Shin mace mai cutar HIV, zata iya haihuwa ba tare da jaririn ya kamu da cutar ba?
AMSA
Cutar HIV na daga cikin cututtukan da jariri zai iya kamawa daga uwansa a lokacin haihuwa ko lokcin shayarwa amma idan aka bi dokikin likitoci,za a iya ƙare jaririn daga kamuwa da cutar.
Karanta cikekken Mataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda Danna nan
Ga Ƙa’idodin:
- Mace ta kasance tana shan magungunan ta na HIV (antiretroviral drugs) musamman a lokacin da take ɗauke da juna biyu,da kuma bayan haihuwa har zuwa lokacin da zata yaye yaro
- Akwai gwaje-gwaje da ake yi wa jaririn daga lokaci zuwa lokaci domin a sanin ko yana ɗauke da cutar
- Akwai magunguna da ake bawa jaririn na prophylaxis (wato zai taimaka mashi ko da idan ya kamu da ciwon amma tests bai nuna ba tukunna)
- Mace tana da damar ta shayar da jaririn,idan har zata cigaba da shan magungunan ta. Amma idan zata iya shayar da shi da madaran jarirai na gwangwani toh babu matsala. Amma kada a haɗa biyun a lokaci ɗaya. Ko ruwan nono zalla ko madara zalla.
Domin karanta bayani akan yadda zaku magancewa marasa lafiyarku masu cutar malaria ko hyperstimulated nervous system (wato yanayi ne da sashin dake sarrafa ƙwaƙwalwa da laka kanyi aiki ba bisa ƙa’ida ba) danna wannan koren rubutun
Domin karanta Abubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan
[…] Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS […]
[…] Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS […]
[…] Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS […]