Yadda Za A Gane Matsalolin Aljanu Tare Da Magance Su

0
58
Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har ya zuwa ranar tashin alkiyama.
Bayan haka, wannan saƙo ne na musamman zuwa ga ‘yan uwa musulmai maza da mata dangane da matsalolin da suka shafi matan aure da ‘yan mata musulmai da samari marasa aure da magidanta baki ɗaya, dangane da matsalar shafar Aljanu, da yadda suke shiga jikin mutum, da alamomin da ɗan Adam zai gane cewa akwai Aljani a jikinsa, sannan da bayani game da matsalar da ake kira (jinnul ashik) namijin dare ko (jinnu ashika) macen dare.
SU WANE ALJANU, KUMA DAGA INA ALLAH YA HALICCE SU?.
Aljanu halittu ne da Allah (S.W.A) ya halicce su, ya ajiye su a duniya don su bauta masa. Sannan ya halicce su ne daga harshen wuta, Allah (SWA) yana cewa : “KUMA YA HALICCI ALJANI DAGA WUTA (Harsashen Wuta)”. Dan Abbas ya ce lallai aljanu an halicce su daga harshen wuta. Don haka sai mu ce, aljanu wasu halittu ne da Allah ya halicce su daga harshen wuta, shi ya sa ba a iya ganin su, kuma ba a iya taɓa su, ko jin motsinsu, saboda su ruhi ne kawai, ba su da tabbataccen gangar jiki, irin na ɗan Adam. shi ya sa suke shiga surar irin jikin da suka ga dama, kamar Kare, Maciji, Kyanwa (Mage), da sauransu. NAU’IN HALITTUN ALJANU. Allah (SWA) ya halicci Aljanu da nau’in halitti mabambanta.
An samo Hadisi daga Aba Sa’alabatal Kushaniy (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce: “ALJANU NAU’I UKU NE (Wasu) NAU’IN MASU FIKAFIKAI NE, SUNA TASHI SAMA, DA NAU’IN MASU ZAMA MACIZAI DA KUNAMAI DA MASU ZAMA WURI ƊAYA SU KAURA” (Hakim ya fidda shi). WURAREN DA ALJANU SUKE ZAMA Sun kasance suna zama a cikin waɗannan wuraren kamar haka:
1. Cikin Daji. 2. Cikin Ruwa. 3. Tsaunuka, da Koguna. 4. . Bayan Daki 5. Bola (Juji).
6. Wajen Wanke – Wanke. 7. Wurin Maƙabarta. Masu zama a cikin jama’a sun fi cutar da jama’a, saboda suna zama a wuraren ƙazanta, shi ya sa mafi yawan cutarwar da Aljannu ke yi wa ɗan Adam su ne ke yi! (Allah ya tsare mu).
DALILIN DA YASA ALJANU KE SHAFAR ƊAN ADAM.
Yawancin Aljanu suna shafar ɗan Adam ne ta ɗaya daga cikin waɗannan dalilai guda 4:-
1. Saboda zalunci da muguntar Aljanin.
2. Da sunan ƙauna ko son da Aljani ke yi wa ɗan Adam, kamar Aljani ya so mace mutum, ko Aljana ta so namiji mutum. A gaba za mu yi bayani a kan wannan matsalar, kuma shi ake kira da Jinnul Ashik (Namijin Dare) ko Jinnul Ashika (Macen Dare) insha Allahu.
3. Saboda cutarwar da ɗan Adam ya yi wa Aljanun, kamar ya zuba masa ruwan zafi ko ya taka shi, sai ya zo ɗaukar fansa.
4. Ko Bokaye da matsafa su turo wa mutum Aljanin. CUTARWAR DA ALJANI KE YI WA ƊAN ADAM. Aljanu na cutar da ɗan Adam ta hanyoyi guda 2, kamar haka:
1. Ta hanyar shiga jikin ɗan Adam:Shi ne aljani ya shiga jikin ɗan Adam gaba ɗaya ko wata gaɓa, kamar hannu, ƙafa, Baya, ƙirji, Kai, Ido ko Kunne, sai ya yi ta cutar da marar lafiya yana wahalar da shi. Wannan ya tabbata a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya ce: “LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN ƊAN ADAM KAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA”. Ma’ana: Yana iya shiga duk inda jini zai shiga, saboda ba shi da gangar jiki da zai hana shi hakan.
2. Ta hanyar Shafar jikin ɗan Adam:- Shi ne ya sanya ciwo ko kuma ya lalata wata gaɓa daga cikin gaɓoɓin ɗan Adam, kamar ya lalata ko shanye hannu, ya sanya ciwo ko ya kurumtar da kunne, ko ya rike muryar mutum ko ya sanya wa mace ciwo a mara ko mahaifa, ko ya taɓa mata wata jijiya sai jini ya yi ta zuba, da sauransu. Irin waɗannan Aljanun ba a samun sa a jikin marar lafiya, sai dai a yi ta amfani da magani wadda musulunci ya yi umurnin amfani da shi, ta kuma hanyar mai kyau.
LOKUTAN DA ALJANI KE SHIGA JIKIN ƊAN ADAM.
1. Yayin da mutum yake cikin matsanancin bacin rai da fushi.
2. Yayin da mutum ya tsorata
3.Yayin da Mutum ya nitse cikin saɓon Allah, kamar kallace-kallacen fina-finan banza, na batsa.
4. Yayin da mutum ya je cikin janaba, saboda babu garkuwa na tsarki a jikinsa.
ALAMOMIN SAMUWAR ALJANI A JIKIN ƊAN ADAM.
a. Yawan mantuwa mai tsanani.
b. Mutuwar wani ɓangare na jiki, hannu ko kafa wanda baya jin magani.
c. Yawan samun damuwa da ƙuncin rai.
d. Rashin nitsuwa a guri ɗaya.
e. Yawan kokwanto.
f. Firgita a cikin barci.
g. Yawan mafarkin matattu.
h. Yawan mafarkin jini ko ruwa.
i. Mafarkin maciji.
j.Jin motsi kamar ana bin ka a baya.
k. Cizon haƙori a cikin barci.
l. Yawan rashin barci.
m. Yawan farkawa daga barci.
n. Mafarkin Shanu.
o. Mafarkin saduwa ba bisa ƙa’ida ba, kamar sau 3 fiye da haka a sati.
p. Yawan zubar jinin haila wanda ya wuce misali.
q. Yawan zancen zuci.
r. Rashin amincewa da mutane.
s. Yawan faɗuwar gaba.
t. Tafiya ko tsayuwa a cikin barci.
u. Yawan mafarkin abubuwan ban tsoro.
v. Yawan yawace-yawace ba bisa ƙa’ida ba.
w. Yawan jin tsoro haka kurum.
x. Yawan jituwa tsakanin miji da mata.
y. Jin sauti kamar ana kiran ka.
z. Daɗewa a banɗaki ba tare da wani dalili ba.
aa. Zancen zuci a banɗaki. bb. Mafarkin kyanwa (mage). Da sauransu. Da zaran ɗan Adam ya ji wannan alamomin a jikinsa, to akwai alamar samuwar aljani a tattare da shi, sai ya fara addu’a da yawan azkar, da yawaita karatun Alku’ani. Idan kuma ya fara jin ciwon kai, ciwon ƙirji, ciwon baya, ko ciwon gabobi, bayan wadancan alamomi da suke sama, sai ya ci gaba da addu’a tare da shan magani, in kuma abun ya yi tsanani, sai ya nemi Malamim Ruqiyya (Ahlus Sunnah), su yi masa, karatun Alkurani. Allah ya tsare mu.
ABIN DA AKE KIRA JINNUL ASHIK:-
Shi ne mace ta wayi gari tana yawan mafarki wani na saduwa da ita cikin barci, wannan al’amarin ya kasance ya yi yawa a tsakanin mata, kuma har ya kai ga wasu cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji.
DALILIN SAMUWAR JINNUL ASHIK:-

Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur’ani da Sunnah, kamar cikin Majmu’ul fatawa na Shasaboda rashin kyautata sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda musulunci ya hana.

2: Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke, kamar zuwa wajen bokaye.  Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta haɗa nema da wani marar tsoron Allah.

4: Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah, amma Allah zai jarrabe ta da wannan shaiɗani. A takaice dai waɗannan hanyoyin da shi wannan shaiɗani zai zo wajenta, sai ya mayar da abin ya koma zuwa soyayya ya raba ta da kowa, ya hana ta yin aure ko ya raba ta da mijinta ko ya hana ta zaman lafiya da shi, shi kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da ita, ya ɗauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta komai da ita, ya sa gaba da ƙiyayya a tsakani. Allah ya kiyaye. Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa’u Bil Kur’an Minal Jinnu Wash Ahayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul Kur’an Li’ilaj as-hir wal Massi as- shaidani suka ce: Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace ta hanyoyi huɗu kamar haka:

1: Wata shi yake kawo kansa

HANYOYIN DA YAKE BI YA ZO MATA A MATSAYIN MIJIN DARE. SU NE KAMAR HAKA:

1. Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wanda take jin kunya ko wadda ba ta sani ba, ko ɗan uwanta ko ta siffar mace ‘yar uwarta.

2. Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a zahiri, ba a mafarki ba, amma kuma shaiɗani ne ba mijinta ba ne.

3. Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu ba.

4. Wata macen takan kwanta ta yi barci ba, wadda ya sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari, sai ta ga kamar wani ya sadu da ita.

ALAMOMIN MIJIN DARE:

Daga cikin alamomin da mace za ta gane tana da wannan matsalar shi ne: Shi wannan shaiɗanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su ɗauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka ba ne. Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da waɗannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta wadannan matsalolin za tace maka tana fama da su. Daga ciki akwai

1. Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambaye ta laifin mijin ba za ta faɗi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘yan’yanta.

2. Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma ba ya jin magani.

3. Tsananin ciwon ƙirji da ciwon baya.

4. Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauƙi da maras yauƙi ko mai kauri kamar koko tare da yawan ƙaiƙayi ko fitowar ƙuraje.

5. Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta ɗauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarki ta haihu.

6. Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma ba ta samun biyan buƙata.

7. Daf da magariba ta dinga jin zazzaɓi ko faɗuwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da ɓacin rai.

8. Idan ta ɗauki Alku’ani za ta karanta, sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci, da zarar ta ajiye Kur’anin sai ta ji ta wartsake kamar ba ita take jin barci ba.

9. Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci, sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.

10.  Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kaɗewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko ya yi ja.

11. Yawan ƙaiƙayin ido da ƙaiƙayin kai na amosani, amma ba amosa ni ba ne.

12.  Yawan ƙaiƙayin kunne da yawan ƙaiƙayin hanci kamar mura, amma ba mura ba ce, ko yawan kumburin ciki.

13. Yawan zubar jini da ba na al’ada ba, ko jini ya rika yi mata wasa. Sannan kuma har ma wacce ba ta da aure budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin dake tsakani da ita wacce take da aure shi ne kamar haka:-

1. Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajenta da maganar aure kamar za a yi, sai abin ya lalace daga wajenta ko daga wajensa.

Yadda Ake Wa Mai Gida A Lokacin Al’ada

DOMIN KARIN BAYANI AKAN MAGUNGUNA DANNA WANNAN LINK DIN

labarin da ya wuceAmfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.