Yadda ake Magance Ciwon Damuwa

2
151

Jin ɓacin rai ko shiga cikin damuwa abu ne wanda yake cikin rayuwa. Mutane su kan ɓata mana rai, ko suyi abinda zai saka ka cikin damuwa, abubuwa su kan iya juyawa ba ta yadda ka tsara ba, mutuwa tana sa mu rasa mutanen da mukeso ko ta tarwatsa mana wani tsari da mukayi. Idan ɓacin rai ko damuwa yana damunka na tsawon lokuta har ya wuce makwanni ko watanni, ko kuma su kan zo maka akai-akai ta  yadda suke hanaka rawar gaban hantsinka da juya maka yadda kake mu’amala da mutane da jin dadin rayuwarka, to fa mai yiwuwa ne kana fuskantar ciwon damuwa. Indai zaka iya samun bayanai, taimakon ƙwararrun likitoci da ma’aikatan lafiya, da goyon baya a kusa dakai, ko da ciwon damuwarka mai tsanani ne, to mai matukar warkewa ne.

Amma kuma ko ma menene, ka saka al’amarin  warkar da kanka a hannunka kuma ka ɗauki mataki idan kana fama da cutar damuwa.

1. Hanya ta farko;

Yadda zaka gane inda asalin cutar damuwarka take da yadda zaka magance ta.

  1. Ka duba alamomin cutar damuwa.

Idan baka riga ka nemi taimako akan cutar damuwarka ba, yanada kyau ka nema kuma kar kace

zakayi hakan kai kadai. Dayawa daga cikin wasu  alamomi sunada alaƙa da cutar damuwa. Idan kanada daya ko mafi daya daga cikin waɗannan alamomin da za’a lissafo a ƙasa, to ka nemi shawara daga wajen likita. Alamomin cutar damuwa sun haɗa da;

  • Rashin yin ayyukan daka saba yi a rayuwarka ta yau da kullum
  • Jin kaɗaici da rasa zamantakewa ta abokanai
  • Rashin jin daɗin abubuwan da kakejin daɗin su a da, kamar su karatu, wasanni, da sauran su.
  • Jin kasala, gajiya, da jin cewa yin abubuwa zasu ɗauke maka ƙarfinka su sakaka gajiya.
  • Yawan shiga cikin baƙin ciki, harda kuka a wani lokacin.
  • Shiga cikin yanayin juyayi da tunanin kai ba komai bane.
  • Shiga cikin yayayin baƙin ciki akai-akai na aƙalla tsawon sati biyu.
  • Jin cewa kai bakada amfani, ɗorawa kai laifi da rashin jin cewa zaka iya yin wani abu mai amfani.
  • Yin barci kaɗan ko dayawa ba yadda ka saba ba, ko rashin yin barci.
  • Ƙarin ƙiba ko rama, yawan cin abinci ko rashin cin abinci.
  • Wahalar yin tunani da maida hankali, rashin daidaito wajen tunani, rashin samun
  • daidaito wajen yanke shawara,yin mantuwa.
  • Rashin yarda da cewa wani abin kirki zai sameka ko yiwa kai mummunan zato, ko ka dinga jin cewa rayuwarka batada amfani. Wannan tunanin ma zai iya saka ka kaji kaman ma ba rayuwa kake ba.
  • Ciwon jiki, ciwon kai, da wasu ciwukan da basa tafiya ko ansha musu magani. Zasu iya zuwa ba tare da wani dalili ba.
  • Jin abu na damunka wanda yake sakaka rashin zama da nutsuwasau da yawan lokaci.
  • Tunanin kashe kai, tunani akan so ka mutu, ko tunani akan hanyoyin da zaka bi ka kashe kanka.
  1. Ka tuntuɓi likitanka.

Kaje likitanaka ya dubaka ko da akwai masu abubuwan da suka danganci ciwo ko ɓangaren lafiyarka wanda kan iya janyo maka ciwon damuwa.

Wani ciwon damuwar yana zuwa a sanadiyar wani bangare da ya danganci ciwon ka, ko maganin ka.

