Tag: ciwon suga

  • Shawara Ga Masu Ciwon Suga

    Shawara Ga Masu Ciwon Suga

    Mutane masu larurar ciwon siga ku daure kullum musamman wajen alwalar safe ko la’asar kuke tsayawa ku lura da tafukan ƙafarku da tsakanin yatsu da kyau, saboda 60% kukan iya yin rauni ba tare da kun ji zafi ba ballantana ku sani, wanda a ƙarshe in aka yi rashin sa’a ƙwayoyin cutar da ke kan fata ko sarari, tsakar gida ko kan titi inda muke takawa suka sami damar hawa kan ciwom sai abu ƙarami ya zamto babba har ya yi muni.

    Da yawa ta inda matsalar gyambon ƙafa ke somuwa kenan a gareku, wanda ƙarshe sai an kai ga yanke kafa, A ƙalla duk awa 1 sai an yanke ƙafa dalilin ciwon suga, kimanin ƙafafu 24 ake cire wa a kullum cikin faɗin duniya.

    Don haka, muddin ka ga rauni a ƙafarka matsayinka na mai ciwon sugar, to ka hanzarta zuwa a duba a wanke a baka magani, kar ka kuskura ka ce ai zai warke da kansa tunda ba shi da girma.

    Haka nan wasu kan yi kuskuren cewa ai cin ruwa ne alhalin diabetic neuropathy ne don haka a lura da ƙafa, a lura da glucose control, Diabetes is not a joke. Banda yawo ba takalmi ko safa koda kuwa a tsakar gida ne, ake shafawa kafa mai sosai take santsi. Da an ji alamun ta fara yin dundurus, ko ba ta bari a iya bacci in dare ya yi to a nemi ɗaukin likita. A kuma dinga yanke farce koyaushe.

    Sannan a dinga rufe ido ana sa tsinken tsintsiya lokaci lokaci ana duddungurar tafin kafar musamman pressure points. ko kuma mutum ya rufe ido ya sa wani ya yi masa, ana jin cewa ba a jin sensation na taɓin ko kuwa in a taɓa mutum ba ya iya guessing yace guri kaza ne tunda idonsa rufe yake, to akwai buƙatar a je ga likita lallai kar a yi wasa, ba sai an jira an ga rauni ba.

    Allah shi taƙaitamana wahala, ya bai wa kowa lafiya.

    Domin karanta Ciwon Suga danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Ciwon Suga.(Diabetes)

    Ciwon Suga.(Diabetes)

    Menene Ciwon Suga?: Cuta ce da ba abu daya ne ke haddasa ta ba, ida ake samun sugar fiye da kima yana zagayawa a cikin jini saboda rashin sinadarin insulin ko kasa amfani da shi.

    Nau’ikan Ciwon Suga.

    Nau’i Na Farko

    Shine ciwon suga din da yake dalilin karancin samar  da insulin. Anfi samu a yara da matasa kasa da shekara 30.

    Nau’i Na Biyu

    Wannan kuma akwai insulin din amma jiki baya iya amfani da shi. Anfi samu a manya masu shekaru sama da 40.

    Menene Insulin?

    Wani sinadari ne da jiki kan samar da shi, yana taimakawa wajen shigar da suga cikin ƙwayoyin halittar jiki domin samar da kuzari (Energy) a jikin mutum. Shi yasa rashin sa ko idan jiki ya kasa amfani da shi yake kawo dagawar sugar a cikin jini.

    Alamomin Wannan Cuta
    •  Yawan fitsari
    •  Yawan jin kishirwa
    •  Yawan jin yunwa
    •  Takan iya zuwa babu alamun(Asymptomatic)
    •  Takan iya zuwa da yanayin gaggawa da ka iya sandin ran mutum ( Diabetic Ketoacidosis)

    Akwai cutuka da yawa da kan iya zuwa da irin wannan yanayi, don haka gwaji ne ke iya tabbatar da ita.

    Menene Tasirin Wannan Cuta?

    Wannan cuta idan ta ta’azzara takan iya haifar da matsaloli da yawa a jikin mutum, musamman wanda basa kula da amfani da magungunan da likita ke basu ko idan basu samu inda ya dace a kula da su ba.

    Wannan Matsaloli Sun Hada Da:
    •  Shanyewar barin jiki (stroke)
    •  Matsalar idanu
    •  Ciwon zuciya
    •  Hawan jini
    •  Rashin wakewar ciwo da wuri
    •  Ciwon koda.
    •  Mutuwar kafa( diabetic foot)
    Shawara Ga Masu Cutar
    •  A kula da irin abincin da ake ci, abi shawarar likita.
    •  Motsa jiki yana taimakawa wajen shingar da suga cikin ƙwayoyin halittar jiki, ta haka yana rage suga ya kuma kara lafiya.
    •  A kula da amfani da  magunguna  ba bisa ka’idar da likita ya bayar.

