A Musulunci, rayuwar aure ba ta kyautatuwa ta zama nagartacciya, har sai idan an aiwatar da ita ta salon da Musulunci ya tsara, ta hanyar ɗora wa ma’aurata wasu nauye-nauye da ake buƙatar da su sauke su kamar haka:
1. Haƙƙoƙin mace a kan mijinta.
2. Haƙƙoƙin miji a kan matarsa.
3. Haƙƙoƙin da miji da mata suke tarayya a kansu.
4. Haƙƙin wanda mutuwa ta raba shi da abokin zamansa daga cikin ma’aurata.
1. Haƙƙoƙin Mace a Kan Mijinta:
(a) Sadaki: Wanda bayaninsa ya riga ya gabata.
(b) Ɗora iyali a kan bin Allah tare da rainonta da kyawawan ɗabi’u.
Shi wannan haƙƙi na biyu da samuwarsa da kuma ɗorewarsa ne mace za ta kyautata tsakaninta da ubangijinta, da kuma tsakaninta da bayinsa.
Da farko Allah Mai girma da Buwaya ya ce:
“Ka ambaci (labarin) Isma’il cikin wannan littafi (Alƙur’ani), haƙiƙa shi mai cika alƙawari ne, kuma Annabi ne Manzo. Ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsaida sallah da kuma ba da zakka, sannan kuma shi yardajje ne a wajen ubangijinsa ).
Abin nufi a nan, Annabi Isma’il yardajjen Allah, a zamansa da iyalinsa yana umartar su ne da su riƙa tsayar da sallah, kuma su riƙa bayar da zakka, domin alaƙarsu da Ubangiji ta kyautata.
Sannan kuma mun ji cewa shi mutum ne mai cika alƙawari, sanin kowa ne kuma duk wanda yake haka za ka tarar yana ƙoƙarin rainon iyalinsa da yin haka. Sannan kuma Allah ya ce da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi):
“Ka umarci iyalinka da tsaida Sallah kai ma kuma ka yi haƙurin dawwama a kan tsaida ita, ba za mu tambaye ka dukiya ba, mu ne ma za mu azurta ka, kuma kyakkyawan ƙarshe (duniya da lahira ) ga masu tsoron Allah yake”.
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya aiwatar da wannan umarni da Allah yayi masa kamar yadda Imamut- Tirmizi ya rawaito hadisi cewa, an karɓo daga Ummu-salama Allah ya yarda da ita ta ce:
“Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan watan Ramadan ya rage kwana goma ya ƙare, ba ya barin ko da mutum ɗaya daga cikin mutanen gidansa matukar dai zai iya yin sallar dare face sai ya tashe shi (domin ya yi)”.
To, ‘yan uwa, idan Annabi bai bar sallar nafila ta wuce mutanen gidansa ba; ina kuma ga sallar farilla. Sannan kuma Allah Maɗaukaki ya ce:
“Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, ku tserar da kanku da kuma iyalanku (daga shiga ) wuta (wadda ) mutane da duwatsu ne makamashinta, kuma akwai wasu ƙarfafan mala’iku masu kauri da suke tsaron ta, waɗanda ba sa saɓa wa Allah abin da ya umarce su da shi, kuma suna aikata duk abin da aka umarce su da shi”.
A wannan ayar kuma kiran muminai gaba ɗaya Allah ya yi, sannan ya umarce su da su dage su bi irin turbar da Annabawa suka bi, wajen ɗora kansu da iyalansu akan hanyar bin Allah da nisantar saɓa masa, domin su gudu tare su kuma tsira tare. Har wa yau, Bukhari ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Malik ɗan Huwairis Allah ya yarda da shi yace: Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da (ayarin) jama’ar Abdul- Kais da suka zo wajen
“Su kiyaye imaninsu da kuma ilmin da ya sanar da su shi, sannan kuma ya ce da su, “Ku koma wajen iyalanku ku sanar da su”.