A wani lokacin ma ciwo na lafiya ko abin da ya dangance shi yana iya kwaikwayon ciwon damuwa. Yanada amfani likitanka ya duba ya gano alamomi na bayyane wanda ke buƙatar magancewa, ko kuma kawar da wasu dalilai na cikin yanayin da kake ciki. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka danganci ciwo ko magani wanda zasu iya janyo ciwon damuwa:

  • Yawanci ko karancin wasu sinadarai, musamman wanda suke fama da ciwon da ake bukatar a rage su.
  • Matsalar rashin daidaiton sinadarai a jiki.
  • Magunguna: wasu magungunan na janyo ciwon damuwa.
  • Ciwuka masu alaka da ciwon damuwa. Ciwon damuwa na yawan tafiya da ciwon tunani.
  • Ciwukan da suka ta’allaƙa da mata kawai, kaman ciwon damuwa na bayan haihuwa ko yanayi da mata ke shiga kafin jinin al’ada ko bayan jinin al’ada.
  1. Kayi bincike akan ciwon damuwa domin ka samu kyakykyawan fahimta akan ciwon damuwa.

Ka koyi abinda zaka iya koya akan ciwon damuwa. Ƙarawa kanka ilimin ciwon damuwa akan yanayin da kake ciki zai taimaka maka wajen magance shi. Ilimin ciwon damuwa nada matuƙar amfani saboda shi zai sa ka ƙara yarda cewa ciwon na gaske ne, kuma abu ne wanda ya kamata a magance, sannan kuma akwai hanyoyi da dama da ake bi a magance shi.

  • Kaje gidan ajiyar litittafai na kusa da kai ka aro litittafai akan ciwon damuwa, ciwon tunani da farinciki ka karanta.
  • Ka duba kan yanar gizo a wuraren da aka yarda dasu kuma aka sahalewa bada bayanai wanda suka danganci lafiya, ka karanta rubuce-rubuce akan ciwon damuwa.
  • Kayi amfani da ilimin da ka samu na ciwon damuwa kaima ka ilimantar da wasu wanda basuda wannan ilimin, hakan kan taimaka maka wajen rage nauyin ciwon damuwarka.
  1. Ka jaraba zuwa wajen ƙwararrun masana akan cutar damuwa.

Ɗaya daga cikin hanyoyi masu matuƙar amfani domin kawar da cutar damuwa shine zuwa a samu zama da ƙwararrun masana akan cutar damuwa. Akwai hanyoyi da dama da ake amfani dasu kuma kowana ƙwararre yanada tashi hanyar da yake amfani da ita. Uku daga cikin mafi shaharar hanyoyin magance ciwon damuwa ta hanyar zama da ƙwararru sun haɗa da:

  • Samun zama da ƙwararre wanda zai taimaka maka wajen gano, fuskantar, yaƙar da sauya tunani mara kyau.
  • Samun zama da ƙwararre wanda zai taimaka maka wajen koyar dakai yadda zaka juya halayyarka mara kyau zuwa ga mai kyau.
  • Samun zama da ƙwararre wanda zai taimaka maka wajen magance yawan shiga yanayi na damuwa da kakeyi ta hanyar duba yadda alamomin cutar ciwon damuwa ke a jikinka.
  1. Ka jaraba amsar magani.

Wasu likitocin ko masana zasu baka magunguna. Kayi tambaya akan magungunan da aka baka, musamman tsawon lokacin da ya kamata ka ɗauka kana sha da kuma abubuwan da sukeyi in an sha. Idan kaji wani sauyi wanda kana ganin baizo daidai da abinda ya kamata kaji ba, ka faɗawa likita ko ƙwararren da ya baka maganin, ƙila sai an sauya maka yadda zaka sha maganin ko kuma a sauya maka maganin baki ɗaya.

  • Idan bakason amfani da magani, ka faɗawa likitanka. Idan kayi bincike ko karatu akan ciwon damuwa, zaka ga akwai wasu hanyoyin da ake bi ana magance ciwon damuwa ba lallai sai tare da magunguna ba, kai da likitanka zaku zauna ku tattauna, sannan ku duba hanyar da ta dace da kai.
  1. Ka jaraba amfani da wasu hanyoyin magance ciwon damuwa masu saka nishaɗi.