    Idan mai wannan cuta ya kiyaye shawarwarin da masa akan harkar lafiya suka bayar, zai a samu saukin matsaloli da ingantacciyar rayuwa.

    Yana dakyau ku karanta wannan Yan Mata Masu Shirin Yin Aure Da Amare Da Kuma Masu Sabon Ciki Karkuga Kamar Na Takura Muku Da Maganar Folic Acid

  • Idan Mutum Yana Fama Da Ciwon Saukar Suga Ko Gyanbon Ciki Mai Zafi, Zai Iya Ɗaukar Azumi?

    Idan Mutum Yana Fama Da Ciwon Saukar Suga Ko Gyanbon Ciki Mai Zafi, Zai Iya Ɗaukar Azumi?

    Amsa: Likita ne kaɗai zai iya bashi amsar wannan tambayar, ta halaccin yin azumi ga wanda ke cikin irin wannan jinyar, ko haramcin hakan, kuma wajibi ne yabi umarnin likita.

    Hujja: “Ga waɗanda baza su iya azumi ba, sai su ciyar da miskinai”.

    Suratul Baqara aya 184.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Ya Hallata Mai Ciki Ta Ɗauki Azumi? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon suga sinadari ne mai matuƙar amfani a jikin mutum. Ana samun sa daga abincin da muke ci da kuma abubuwan da muke sha.

    Idan suga ya yi yawa, ko kuma ya yi kaɗan a jikin mutum, ana iya kamuwa da rashin lafiya wadda za ta iya sanadiyar mutuwar mutum idan ba a ɗau mataki ba.

    Akwai wani sinadari da ake kira insulin a jikin ɗan Adam. Sinadarin insulin shi ne yake kula da daidaituwar sinadarin suga a cikin jini. Idan mutum ya ci abinci mai dauke da sinadarin suga (carbohydrate), sai sugan ya koma cikin jini bayan ya narke. 

    Sai sinadarin insulin ya zo ya daidaita suga, domin kada sugan ya cutar da jiki. 

    Ma’anar ciwon suga, cuta ce wadda take faruwa sanadiyyar ƙaruwar yawan sinadarin sikari (suga) a cikin jini na tsawon lokaci. Cutar tana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin, ko kuma insuin ɗin ya daina aiki gaba ɗaya.

    Rabe-raben Ciwon Suga

    Rabe-raben ciwon suga suna da yawa, amma za mu yi magana a kan guda uka kawai:

    1. Type I Diabetes

    Wannan nau’in ciwon sugan, yana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin.

    Idan sugan  mai wannan nau’in ciwon sugan ya ƙaru, ba zai sauka ba, saboda babu insulin. Idan kuwa ana so ya sauka, to dole sai an yi allurar insulin.

    Wannan nau’in  ya fi kama yara. Haƙiƙanin abin da yake janyo wannin  nau’in ciwon ba a san shi ba, amma dai an tabbatar da cewa ana iya gadon ciwon daga wurin mahaifa(iyaye)

    2. Type 2 Diabetes

    Wannan nau’in yana farawa ne idan sinadain insulin ya daina aiki, ko kuma aikinsa ya ragu. Idan sugan mai wannan nau’in ya ƙara, ba zai sauka ba, har sai an sha maganin da zai dawo da aikin insulin.

    Wannan nau’in ya fi kama manya.

    Abubawan da suke janyo haɗarin kamuwa da wannan nau’in sun haɗa da:

    Ƙiba: Ƙiba mara misali, musamman wadda ta haura ma’aunin Body Mass Index (BMI) 3okg/M2.

    Rashin kazar-kazar: Waɗanda ko yaushe a zaune suke, ba sa kai-kawo, ba sa aiki kuma ba sa son aiki.

    Cin abincin da ba shi da inganci a likitance: Yawan cin abinci, musamman wanda yake ɗauke da sinadaran cholesterol, suga, fat masu yawa a cikin su. Misali butter, chees, lemukan roba da na gwangwani, Askirin (lce cream) da sauransu.

    Shan giya

    Gado: Idan mahaifi ko mahaifiya suna da ciwon suga.

    3. Gestational Diabetes

    Wannan nau’in ciwon suga yana faruwa ne ga masu juna biyu (ciki).