Saboda waɗannan dalilan da muka ji ya zama lallai akan miji ya sanar da matarsa ilmin yadda za ta bauta wa ubangijinta, ko kuma ya tura ta inda za ta je ta koya, kamar yadda matan sahabbai suke zuwa wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) su koyo addini.
Bayan haka, an karɓo daga Amru ɗan Ahwas Allah ya yarda da shi ya ce, ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa na bankwana yana cewa: “Ku saurara, ku yi wa mata wasici da alheri”. ( Tirmizi ne ya rawaito shi ). Haka kuma an karɓo daga A’isha (Allah ya yarda ita ) ta ce: ” (wata rana ) Yahudawa sun zo wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai suka ce da shi: “Assamu alaikum” wato halaka ta tabbata a kanku, a maimakon su ce: “Assalamu alaikum” wato amincin ya tabbata a gare ku, jin haka, sai A’isha ta ce: Halaka a kanku, Allah kuma ya tsine muku; ya yi fushi da ku. Sai Annabi ya ce da ita: ‘
A a A’isha, yi a hankali, ina umartar ki da yin sauƙi, kuma ki kiyayi kausasawa da munanan maganganu. Sai kuwa ta ce da Annabi ba ka ji abin da suka ce ba ne? Annabi ya ce: To ke ba ki ji abin da na ce da su ba? Ai na mayar musu da martani da cewa a kansu dai. Sai Allah ya amsa mini addu’ar da na yi musu, su kuma ba zai amsa musu wadda suka yi mini ba. (Bukhari ya rawaito shi).
A nan idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa, waɗannan hadisai suna ɗora magidanta ne a kan hanyar da ya kamata su ɗora matansu a kai, ta nusar da su yadda ya kamata su zauna da mutane a cuɗanyarsu da su. Allah dai ya ba mu ikon kulawa da kuma aiki da wannan koyarwar ta Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), amin.
(c) Samar wa Mace Mazauni (Gida ko ɗaki):
Shi kuma wannan nauyi ya hau kan miji ne a sakamakon faɗar Allah Madaukaki da ya ce:
“Ku zaunar da su (mata) a inda kuke zaune daidai halinku, kar ku cuce su don ko ƙuntata musu”. Da kuma faɗar Allah Maɗaukaki cewa: “Ku ji tsoron Allah Ubangijinku kada ku fitar da su daga ɗakunansu, suma kada su fita, sai dai idan sun zo da mummunan aiki mabayyani, waɗancan iyakokin Allah ne, to haƙiƙa ya cuci kansa”.
Saboda haka, haramun ne mai gida ya ce da matarsa ta fice ta bar masa gidansa, ko ɗakinta don ya sake ta, matuƙar dai ba ta gama idda ba. Haka kuma ita ma mace bai halatta ta bar gidan mijinta ba don ya sake ta har sai bayan ta gama idda. Wannan sai ya tabbatar mana da cewa alhakin miji ne ya tanadar wa matarsa mazauni.
(d) Ciyarwa da Tufatarwa:
Haka ma ciyarwa da tufatarwa, haƙƙƙi ne da mace take da shi a kan mijinta. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki ya ce: “Ciyar da mata da tufatar da su gwargwadon iko, wajibi ne a kan wanda aka haifawa ɗa, ba a ɗora wa (kowanne) rai sai gwargwadon ikonsa”.
A wata ayar kuma Allah Maɗaukaki ya ce: “Mai yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuma aka ƙuntata arzikinsa, (wato talaka), to, ya ciyar daga ɗan abin da Allah ya ba shi, Allah ba ya ɗorawa kowacce rai sai abin da ya ba ta, da sannu Allah zai sanya sauƙi bayan matsi (tsanani)”.
A hadisance kuwa, an karɓo daga Hakim ɗan Mu’awiya daga mahaifinsa (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Na tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa, menene haƙƙin matar kowannenmu a kansa? Sai ya ce: “Ka ciyar da ita idan ka ci, ka kuma tufatar da ita idan ka tufata…”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi).
