Mutum A Gidan Gwaji (DUNIYA)

0
17

Allah Maigirma da Ɗaukaka ya bayyana cewa: “Shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya gwada ku. Wane ne mafi kyawun aiki a cikin ku”(Suratul Mulk: 2).

Kuma manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya siffanta Aljanna da haja. (Kayan sayarwa) mai tsada, ba a samunta a ɓagas sai an yi aiki mai kyau, aiki na gari, sannan za a iya mallakarta.

Don haka ne Allah Ya sauko da mutum a gidan duniya, sai Ya jarraba shi da shaiɗan wanda kullum aikinsa shine;ya ɓatar da mutum, ya afka shi cikin saɓo. Wato ya sa shi ya faɗi a jarrabawa!
Bugu da ƙari, shi shaiɗan yana da mataimaka masu taya shi aikin ɓatar da mutum, waɗannan mataimaka suna da yawa, amma mafi hatsari a cikinsu suna:Son zuciya da ruɗin duniya. Saboda haka, idan mutum yana son ya ci jarrabawar Allah ba shi da hanyar da ta wuce saɓawa waɗancan magauta guda uku.
• Shaiɗan;
• Son zuciya;
• Ruɗin zuciya

• Saɓawa Shaiɗan: Ka da mutum ya manta da ƙiyyayyar da shaiɗan ya ke yi masa, don haka ya kamata ya dauwama akan nema tsarin da shi, sannan ya riƙe koyarwar Musulunci sosai.
• Saɓawa Son Zuciya: Ta hanyar bin ƙa’ida, da riƙe gaskiya da tsarin amana, ko da ransa ba ya so.
• Saɓawa Ruɗin Duniya: Ta hanyar neman halal, da haƙuri da abin da ya samu ta hanyarsa, ka da ya yi garajen tara kayan more rayuwa ta hanyar sata da zamba
Domin haka mutum a gidan duniya kamar a filin kokawa ya ke, abokan karawarsa su ne shaiɗan da son zuciya da ruɗin duniya, wanda ya yi jarumta ya nana su da ƙasa, to shi ne zai ci kambu kuma shi ne wanda zai zama jarumi, gwarzon maza (ko kuma jarumai mata!)
Domin haka ne Allah Ya aiko da Manzanni suka bayyana dokoki, suka ajiye ƙa’idoji, suka tsara hanyoyi, suka shata iyakoki. Mutumin da ya tsaya idan aka tsayar da shi, ya kuma nufi inda a ka umarce shi ne wanda ya kaywar da waɗancan abokan kokawa tasa, kuma shi ne ya ci jarrabawa, don haka sakamakosa shi ne samun dacewa da yardar Allah. (Allah Ya sa mu dace).

Idan mutum ya yi tunani, zai gane cewa, yin haƙuri a cikin bin Allah, da kuma yin duniya wajen saɓawa son zuciya ba a cikin shari’ar addini kawai yake ba, a’a har ma cikin shari’ar rayuwa. Akwai abubuwa da baya so, amma haka yake haƙura ya tafi yadda ake tafi da shi a cikinsu. Ba a komai ne zai gudanar da rayuwarsa yadda ya ke so ba, kamar tsufa da rashin lafiya da mutuwa waɗanda ba shi da tasiri a kansu. To, haka ma a cikin bin shari’ar addini, sai ya haƙura ya bi doka ko ta yi masa daɗin ko ba ta yi masa ba, kamar yadda ya saba yi, a shari’ar rayuwa. Abu dai mafi muhimmanci wanda yin tunani a kansa zai taimaka mana wajen ƙara yin haƙuri cikin bin Allah shi ne, duk abin da shari’a ta umarce shi da shi, to wannan abin amfani ne da alhari gare shi, a duniya da lahira, kuma duk abin da shari’a ta haramata masa, to sharri ne a gare shi da masifa da ƙangi da shiga halin ƙaƙa-naka-yi. Allah Ya kiyashe mu, ameen.
Duba ka gani; Allah Ya wajabta yin lmani da shi (Allah Shi kaɗai, wanda ba shi da abokin tarayya, mai iko ne bisa komai. wanda ya halacci dukkan halitta).kuma ya haramta imani da yin bauta ga wani wanda ba Shi ba, ko Mutum ko Aljan ko Mala ika ko tauraro ko Rana ko Wata ko Dutse ko itace, da sauransu. Wanda ya ke dukkansu samar da su Allah Ya yi gajiyayyu ne mubuƙata ne ba su da ikon yin wani abu sai da izinin Allah.Ka ga a nan wanda ya yi aiki da umarnin Allah shi ne zai amfana, saboda zai samu nutsuwa a rayuwarsa. Wanda ya saɓa masa kuma shi ne zai cutu domin zai rayu cikin ruɗani, da damuwa.
Haka kuma, Allah Ya halatta madara da zuma, amma ya haramta giya, kuma ya halatta ciniki da saye da sayarwa na ƙa’ida, amma ya yi aure daga mace ɗaya zuwa huɗu, amma Ya haramta zina. Allah Ya halatta zaman lafiya,, zumunci, da mutunci, da alheri, da ƙaunar juna, amma Ya haramta gaba, da ƙullata, da kinibibi, da maunafunci, da ƙeta, da dai kowane mugun hali. Dukkan abin da Allah Ya halatta mana alheri ne garemu, kuma dukkan abin da ya haramta mana sharrine. Allah Ya sa mu gane, ameen.

Domin karanta cikakken bayani akan Dabarun Yaƙi danna nan.

Wannan bayani anciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Yake Sonsa wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.