Kayi bincike akan wasu hanyoyin da ake bi ana magance ciwon damuwa wanda suke sa nishaɗi da jin daɗi.

  • Karatu akan abinda kakeso.
  • Fita zuwa wajen shaƙatawa, ko kai kaɗai, ko tareda wasu.
  • Yin abubuwan da kakeso wanda suke saka nishaɗi.

2. Hanya ta biyu:

Yadda zakayi sauyin inganta yanayin tafiyar da rayuwarka.

  1. Kayi barci yadda ya kamata.

Yin barcin da ya kamata yana taimakawa wajen inganta lafiya. Rashin samun ishashshen barci yakan janyo tunani mara kyau kuma hakan yakan zama wani halayya mara kyau da yake saka tashi da daddare yana hanaka barci. Tashi daga barci kaji kasala ko gajiya na ɗaya daga cikin matsalolin da ake fuskanta idan ana fama da cutar damuwa, kuma yawan barci yakan bar masu fama da ciwon damuwa cikin kasala.

  • Kayi ƙokarin tsara lokacin barci da tashi a kullum.
  • Ka raba ɗakin kwanciyar ka da abubuwan da zasu dinga ɗauke maka hankali.
  1. Motsa jiki.

Motsa jiki yakan saki wasu sinadarai a jikin mutum wanda suke saka kuzari. Ka fara motsa jikin ka da kaɗan, da kaɗan har ka saba kazo kanayin mai ɗan yawa.

  • Ka nemo abokan yin motsa jiki wanda zaku dinga yi tare, hakan yana sa kaji kanada ƙarfin gwiwar yi ganin ba kai kaɗai bane kakeyi.
  • Yin wasanni na motsa jiki na daga cikin hanyoyin da suke sa mutum yaji ya motsa jikinshi yadda ya kamata. Ka nemi wasan motsa jiki da kafiso ka dinga yi.
  1. Kaci abinci mai amfani da gina jiki.

Ka rage shan sukari, da cin abinci wanda aka riga aka sarrafa wanda sinadaran shi sun fita, da cin abinci mara amfani.

Ka dinga cin kayan lambu, kayan ganye, da abincin da ba’a sarrafa ba wanda yakeda sinadarai a jikin shi.

Cin abinci mai amfani da gina jiki na matuƙar taimakawa wajen inganta yanayin mutum.

  1. ka gyara tsaftar ka, da yanayin jikin ka, da shigar ka.

Shiga cikin yanayin damuwa nada sauƙi idan baka gyara tsaftar ka, yanayin jikin ka, da shigar ka. In kana tsafta a kullum da kula da jikin ka, yana inganta yanayin ka izuwa ga mai kyau, hakan kuma yana inganta yanayin lafiyar ka wanda yake rage shigarka yanayin ciwon damuwa.

  1. Ka ƙarfafa mu’amalar ka mai kyau da mutane, da samun goyon baya.

Samun goyon baya daga wajen mutanen da suke sonka da ƙaunar ka nada matuƙar amfani a hanyar magance ciwon damuwarka. Ka faɗawa mutanen da ka yarda dasu cewa kana fama da ciwon damuwa kuma zakaji dadi idan zasu fahimce ka kuma su tausaya maka. Yanada kamar wuya mutane su fahimce ka har su taimake ka idan har basu san abinda yake damunka ba. Sanin halin da kake ciki zai taimaki mutane su baka goyon bayan da ya kamata su baka.

  1. Ka kasance cikin mutane masu amfani.

Kayi magana da abokanai, ƴan uwa, da mutanen arziƙi wanda suke saka ka farin ciki kuma kake jin daɗin kasancewa tare dasu.

3. Hanya ta uku:

Yadda zaka sauya halayyar ka. 

  1. Ka kasance kanada abin da kakeyi wanda yake hanaka zaman banza.

Kasancewa cikin aikin yi yana taimakawa wajen kawar da tunani mara kyau daga zuciyar ka. Ga masu fama da cutar damuwa, bin hanya ta farko ta magance ta itace mafi wahala, saboda haka, yin abubuwan da suka dace su zasu taimake ka wajen gyara al’amuran rayuwarka.