Sannan kuma sahabin Annabi Amru ɗan Ahwas ( Allah ya yarda da shi ) ya ce: Haƙiƙa ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa na bankwana yana cewa: “Ku saurara, haƙiƙa matanku na da haƙƙi a kanku, haƙƙinsu a kanku, ku kyautata tufatar da su, da ciyar da su”.( Tirmizi ne ya rawaito).
Bisa dogaro da waɗannan dalilai, ya zama tilas a kan miji ya ciyar da matarsa, ya tufatar ita gwargwadon irin halin da yake da shi. Sannan kuma amana ce a wuyan miji ya ciyar da matarsa da halal ba da haramun ba.
Haɗarin Ƙuntata wa iyali wajen ciyarwa
Musulmin da Allah ya yi masa yalwar abin da zai ciyar da iyalinsa, da abin da zai tufatar da su, amma sai ya zama yana ƙuntata musu, ta hanyar ƙin wadata su da abin da zai ishe su, to, a zahirin gaskiya babu wanda yake cuta sai kansa, domin kuwa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ya isa mutum laifi, ya riƙa tozarta wanda yake ci a ƙarƙashinsa”. (Abu Dawuda ne ya rawaito shi).
Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) yace: Haƙiƙa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya ce: “Babu ranar da bayi za su wayi gari a cikin ta, face sai wasu mala’iku biyu sun sauko, sai ɗaya daga cikinsu ya kama cewa: “Ya Allah ka bai wa mai ciyarwa”. Sai shi kuma ɗayan ya ce: “Ya Allah ka haɗa matsolo da asara”. (Bukhari da Muslimu ne suka rawaito shi). Don haka, ‘yan uwa sai a yi hattara.
Bayan haka, da Allah zai datar da iyalan malam matsolo da samun wata kafa da za su riƙa ɗiban abin da zai ishe su daga cikin dukiyarsa, a shari’ance, ba su yi laifi ba, in sun ɗebi abin da zai ishe su, matuƙar dai ba za su yi ɓarna ba.
An karbo daga A’isha (Allah ya yarda da ita) ta ce: “Hindu ‘yar Utba matar Abi Sufyanu ta shiga wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai ta ce: “Ya Manzon Allah, mijina Abu Sufyan matsolon mutum ne, ba ya ba ni abin ciyarwa da zai ishe ni, kuma ya ishi ‘ya’yana, sai in na ɗebi wani abu daga cikin kudinsa ba da saninsa ba, shin ko ina da laifi game da hakan da nake yi? Sai Annabi ya ce: “Ki ci gaba da ɗaukar abin da zai ishe ki ya ishi ‘ya’yanku daga kuɗinsa”. Wato yin hakan ba laifi ba ne. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).
Sannan dai ita wannan ta’ada ta matsolanci, haɗarin ta yana da yawan gaske, domin kuwa tana sa mai yin ta ya rasa samun alherin da masu ɗaukar abin hannunsu su bayar suke samu:
Na Farko: zai rasa samun addu’ar alherin da mala’ika yake yi wa masu ɗaukar abin hannunsu su bayar duk wayewar garin Allah, kamar yadda muka ji.
Na Biyu: Ya rasa kwarjinin da masu bayar da abin hannunsu suke samu a wajen waɗanda suke agazawa.
Na Uku: An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Hannun da yake bayarwa ya fi hannun da yake karɓa. (In za ka bayar) ka fara da wanda nauyinsa ke kanka, ka ba wa babarka, da babanka, da ‘yan uwanka, sannan wanda ya fi kusa da kai, sai wanda yake da kusanci da kai”. (Nasa’i da Darakudni ne suka rawaito shi, kuma Darakudni da ibn Hibban suka inganta shi).
Domin karanta cikakken bayani a kan Dokokin Suturar Musulma danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.
Edita@rumasau-kallamu