Shakku A Cikin Sallah

0
31
  1. Wanda ya yi shakka a cikar sallarsa, a kan ya yi ko bai yi wani aiki ba, zai yi gini a kan bin da yake da yaƙini a kai. 

Misali, wanda yake kokwanton ya yi raka’a biyu (2) ne, ko ɗaya (1), to zai yi gini bisa mafi ƙaranci (wato a kan raka’a 1), sai ya cika 1, sai ya yi sujjadar ba’adi. 

  1. Duk wanda ya yi sallama, alhalin yana shakkar a kan cikar sallarsa, to sallarsa ta ɓaci, sai ya sake ta. 
  2. Wanda ya yi shakka yin sallama a sallah, idan yana kusa (lokacin bai yi tsawo ba), kuma yana da alwala, sai ya yi sallamar. Idan kuma ya yi nisa, sallarsa ta ɓaci, sai ya sake sallah. Abin nufi, wanda bai riski ruku’u ba, a raka’ar qarshe a sallar jam’i.
  1. Wanda yake yawan wasi-wasi, zai zo da abin da yake shakka, sai ya yi sujjada ba’adi. 
  2. Wanda ya yi kokwanto a kan ba shi da tsarki ko samuwar najasa (misali, fitar tusa, fitsari, maziyyi, maniyyi ko wadiyyi), kuma ya samu tabbacin babu rashin tsarki ko samuwar najasar, babu komai a kansa. 

Amma idan tunaninsa kan shakkar tsarki ta yi tsayi, to sallarsa ta ɓaci. Idan ya samu tabbacin ba shi da tsarki, zai yanke sallah, ya yi tsarki, ya sake sallah. 

Domin Karanta  Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceNau’o’in Sujjadar Rafkanuwa
Labarin na GabaRafkanuwa A Sallar Nafila