  • Ka dinga yin abubuwan da kakejin daɗin yinsu wanda suke saka ka nishaɗi.
  • Ka samu ka tsara yadda zaka dinga tafiyar da rayuwarka a kullum ta hanyar tsara jadawalin abubuwan da kake son kayi.
  1. Ka ci/sha abinda kakeso daga lokaci zuwa lokaci sannan kayi abubuwan da suke saka ka farin ciki.

Ciwon damuwa yana zuwa da yanayi na rashin   farin ciki, in kana cin/shan abinda kakeso daga lokaci zuwa lokaci sannan kana abubuwan da suke saka ka farin ciki, hakan yana taimakawa wajen rage samuwar faɗawar ka cikin ciwon damuwa.

  1. Ka samu littafi na musamman ka dinga rubuta abubuwan da kake fuskanta game da ciwon damuwarka na yau da kullum.

Ka samu littafi ka dinga rubuta al’amuran rayuwarka na yau da kullum game da ciwon damuwarka a inda kai kaɗai ka sani, inda babu wanda zai gani sai kai. Rubuta abubuwan da kake fuskanta game da ciwon damuwa a rayuwarka na yau da kullum kan taimaka wajen rage ko cire damuwar da take tattare dakai, saboda hakan yana nuna kasan abubuwan dake damunka kuma a sannu a hankali zaka nemo hanyoyin magance su.

  1. Ka taimaki wasu.

Taimakon wasu hanya ce mai kyau wadda take taimakawa mutum wajen fita daga cikin ciwon damuwarshi. Hakan yana cire maka tunanin kan ka ya koma kan wasu wanda ke da amfani saboda hakan yana hanaka shiga damuwa akan kan ka ne.

4. Hanya ta huɗu:

Yadda zaka sauya yanayin tunaninka daga mara kyau zuwa mai kyau. 

  1. Ka mayar dashi matsayin tunani na hanyar zuwa ga lafiya.

Ciwon damuwa yakan sa kaji kamar bazai ƙare ba, musamman idan ya haɗu da gajiya/kasala sai kaji komai ma yana maka wahala. Saboda haka, yanada kyau da amfani ka dinga kallon abun a matsayin tafiya wadda akeyi da taku ɗai-ɗai, a maimakon tafiyar da ake tashi ɗaya na nan da nan. Akwai lokacin da zakaji bakason ma taɓuka komai na gyara yanayin tunanin da kake ciki har ka dinga tambayar kanka wasu abubuwan kana kokwanton kanka, amma kuma a dai dai irin wannan yanayin ne ya kamata ka zage dantsen ka wajen ganin baka bar kanka ka tsunduma cikin ciwon damuwa ba.

  1. Ka fahimci muhimmancin rabuwa da tunani mara amfani.

Fahimtar muhimmancin rabuwa da tunani mara amfani yana taka rawa tare da bada gudun mawa matuƙa wajen magance ciwon damuwa. Masu fama da ciwon damuwa suna fama da tunani mara amfani sosai wanda hakan ƙara jefa su cikin ciwon damuwa yakeyi.

  1. Ka sauya yadda kake tunanin ka.

Daga cikin samun ci gaba wajen magance ciwon damuwarka shine ka gane yanayin yadda kake tafiyar da tunanin ka da abubuwan da suka kamata ka mayar da hankalinka a kansu.

  • Ka yarda da kanka.
  • Ka dinga faɗawa kanka kalmomi masu ƙarfafa maka gwiwa.
  • Ka yarda cewa duk wani tunani mara kyau ko amfani da yake tattare dakai zai tafi.
  • Ka lissafo abubuwan da suke da kyau a tattare dakai wanda kake alfahari dasu kuma kana jin daɗin su saboda suna karfafa maka gwiwa.
  • Ka dinga yanke lissafaffiyar shawara mai kyau kuma kayi aiki a kanta.
  1. Ka dinga kallon yawancin abubuwa da suke faruwa dakai a rayuwarka da ido mai kyau.

Kada ka mayar da hankalinka akan abubuwan da basuda daɗi a rayuwarka, maimakon hakan, ka zauna ka kalli abubuwan da suke faruwa a rayuwarka da ido mai kyau.

Ka godewa Allaah bisa ni’imomin da ya haɗaka dasu.

Ka kalli waɗannan abubuwan da suke da matuƙar muhimmanci a rayuwarka wanda Alllaah ya azurtaka dasu kuma kake jin daɗin su ka godewa Allaah.

  1. Ka sauya yanayin yadda kake magana.

Yanayin yadda kake magana shima yana taka rawa wajen rage ko ƙara yanayin yadda tunaninka yake. Ka dinga magana cikin farin ciki da annushuwa ta yadda zaka dinga ganin komai ta fuska mai kyau ba ta fuskar yadda zaka dinga ganin komai a duhu ba.

  1. Ka yarda cewa ciwon damuwa zai iya dawo maka bayan ka samu sauƙi na ɗan wani lokaci ko lokaci mai yawa.

Indai kana fama da ciwon damuwa, idan ka samu sauƙi na ɗan lokaci ko lokaci mai yawa, akwai babbar yiwuwar dawowarshi gareka.

Yarda da hakan yakan rage maka ƙara faɗawa cikin wani hali na ciwon damuwa wanda yafi wanda ka saba shiga saboda zaka iya gane alamomin shi da kuma abubuwan da yake bijiro maka dashi kafin yazo da kuma lokacin da yazo.

Shawarwari

  • Ka kasance kana cikin yin wani abu da zai hanaka zaman kaɗaici da zaman banza,ko na sana’a, ko karatu. Zaman kaɗaici da zaman banza, ko zama ka dinga tunani akan duk abubuwa marasa kyau dasuke tattare a rayuwarka ba tare da ka faɗawa wani ba na taimakawa wajen ƙara jefaka cikin ciwon damuwa.
  • Ka guji kwatanta kanka da wani/wasu.
  • Ka kewaye kanka da abubuwa masu amfani a rayuwarka. Ka cire duk wani abu da yake ɓata maka rai ko yake tuna maka da wani abu ko lamari mummuna.

Gargadi

  • Barin ciwon damuwa a tattare dakai ba tare da magance shi ba da zummar/fatan zai tafi da kanshi abu ne mara kyau, da wasa da lafiya, da ganganci. Yanayin tsayin ciwon damuwa ba tareda magance shi ba, yanayin tsayin munin cutar. Yawanci/duka cutar damuwa suna munana ne idan aka barsu ba’a nemi yadda za’a magance su ba. Idan kaji kana fama da cutar damuwa, ka nemi taimako da gaggawa.
  • Ciwon damuwa yakan saka mutane su dinga jiwa kansu ciwo a jikinsu ko kisan kai ma gaba daya. Ka tuna duk wani zaɓi da kake dashi mai kyau a rayuwarka game da samun sauƙi kamar yin magana da mutane akan abinda ke damun ka, samun goyon baya da kuma neman taimako na musamman.
  • Kawai don kanada alama ƙwaya ɗaya ta ciwon damuwa baya nuna cewa kanada ainihin cutar ciwon damuwa. Kada ka tsoratar da kanka akan hakan. Idan kanada damuwa akan hakan, kaje ka samu likitoci ko ƙwararru na musamman a wannan fannin da zasu taimaka maka.
  • Idan kana neman wanda zai taimaka maka wajen magance maka ciwon damuwarka, kaje wajen wanda ka kasance ka yarda dashi da kuma ƙwarewarshi, sannan kayi tambaya kuma ka fahimci banbancin tsakanin likitoci/ƙwararru masu zama na musamman wanda suke magance ciwon damuwa da sauran ciwuka irinshi. Idan ka jaraba wani likita/ƙwararre bai maka ba, ka sauya zuwa wani har sai ka samu wanda ya dace dakai.
labarin da ya wuceMatakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)
Labarin na GabaSanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i
Sufian Ibrahim
Sufian Ibrahim marubuci ne, kuma therapist ne, musamman mental health therapy da addiction therapy, poet ne, spoken word artist ne, jakadan zaman lafiya ne, sannan kuma mai san yaga chanji mai kyau a yanayin rayuwar al’umma ne. Yana karatu ne a Jami’ar Bayero dake Birnin Kano (BUK), inda yake karantar haɗakar nazarin halittu a ɓangaren kimiyyar rayuwa.

2 SHARHI