Matakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)

0
202

Wannan wasu matakan kariya ne da mace da ta ke da shirin ɗaukar ciki ya kamata ta samu tun kafin samun cikin, domin samun cikarkiyar lafiya lokacin rainon ciki da kuma haihuwa.

MENE YA SA KIKE BUƘATAR MATAKAN KARIYA KAFIN SAMUN CIKI?

Tabbatacciyar lafiyar mace kafin samun ciki, yana ɗaya daga cikin manyan mahangar samun lafiyayyen ciki da haihuwa.

MATAKAN KARIYA.

  1. Ga macen da ta ke da wata cuta da ta ke shan magani a kai, ya kamata likita ya tabbatar mata da cewar cutar ba ta matakin da zata iya ba ta matsala idan ta samu ciki, wannan cututtuka sun haɗa da:
    -ciwon siga
    -Sikila
    -Asima
    -Ciwon zuciya
    -Hawan jini…… Da sauran su.
    Baya ga haka, akwai wasu maganin da ake sha a waɗannan cututtuka, wanda ka iya ba wa jaririn da za ta haifa matsala, don haka, likita zai canza mata su zuwa ga wanda ba su da matsala a kan jariri.
  2. Folic Acid
    Wannan magani mace kan fara shan sa kafin samun ciki da kuma wata 3 na farkon ciki, bisa shawarar likita. Yana bayar da kariya a kan haihuwar yara masu ƙaramin kai ko buɗaɗɗiyar laka.
  3. Abinci.
    Akwai buƙatar mace ta ƙara samun abincin mai gina ciki da ƙarin lafiya domin ita kanta da kuma jaririn da zai zauna a cikinta.
  4. Barin shan magani barkatai ba tare da shawarar likita ba, saboda akwai magungunan da suke bayar da matsala ga jariri ko su kawo ɓarewar cikin, idan aka samu.

Danna koren rubutun nan domin karanta Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu) ko yadda ake amfani da na’urar gwajin ciki ko Yadda zaki kare kanki daga Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

labarin da ya wuceCiwun Sanyi (TOILETS INFECTION)
Labarin na GabaYadda ake Magance Ciwon Damuwa