Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu)

0
280

Shin waɗanne alamu ne mace za ta ji ko ta gani idan tana ɗauke da sabon ciki wato juna biyu, ta yadda za ta ga ne tun kafin ta je asibiti a tabbatar.

Haƙiƙa ba kowace mace ce ta kwan da sanin cewa babban abin da ke kawo ɓatan wata (wato ko juna biyu rashin ganin al’ada ba) shi ne samun juna biyu ba. Musamman a sabbin aure ko kuma a mata marasa kamun kai.

Bayan juna biyu kuma cuttukan da ke sa shigar ƙwayoyin cuta ciki ko bakin mahaifar mace [uterus] su ne kan gaba wajen kawo ɓatan wata (rashin ganin haila), ko rikicewar lissafin wata.

SAURAN ABUBUWAN DA KE KAWO ƁATAN WATA SUN HAƊA DA:

  1. Shayarwa
  2. Halin damuwa, ƙunci ko fargaba
  3. Rashin lafiya a yan tsakani.
  4. Bayar da gudunmawar jini
  5. Rashin zama guri guda.
  6. Rashin samun hutu, kamar a masu wasannin motsa jiki ko doguwar tafiyar ƙasa.
  7. Wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai, walau na asibiti ko na gida.

MENE NE YA KE TABBATAR DA CIKI?

Ma’ana waɗanne alamu mace mai juna biyu za ta ji ta tabbatar ciki ne? Ga su nan a zayyane:

A watan farko, mace za ta yi ɓatan wata, bayan ƴan satittuka, sai ta fara samun;

  • Tashin zuciya da sassafe, har da amai a wasu lokutan, koda kuwa ba ta ci komai ba.
  • Saurin gajiya, kasala, ko yaya ta yi wani ɗan aiki.
  • Ko Ganin jiri (dizziness) idan ta zo miƙewa bayan jimawa a zaune.
  • Yawan zubar da miyau, tare da jin sa yana yawan taruwa ga kuma kauri.
  • Zazzaɓi amma ba me zafi can ba, haka dai kurum za ta ji kamar ba ta da lafiya
  • Sai rashin son ƙamshin abu, koda turare ne a wasu lokuta. Tare dajin za6in wani abun daban wanda kafin a jima sai ta ji ta bar sha’awar wannan, ta fara sha’awar wani daban.

BATUN GWAJIN JUNA BIYUN FA?

A wane lokaci ne ake so a je a yi gwajin juna biyun in ana kokonton likita ?

-Akan tabbatar ta hanyar auna fitsari ko jini.

-Sannan sai ta scanning din hoton ciki, idan ma cikin ne, to ta hanyar hoton za a tabbatar, sannan a tantance shin a cikin mahaifa ya ke, yadda akeso ko wajen mahaifa wato [ectopic pregnancy].

A watannin da ciki ya fara tsufa kuma wato yakai kamar wata uku (3). Akan ga alamu kamar haka:

  • Girman ciki ya fara bayyana.
  • Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari.
  • A wasu lokutan akan samu ciwon baya.
  • Ciwon ƙirji wato zafin ƙahon zuci ko kwarnafi saboda ‘acid’ ɗin ciki na tasowa saman ƙirji.
  • Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki (stretch marks) da buɗewar hanci a wasu da kuma jin nauyi ko ciwon nonuwa.


Ba dole ba ne kowace mace ta samu dukkan waɗannan alamun, amma fiye da rabin mata suna samun aƙalla rabin waɗannan alamun.

Allah ka sauki dukkan masu ciki lafiya. Amin

Danna koren rubutun nan domin karanta yadda ake amfani da na’urar gwajin ciki ko Yadda zaki kare kanki daga Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

labarin da ya wuceCiwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))
Labarin na GabaAmfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)