    Yanayin su ɗaya da Type 2 Dm. Sai dai ana warkewa daga wannan nau’in bayan an haihu. Ana iya ba su magani su sha, ko kuma a yi musu allurar insulin idan ana so suga ya daidaita.

    Alamomin ciwon suga

    i. Yawan fitsari  fiye da misali.

    ii. Yawan shan ruwa fiye da misali.

    iii. Yawan cin abinci fiye da misali.

    Illolin ciwon suga

    Masu gajeren zango: Su ne waɗanda suke faruwa a ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma suna iya sanadiyyar mutuwar mutum nan take. Sun haɗa da:

    a. Suga ya yi yawa sosai a jinin mutum, yawan da ya wuce hankali; irin wannan matsalar tana janyo mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma mutum ya rasa ransa a nan take.

    b. Suga ya yi ƙasa; wannan idan mutum yana shan maganin suga ko allurar cutar suga (insulin) fiye da yadda jikinsa yake buƙata; yana iya janyowa mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma ya fita daga hayyacinsa.

    Masu dogon zango: Su ne waɗanda suke faruwa bayan mutum ya daɗe da ciwon suga a jikinsa.

    Misali:

    Ciwon ƙoda.

    Ciwo ko kuma gyambon ƙafa, wanda zai iya janyowa a yankewa mutum ƙafa.

    Ciwon ido wanda zai iya janyowa mutum ya makance.

    Ciwon zuciya.

    Cutar shanyewa ɓarin jiki

    Da sauransa.

    Magani/Shawarwari

    Magungunan ciwon suga, kala biyu ne. Akwai na ƙwaya da kuma allura.

    Idan mutum yana da ciwon suga, yana da matuƙar muhimmanci ya dinga yin waɗannan ababuwan:

    Shan magani ko yin allura a kan ƙa’ida.

    Yawan duba sinadarin suga akai-akai.

    Yawan motsa jiki a ƙalla san huɗu a sati kamar tafiyar ƙasa ta tsawon minti talatin.

    Daina shan giya

    Rage shan kayan zaƙi masamman lemukan gwangwani ko na roba.

    Rage cika ciki da abinci mai sinadain sikar (carbohydrate) a ciki kamar shinkafa, tuwo, masara, doya da sauransu.

    Yawaita cin ganyayyaki kamar su alayyahu, zogale, rama, ganyan salak da sauransu.

    Kammalawa

    Ciwon suga ciwon ne mai haɗarin gaske. Har yanza babu maganin da yake warkar da ciwon gaba ɗaya.

    Amma ana iya shan magani ko ayi allura domin a zauna lafiya. Don haka shan magani da zuwa asibiti ya zama wajibi ga duk mai cutar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE) danna nan.

  • Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Kunun kwakwa yana ɗaya daga cikin abin sha mai riƙe ciki, sannan ba shi da wahalar narkewa a ciki.

    Yana rage hawan suga ga masu ciwon suga, ruwan kwakwa yana wanke koda da samun fitar fitsari cikin sauri da inganta aikinta wajan tace abubuwa da sauransu.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Kofi ɗaya na Farar shinkafa
    Kofi ɗaya na Kwakwa
    Kofi ɗaya na Gyada
    Kofi ɗaya na Madara
    Sai a zuba ruwan zuma gwargwadon yadda ake buƙata ko sikarin da suke amfani da shi na masu ciwon siga.

    Yadda ake haɗa kunun kwakwa

    1. Da farko za a wanke shinka fara, sai a jiƙa ta da ruwan zafi tsawon minti talatin (30)

    2. Sai a jiƙa gyadar, a surfa ta, a wanke ta (kamar yadda ake wanke wake).

    3. Sai a juye su (Shinkafa, gyaɗa, kwakwa) a abin da za a markaɗa (blender). A zuba ruwan kwakwar a yi blending sosai; (Za a iya ƙara ruwa idan ruwan kwakwar bai isa ba)

    4. Sai a tace a ɗaura a tukunya a yi ta juyawa har sai an ga ya yi kauri.

    5. Sai a zuba zuma ko sikarin masu ciwon siga (gwargwadon yadda ake buƙata) da madara kofi ɗayan nan a motsa. Sai a kashe wutar, a bar shi ya kama jikinsa kamar na minti biyar

    Wannan abin shan, yana da kyau ga masu ciwon siga da ‘yan sama da shekara arba’in (40). Su mayar da shi abincin darensu, domin ƙarin lafiyarsu.

    Domin sanin yadda ake Buredin Kwakwa danna koren rubutun nan.

    Domin sanin yadda ake Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread) danna koren rubutun nan.