai dai a rafkanuwa cikin karatun Fatiha, karatun surah, asirtawa, bayyanawa, ƙarin raka’a ko manta rukuni cikin rukunan sallah (sujjada ko ruku’u). 

  1. Wanda ya manta karatun Fatiha (a sallar nafilah) bayan ya yi ruku’u, zai wuce, sai ya yi ƙabli. 
  2. Wanda kuma ya manta karatun surah a sallar nafila, ko asirtawa, ko bayyanawa, to ya wuce, babu sujjada a kansa (a sallar nafilah). 
  3. Wanda ya miƙe domin raka’a ta uku (3) a cikin sallar nafila, to, ya dawo ya zauna, sai ya yi sujjada ba’adi. Idan kuma har ya ƙulla raka’a ta ukun (ma’ana har ya yi ruku’u), sai ya cika ta, ya ƙara wata ɗaya (ta zama huɗu (4) kenan), sai ya yi ƙabli. 
  4. Wanda kuma ya manta rukuni kamar ‘ruku’u’ ko ‘sujjada’ har ya yi sallama (a sallar nafila), babu sujjada a kansa. 
  5. Wanda yake kokwanto a cikin sallar ‘Shafa’i da Wuturi’, ma’ana, yana tunanin Shafa’i yake, ko Wuturi, ko ya bar raka’ar a matsayin raka’a ta biyu ta Shafa’i, idan ya sallame (Shafa’in), sai ya yi wuturi. Wanda ya samu sallar tare da liman, amma zai yi ciko.
  6. Wanda ya katsar da sallar nafila da gangan, ko ya bar wani rukuninta da gangan, zai ya maimaita wannan sallar baki ɗaya. 

Domin Karanta  Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceShakku A Cikin Sallah
Labarin na GabaCizo Nawa Sauro Take A Kamu Da Malaria?