Tag: HIV/AIDS

  • Shin Sauro Yana Yaɗa Cutar HIV/AIDS?

    Shin Sauro Yana Yaɗa Cutar HIV/AIDS?

    Mun san da cewar macen sauro tana da saliva wato miyau, sannan tana da allurai har guda 6 waɗanda da su take aikin zuƙar jinin mutum, guda 4 tana amfani da su ne wajen huda fatar mutum yayin da guda 2 ɗin kuma suke ɗauke da wani “pipe” da ake kira da “tube” wanda 1 magudanar miyau ne 1 kuma magudanar da jinin mutum yake bi ne yana komawa jikin sauron wannan ɗaya daga cikin dalilai ne da yasa ba sa iya yaɗa cutar HIV ko da sun ɗauko ta daga mai ƙanjamau ɗin, kamar yanda Professor Wayne Crans da ke jami’ar Rutgers ya sanar da manema labarai

    Dalili na 2 kuma shi ne: ƙwayar cutar HIV ba ta replicating ma’ana yaɗuwa a cikin hanjin sauro ko da ya yi ƙoƙarin yaɗa ta ga wanda ba shi da cutar, nan da nan Allah yake kiyaye bayinSa cutar take breaking down wato nan take take mutuwa. Ga mutane, cutar HIV tana nannaɗewa ne ga T-cells hakan yakan saka ta yaɗuwa amma a cikin sauro kuwa babu T-cells don haka cutar ba za ta iya tsallakawa zuwa miyau ɗin sauro ba.

    Wannan ikon Allah ne kam, domin kuwa ban manta da hadisin nan da ke cikin Sahihul Bukhari ba wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace “Idan alfasha ta yi yawa a ban ƙasa to sababbin cututtuka da ba ku san su ba za su yawaita”, a nan Allah cikin ikonSa ya kiyaye wasu mutanen daga kamuwa da cutar ƙanjamau ta hanyar cizon sauro wanda suke zuƙowa daga masu ƙanjamau cutar da aka fi samu silar alfasha duk da dai ana samu ta ɓangaren amfani  da reza ko kuma allurar da take ɗauke da jinin mai cutar, wannan duk tsantsar lissafi ne na Allah Azza wajallah wanda dama shi ne “AL-HASIBU” mai lissafa kuma Mai ƙididdige abu. Allahu Akbar !

    A likitance ma ko da a ce sauro zai yaɗa cutar HIV to sai an samu cizon sauraye sama da miliyan 10 kafin a samu guda 1 da zai iya saka cutar, a kintace, masu cutar HIV ba sa ɗauke da unit 10 na cutar. A haɗarance kuma, ko da zaka hadiye sauro ko kuma make shi da hannu hakan ba zai sa ka kamu da cutar HIV ɗin a jikin sauron ba, hakan na nufin sauro ba shi da isasshen jinin mai ƙanjamau da har mutane suke tunanin zai iya yaɗa shi ga mara ƙanjamau ba.

    Suna ƙyanƙyashi ‘ya’yansu ne ta hanyoyi 4

    Na farko haihuwar ƙwayayen (eggs) daga nan kuma cikin ikon Allah da hikimarSa sai ƙwan ya koma abinda ake kira da larva (za su yi kama da caterpillar ko kuma ɗan mitsisin kifi) daga nan kuma sai pupa (kamar tsutsa) sai kuma su zama adult, sai Allah Azza wajallah ya ba su ikon buɗe fika-fikansu sai su fara tashi su zama sauro.

    Namijin sauro yana kai kwanaki 10 kafin ya mutu amma macen takan share kwanaki 42 zuwa 56 kafin mutuwarta. Bambancin adadin kwanakinsu kuwa yana da alaƙa da ɗawainiyar da macen take na ɗaukar nauyin ƙyanƙyashe ƙwayayenta.

    Ko da jininka ko babu Allah Azza wajallah yana ba wa sauro tsawon a ƙalla rayuwar sati 2 zuwa 3, ba wai dole sai da jini suka ta’allaƙa su rayu ba kamar yanda wasu suke tunani ba.

    A kowanne kwana 3 macen sauro take zuba ƙwayayenta akan ruwa, musamman ma ruwan kwata, ba abin mamaki ba ne kenan idan ya zamana sauro ya yawaita a kwatocin unguwanni da mutane marasa tsafta.

    Don karanta littafin sauro halittar Allah mai ban al’ajabi danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Hiv/Aids Cutar Kanjamau (Sida)

    Hiv/Aids Cutar Kanjamau (Sida)

    MA’ANAR CIWON SIDA: Cutar Kanjamau wanda a turance ake kira da Acquired Immunodeficiency syndrome (AIDS) cuta ce me hadari ga rayuwar dan adam wacce kwayar cuta me karya garkuwar jiki da ake kira a turance  da Human Immunodeficiency Virus(HIV) ke kawo ta.

    Ita wannan kwayar cuta ta (HIV) na ruguza kariya da jiki ke samarwa daga cututtuka wanda hakan ke ba wa wasu cututtukan daman yi wa jiki illa da wuri.

    HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR KANJAMAU

    1. Ana iya kamuwa ta hanyar saduwar da ba’a yi amfani da kwarkwaron roba ba ga Wanda yake dauke da wannan ciwo.
    2. Amfani da abubuwan masu kaifi kamar reza da wuka, kibiya, allura da mai cutar ke amfani dasu.
    3. Bayar da jini mai dauke da cutar sida ga mai buqata.
    4. Ta nonon uwa ga ya/yaro wajen shayarwa.
    5. Haduwar jinin uwa  mai dauke da cutar, dana jariri ko jaririya lokacin haihuwa (transplacental).

    Domin karanta Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa) Danna nan

    ALAMOMIN TA:

    Daga alamomin ta akwai

    1. Zazzabi Mara yankewa.
    2. Ciwon kai Mara yankewa.
    3. Ciwon jiki akai-akai.
    4. Kuraje.
    5. Ciwon gabobi.
    6. Zawo.
    7. Gyanbon baki ko na al’aura.
    8. Zufa da daddare.
    9. Ciwon makogwaro.
    10. Kaluluwa mafi akasari a wuya.
    11. Tari Mara yankewa.
    12. Ramewa akai-akai.
    13. Rawar dari Mara yankewa.

    Ganin alamomin ta ba ya tabbatar da samuwar ta har sai an tabbatar da hakan ta hanyar gwajin jini.

    Yana dakyau ku karanta Physiology da Hausa Kashi na Takwas: Gastrointestinal System(Sashin Sarrafa Abinci)

    HANYOYIN KARE KAI
    1. Amfanin da kwarkwaron roba lokacin saduwa.
    2. Kin yin amfani da abubuwa masu kaifi kamar reza ko allura ko jinin da wanda ke dauke da cutar yayi amfani da su.
    3. Kara karfin garkuwar jiki.
    4. Yin gwajin cutar lokaci bayan lokaci.
    5. Takaita abokan saduwa.
    6. Shan magani ga wanda ke dauke da cuta.
    7. Gwajin jini kafin sanyawa mai bukata.
    MAGANIN TA

    Har yanzu babu wani magani da bincike ya tabbatar da warkewa daga cutar, amma akwai magunna da dama da ke dakusar da haihuwar kwayar cutar.

    Hadi da shan magani, cin abinci mai kara karfin garkuwar jiki na da amfani matuka.

    Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

    Sannan matuqar zaku Sha magani tareda da kiyaye dokoki to tabbas zakuyi rayuwa tamkar kowa.

    WASU ABUBUWA NE ZAKA IYAYI TAREDA MAI CUTAR:

    Zaku iyayin abubuwa Kar harka ba tareda kasamu wanna cuta ba:-

    – Cin abin tare a kwano daya.

    – wanka tare

    – Wasa tare

    – Kwanciya tare da Mai cutar

    – Gaisuwa tareda Mai cutar

    – Zama guri daya da Mai cutar

    – Amfani da cokali daya da Mai. Cutar.

    – Amfani da Kofi daya da Mai cutar

    TUNATARWA:

    Kira ga al’umma duk Wanda/Wadda akasamu da wannan cuta to kar a kyamaceshi, ajashi ajiki, abashi kariya da kulawa sannan kuma da Shawarwari, tareda da kiyaye yaduwar cutar ga al’umma.

    SHAWARA:

    Aduk lokachi da bawa ya tsinci Kansa da irin wadannan alamomi to Kar yai qasa agwiwa ya ziyarchi asibiti mafi kusa Don yin gwaje-gwaje da Kuma samun gamsasshen bayani dangane da cutar.

    Domin karanta bayani akan Matsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya Danna nan

  • HIV/AIDS 

    HIV/AIDS 

    Shin mace mai cutar HIV, zata iya haihuwa ba tare da jaririn ya kamu da cutar ba?

    AMSA

    Cutar HIV na daga cikin cututtukan da jariri zai iya kamawa daga uwansa a lokacin haihuwa ko lokcin shayarwa amma idan aka bi dokikin likitoci,za a iya ƙare jaririn daga kamuwa da cutar.

    Karanta cikekken Mataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda Danna nan

    Ga Ƙa’idodin:
    • Mace ta kasance tana shan magungunan ta na HIV (antiretroviral drugs) musamman a lokacin da take ɗauke da juna biyu,da kuma bayan haihuwa har zuwa lokacin da zata yaye yaro
    • Akwai gwaje-gwaje da ake yi wa jaririn daga lokaci zuwa lokaci domin a sanin ko yana ɗauke da cutar
    • Akwai magunguna da ake bawa jaririn na prophylaxis (wato zai taimaka mashi ko da idan ya kamu da ciwon amma tests bai nuna ba tukunna)
    • Mace tana da damar ta shayar da jaririn,idan har zata cigaba da shan magungunan ta. Amma idan zata iya shayar da shi da madaran jarirai na gwangwani toh babu matsala. Amma kada a haɗa biyun a lokaci ɗaya. Ko ruwan nono zalla ko madara zalla.

    Domin karanta bayani akan yadda zaku magancewa marasa lafiyarku masu cutar malaria ko hyperstimulated nervous system (wato yanayi ne  da sashin dake sarrafa ƙwaƙwalwa da laka kanyi aiki ba bisa ƙa’ida ba) danna wannan koren rubutun 

    Domin karanta Abubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan