Tag: ilimin lafiya

  • Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa; zaɓar abubuwan da za su taimaka wa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kin san yanayin fatarki, sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum.

    Ga misalan yadda za ki kula da fatarki:

    1. Goge Kwalliya Kafin Bacci

    Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani, to yana da kyau ki samu abin da za ki goge ta tas, kafin ki kwanta barci. Koda wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa, amma idanuwa da laɓɓa suna buƙatar kula ta musamman, saboda haka; sai ki samu abin goge kwalliya (wiper) jiƙaƙƙiya, ki sake gogewa a hankali.

    2. Wanke Fuska

    Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya, sai kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi, ba mai zafi ba; sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska, sannan a sake ɗaurayewa.

    3. Amfani Da Toner

    Bayan an wanke fuska, ana so a shafa toner. A samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan, sai ana shafawa a hankali ban da gurin ido sannan ba a wankewa.

    4. Amfani Da Moisturizer

    Bayan toner ta bushe a kan fuskarki, yana da kyau a yi amfani da moisturizer a kan fuska, hadda tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido, sai ki samu wani mai na musamman.

    5. Yin Murza (Scrubbing)

    Ana iyayin murza ta, musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati, za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa, sai kina dangwala da hannunki, kina murzawa a hankali a kan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

    6. Yin Amfani Da (Sunscreen)

    Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska, ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana, ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau danna nan

  • Ciwon Hanta (Hepatitis B)

    Ciwon Hanta (Hepatitis B)

    Hanta, ɗaya ce daga cikin sassan jikin ɗan adam. Kuma jigo ce wajen kula da tafiyar da jikin ɗan adam. Mutum ba zai iya rayuwa babu hanta ba. Abubuwa da dama suna iya janyo ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.

    Akwai ciwon hanta mai tsanani da mara tsanani. Akwai mai dogon zango da mai gajeran zango. Kuma kowanne daga cikin nau’o’in ciwon hanta zai iya kashe mutum.

    Amfanin Hanta

    Amfanin hanta yana da yawa a jiki, amma ga kaɗan daga cikin su:

    1. Sarrafa abinci: Hanta tana kula da daidaituwar abinci a jiki. Misali, idan mutum ya ci shinkafa mai yawa, hanta ce take sarrafa abincin domin a ajiye shi zuwa wani lokaci.

    2. Sarrafa magunguna: Hanta tana taka rawar gaske wajen kula da shige da ficen magungunan a jikin ɗan adam.

    3. Samar da sinadarai: Hanta tana samar da sinadaran da jiki yake buƙata wajen yaƙar cututtuka da kuma samar da zaman lafiyar jiki. Sinadaran sun haɗa da: bile, plasma proteins, clotting factors da sauransu.

    4. Fitar da datti; Cututtuka da sinadarai marasa amfani daga jiki kamar su ammonia, billurubin da sauran su.

    Abubuwan da suke janyo ciwon hanta

    1. Ƙwayar cutar Virus: Kamar Hepatitis (A, B, C, D da E) virus, cytomegalovirus (CMV), Epstein-Barr virus da sauransu.

    2. Shan giya: Giya tana janyo cututtuka iri daban daban a jikin ɗan adam, daga ciki har da ciwon hanta.

    3. Shan magunguna barkatai: Wasu daga cikin magungunan da muke amfani da su, suna iya janyo ciwon hanta musamman idan ana shan su ba bisa ƙa’ida ba.

    Abubuwan da suke janyo ciwon hanta suna da yawa. Amma zan yi bayani a kan ciwon hanta wanda ƙwayar virus ta Hepatitis B take janyowa.

    Ciwon hanta na Virus ɗin Hepatitis B:

    Mutane da dama a Nigeria suna ɗauke da wannan ƙwayar cutar. Wasu sun san suna da ita, da yawa ba su san suna da ita ba. Virus ɗin Hepatitis B tana iya lalata wa mutum hanta, tana janyo ciwon hanta mai tsanani kuma tana iya janyo cutar dajin hanta (cancer).

    Yadda ake ɗaukar ƙwayar cutar Hepatitis B Virus

    Virus ɗin Hepatitis B tana shiga jikin mutum ne ta hanyar cakuɗuwar jinin mai ɗauke da virus din da jinin wanda ba shi da cutar. Misali:

    1. Yankewa: Idan wanda yake ɗauke da ƙwayar cutar Hepatitis ya yanke da abu mai kaifi (kamar reza, wuƙa, aska, almakashi da sauransu), to duk wanda ya yi amfani da wannan abu mai kaifin, kuma shi ma ya yanke, to virus ɗin za ta iya shiga jikinsa.

    2. Ƙarin jini: Idan aka ƙara wa mutum jini mai Hepatitis, to zai iya ɗaukar virus ɗin.

    3. Jima’i: Wanda yake da Hepatitis B Virus zai iya shafawa wanda ba shi da ita a lokacin jima’i.

    Yadda ake samun kariya daga cutar Hepatitis B virus

    1. Rigakafi: Akwai allura da ake yi domin samun kariya daga kamuwa da cutar Hepatitis B virus. Ana yin allurar ne sau uku, a tsawon wata shida. Idan aka yi wa mutum rigakafin, zai samu kariya mai yawan gaske.

    2. Kaucewa amfani da abu mai kaifi: A yi ƙoƙari wajen kaucewa amfani da duk wani abun da zai iya yankar mutum. idan kuma lallai sai anyi amfani da abu mai kaifi kamar lokacin yanke farce ko aski da sauransu, to kowa ya yi amfani da nasa shi kaɗai. A daina yi wa mutane aski ko yankan farce da abu guda ɗaya.

    3. Gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus: Yana da kyau mutum ya je a yi masa gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus domin ya san ko yana da ita ko ba shi da ita. Idan ba shi da ita, sai ya je a yi masa allurar rigakafi. Idan kuma yana da ita, sai ya yi ƙoƙari wajen kaucewa yaɗa ta.

    4. Kaucewa taɓa jinin mutum: Taɓa jinin wanda yake ɗauke da virus ɗin Hepatitis B ba tare da safar hannu ba, za iya janyowa a ɗauki cutar musamman idan akwai ciwo (komai ƙanƙantar sa) a hannun.

    5. Tantance jini kafin ƙara wa mutum: Masu aiki a ɗakin gwaje-gwaje da ɗaukar jini, su tabbata sun yi gwajin Virus ɗin Hepatitis B da ma wasu cututtukan kafin su ɗauki jinin mutum.

    Alamomin ciwon hanta na Hepatitis B virus

    Idan virus ɗin Hepatitis B ta shiga jikin mutum, ba lallai ya ji wata alama ba, kuma ba lallai ya san ya ɗauki cutar ba. Amma wani lokacin, cutar hanta tana iya nuna waɗannan alamomi idan ta shiga jikin mutum;

    • Zazzaɓi
    • Kasala
    • Ciwon ciki
    • Canjawar ido zuwa launin rawaya (yellow) ko kore
    • Ciwon jiki da sauransu
    Bayan waɗannan alamomin na ɗan wani lokaci, virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum ba tare da ta janyo masa wani abu ba.

    Rayuwar Hepatitis B Virus a jikin ɗan adam

    Idan cutar Hepatitis B virus ta shiga jikin mutum, ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan za su faru:

    1. Ƙwayar virus ɗin za ta iya janyo wa mutum ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.
    2. Ƙwayar virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum na tsawon lokaci ba tare da ta janyo masa ciwon hanta mai tsanani ba, amma zai iya yaɗa cutar.
    3. Ƙwayar virus ɗin za ta iya mutuwa da kanta ba tare da an sha mata wani magani ba.

    Alamomin ciwon hanta mai tsanani sun haɗa da:

    • Kumburin jiki, musamman ciki da ƙafa
    • Aman jini
    • Yin kashi baƙiƙƙirin kamar kwalta
    • Ramewa
    • Fita daga hayyaci

    Maganin Hepatitis B virus

    A likitance, babu magani guda ɗaya wanda yake kashe virus ɗin. Amma akwai wasu magunguna da ake ba wa mai cutar domin rage ƙarfin tasirin ta a jikinsa. Ba a bayar da maganin sai mai cutar ya cika wasu ƙa’idoji da sharuɗa.

    Idan mutum bai cika waɗannan ƙa’idoji da sharuɗa ba, to ba za a rubuta masa maganin ba. Zai ci gaba da gudanar da rayuwar sa kamar yadda ya saba. Sai dai kawai zai dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci domin kula da ci gaban cutar.

    Shawarwari ga masu ciwon Hepatitis B virus

    • Za ka iya ci gaba da gudanar da rayuwarka cikin ƙoshin lafiya duk da cewa kana da Hepatitis B virus. Amma akwai buƙatar a dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci.

    • A Kaucewa yaɗa cutar ta hanyar daina yin amfani da abubuwa masu kaifi na kowa da kowa kamar su almakashi da reza da abin yankan farce da sauransu.

    Wasu abubuwa da ake alaƙanta su da ciwon hanta

    1. Shan rake: Shan rake ba ya maganin ciwon hanta ko wane iri ne.

    2. Sinadarin abinci mai gina jiki (Protein): Mai cutar Hepatitis B virus, zai ci abinci kamar yadda kowa yake ci. Babu abin da zai hana shi cin abinci mai gina jiki kamar su nama, kifi, ƙwai, gyaɗa, wake da sauransu.

    Idan mutum yana da ciwon hantar da ya janyo masa rashin lafiya mai tsanani, ana buƙatar ya rage cin abinci mai gina jiki (protein) ya kuma yawaita cin abinci mai sa kuzari kamar su tuwo, shinkafa, doya da sauransu (Carbohydrate).

    A kula sosai, ban ce a daina cin mai gina jiki ba, cewa na yi ya rage. Kuma ba a ce ya dinga shan rake ba, cewa aka yi abinci mai saka kuzari.

    Wannan bayani an samo shi ne daga Hamisu Adam Abubakar.

    Domin karanta Ciwon Suga (Diabetes) danna nan.

  • Amfanin Ƙaho

    Amfanin Ƙaho

    Taƙaitaccen Tarihin Ƙaho:

    Ƙaho, abu ne mai asali da tarihi a Musulunci, domin kuwa, tun kafin yin hijira daga Makka zuwa Madina da kamar shekara guda a lokacin da aka yi Isra’I da Mi’iraji da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Mala’iku masu yawa sun nusar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da yin amfani da ƙaho da kuma bashi muhimmancin gaske. Don haka, Manzo (SallallahuAlaihi Wasallam) ya yi ƙaho; kuma ya biya wanda ya yi masa ƙahon lada.

    Matsayin Ƙaho:

    Ƙaho abu ne da yake da babban matsayi da gagarumar falala, wanda har hakan ya sa Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ƙaho ne mafi alherin abin da mutane suke yin magani da shi”.

    Ranakun da Ake Yin Ƙaho a Cikin Wata:

    Ga mai son ya ci cikakkiyar gajiyar yi ƙaho, to, ya yi shi a ranar sha bakwai (17) ko sha tara (19), ko kuma ranar ashirin da ɗaya (21) ga watan shekarar Hijira. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “wanda ya yi ƙaho a ɗaya dagacikin waɗannann ranakun; da izinin Allah ƙahon zai zamar maganin duk wata cuta”.

    Ranakun da Ake Yin Ƙaho Cikin Sati:

    Ga mai son ya yi ƙaho a ranakun da suka dace daga cikin ranakun sati, to ya yi a ɗaya daga cikin waɗannan ranaku uku masu zuwa: Ranar Litinin, Talata da Alhamis.

    Ranakun da ba a Yin Ƙaho a Cikinsu a Sati:

    An karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda da su, ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku nisanci yin ƙaho a ranar Laraba, da Juma’a, da Asabar da kuma ranar Lahadi…”.

    Fiyayyen Lokacin da Ake Yin Ƙaho a Cikinsa:

    Yin ƙaho da safe kafin Karin kumallo shi ne fiyayyen lokacin da ake yin ƙaho a cikinsa.
    Guraren da Ake Yin Ƙaho
    Ana yin ƙaho a sassa daban-daban na iki, kamar yadda aka rawaito cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ƙaho a ƙafa da kafaɗu da gyaffan wuya ko mahaɗar wuya da baya, kuma ya yi ƙaho a ka.
    Kuma ana iya gudnar da ƙaho a wasu guraren daban daga waɗanda aka ambata a sama, gwargwadon buƙata.

    Amfanin ƙaho:

     Ƙara hankali.
     Ƙara kaifin hadda.
     Maganin cututtukan jiki.
     Rage yawaitar jinni don daidaita gudanarsa
     Rage maiƙon cikin jinni
     Maganta matsanancin ciwon kai.
     Rage yawan majinar jiki.
     Kara wa sinadaran yaƙar cututtukan jiki ƙarfi
     Raba jiki da guba

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Jiga-jigan Magunguna

    Jiga-jigan Magunguna

    Ga abin da Allah (Subhanahu wata’ala) Ya ce game da mafificin littafinsa Alƙur’ani mai tsarki.“Kuma muna saukar da abin da yake waraka da jinƙai a wannan Alƙur’ani ga muminai kuma ba ya ƙarar azzalumai (wato kafirai) da komai sai taɓewa”.

    Kuma Allah Ya ce da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam):“…. ka ce shi (Alƙur’ani) shiriya ce da waraka ga waɗanda suka yi Imani”.

    A sakamako wannan bayani na Allah (Subhanahu wata’ala) Alƙur’ani waraka ce game da matsalolin zukata kuma magani ne game da cututtukan jiki.

    Kuma shi ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa duk dare.
    Kamar yadda Hadisi ya inganta cewa ɗaya daga cikin sahabbai ya yi wa wani mutum da kunama ta harba ruƙuya da fatiha ya warke nan take.

    Kuma an karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Waraka na tare da abubuwa Uku:

    1. Jinin da aka jawo da ƙaho
    2. Maƙwararar zuma
    3. Lalas (sakiya) da wuta. Sai dai ni ina hana al’ummata yin lalas.”
    Bukhari ne ya rawaito shi.

    Sannan kuma ƙwayoyin baƙin algaru (habbatus-sauda) suna bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawar da cututukan sanyi, kamar yadda bayani ya gabata.
    Nonon raƙumi da fitsarinsa magani ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya yi umarni da a sha su don samun waraka daga cuta. Kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

    Bayan haka, addu’a ma na maganta matsaloli da cututtukan da suka addabi bayi, kamar yadda bayani ya gabata cewa, Annabi Ayyub (Alaihis-Salam), ya roƙi Allah warakar ciwon da ya same shi, Allah ya amsa masa Ya yaye masa ciwon.
    Haka kuma sadaka na maganta cututtuka; ta kuma tafiyar da zunuban bawa kamar yadda ruwa yake kasha wuta. kamar yadda hadisai tabbatattu suka tabbatar.

    Amfani da ruwan Zam-Zam yana maganin cutar da aka sha shi dominta, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Ba Duka Wanda Ke Da Ciwon Dake Warkewa Ba Ne Yake Warkewa

    Ba Duka Wanda Ke Da Ciwon Dake Warkewa Ba Ne Yake Warkewa

    An karɓo Hadisi daga Aɗa’u ɗan Abi Rabah ya ce Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce: “Da ni bana nuna maka wata mace daga cikin ‘yan Aljanna ba? Sai na ce: Eh, nuna min, ya ce: Wannan baƙar matar ta zo wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: Ana kifar da ni in faɗi, kuma ina yin tsiraici ka roƙar min Allah Maɗaukaki.

    Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “In kin so ki yi haƙuri ki dace da samun Aljanna, in kuma kin so ina roƙa miki Allah Madauƙaki ya ba ki lafiya.” Sai ta ce, zan yi haƙuri (don na sami Aljannar). sai ta ce: Amma fa ina yin tsiraici ka roƙar min Allah (ko an kifar da ni) kar in yi tsiraici, sai ya yi mata addu’a”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

    Bayan haka, cutar da ta zama ta tun asalin halittar bawa, ba ta magantuwa, kamar wanda aka halitta babu yatsu, ko rangwamen hankali ko rasa wani sashi na jiki.
    Gaɓar da wata cuta ta lalata jijiyoyin da suke kai saƙo gare ta, kamar ido ko kunne a dalilin ƙyanda ko sanƙarau.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan

  • Gano Ciwo Shi Ne Makamar Sanin Maganinsa

    Gano Ciwo Shi Ne Makamar Sanin Maganinsa

    Haƙiƙa sanin cutar da take tare da mara lafiya da kuma tantance ta daga wata  cutar, ita ce ƙwaƙƙwarar makamar shawo kan cuta da gano sahihin maganinta.
    Don haka farkon abin da ya kamaci mai bayar da magani shi ne, ya yi ƙoƙarin gano cutar da take tare da mara lafiyar da zai ba wani magani, sannan kuma sai ya bayar da maganin da ya dace da ita cutar da ya gano. Ga Misali: Maganin mai ciwon jahilci shi ne,ilmantarwa, maganin mai jin yunwa, ya ci abinci, maganin mai jin ƙishiriwa, ya sha ruwa, maganin wanda ya gaji kuma, shi ne ya huta, da dai sauransu.

    Kashe Kashen Cuta.
    Cututtuka dake samun bayi sun kasu kamar haka:
    1. Cututtukan da suka shafi zuciya da tunani
    2. Cututtukan da suka shafi sassan jiki da ɓangarorinsa.
    3. Cututtukan shafar aljanu da wasunsu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Nau’ikan Abinci 5 Da Ya Kamata A Kauracewa Kafin Kwanciya Bacci

    Nau’ikan Abinci 5 Da Ya Kamata A Kauracewa Kafin Kwanciya Bacci

    1. Naman kaza: Naman kaza da sauran danginsa suna hana barci mai dadi, matukar aka ci kafin barci. Wannan na faruwa ne, saboda narkewar abinci a jikin dan Adam na ɗaukar lokaci ya yin barci. A maimakon ɗan Adam ya yi barci mai daɗi, jikinsa zai maida hankali ne wajen narkar da abincin.
    2. Kayan kwalam masu sukari: Wannan a bayyane yake, duk da mutane da yawa na cin irin wadannan abincin kafin su kwanta. Wannan ba abin da ya dace ba ne, don kuwa suna ɗaukar lokaci kafin su narke a jiki. A maimakon jikin mutum ya samu sauki da hutu yayin kwanciyar barcin, sai ya yi ta kokarin narkar da abincin wanda hakan zai hana barci mai nagarta.
    3. Shayin Coffee: Duk da kuwa abin sha ne, yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata a guda kafin a kwanta. Wannan kuwa za a iya danganta shi ne da sinadarin ‘caffeine’ da ke ciki wanda ke hana barci.
    Amma kuma, idan mutum na da burin kin barci, toh zai iya shan coffee don wannan aikin. Abin kiyayewa a nan kawai shi ne, kada ya zama mutum ya saba, don akwai matsalolin da ke akwai dangane da sabo da shan sinadarin caffeine.
    1. Abinci mai yaji: Duk yadda mutum ke son abinci mai yaji, zai fi idan aka ci da safe ko da rana amma a kiyaye da dare. Abinci mai yaji kan jawo tashin zuciya, idan aka ci da dare kuma hakan yakan hana nagartaccen barci.
    2. Abinci mai maiƙo: A shawarce abinci mai maiko abin gudu ne da daddare ,don samun lafiya mai inganci. Maiƙon dake ƙunshe a abincin nasa ciki ya fitar da ‘acid’ wanda yake kawo tashin zuciya. A don haka ne idan ana bukatar barci mai nagarta tare da gudun tashin zuciya da safe, sai a guji abinci mai maiko da dare.
    Domin sanin menene nutrion dannan nan
  • Ta Yaya Zan Gina Ƙwaƙwalwar Jaririna Tun Yana Ciki?

    Ta Yaya Zan Gina Ƙwaƙwalwar Jaririna Tun Yana Ciki?

    Za ki iya gina ƙwaƙwalwar jaririnki yana ciki ta hanyar amfani da Folic Acid/Folate.

    Folic acid na ɗaya daga cikin nau’ikan Vitamin B ne (Vitamin B complex), ana samun shi a cikin bushasshen wake, peas, lemon zaƙi, hanta, ganyen salad da dai sauransu.

    Folic acid na taimakawa wajen tattali da kuma ƙyanƙyasar cells, da kuma hana canjin (DNA) wanda yake kaiwa ga cancer. Wannan Folic acid ko kuma folate yana gina ƙwaƙwalwar yaronki a ciki, ƙashin kansa (wanda ya zagaye ƙwaƙwalwar), da kuma lakarsa, domin su hana ginuwar matsaloli kamar neural tube defect; spina bifida.

    Wannan cuta na samar da tawaya a ƙwaƙwalwa da kuma laka, wanda yana faruwa a watan farko na ciki kafin ma mace ta san tana da juna biyu. Misalin hydrocephalus (taruwar ruwa a cikin ƙwaƙwalwa).

    Bugu da ƙari, ba ga jaririnki kaɗai ba, harda kanki ma, rashin folic acid kan haifar da yawan ɓarewar ciki, haifar bakwaini da sauransu.

    Daga ƙarshe nake ba da shawara ga duk wadda take son gina ƙwaƙwalwar jaririnta, da ta ci abubuwan da suke ɗauke da folic acid a ƙalla 400mcg wanda na ambata su a baya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Tarbiyar Yaro danna nan

  • Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE)

    Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE)

    Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum yaji ciwo, ko kuma ya yanke jikinsa, yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su ‘plasma‛, ‘Red Blood Cells (RBC)’, ‘White Blood Cells (WBCs)‛, ‘Platelets‛ da sauransu.

    Cutar sickler tana faruwa ne idan aka samu matsala a RBC.

    RBC yana ɗauke da sinadarin ‘Haemoglobin (Hb)’ a cikinsa. Haemoglobin (Hb) kala–kala ne; akwai Haemoglobin A (HbA), Haemoglobin B (HbB), Haemoglobin C (Hbc), da sauransu. HbA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran Hb ɗin ba lafiyayyu ba ne.

    Cutar sickler tana ɗaya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.

    Ma’anar cutar sikila

    Cutar sickler tana nufin mutum yana ɗauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurɓatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi

    Yadda ake samun cutar sikila

    Ana samun cutar sickler ne daga wurin iyaye (uwa da uba). Uba shi kaɗai ba zai iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler ba, haka ma uwa ita kaɗai ba za ta iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler ba. Dole sai da gudunmawar kowanne daga cikinsu (uwa da uba).

    Kowane mutum yana da sinadaren haemoglobin a jikinsa nau’i biyu. Zan yi magana a kan haemoglobin A da kuma haemoglobin S kawai saboda su ne suka fi yawa. kowane mutum yana da ɗaya daga cikin waɗannan Haemoglobin ɗin:

    (1) Haemoglobin AA (HbAA)

    (2) Haemoglobin AS (HbAS)

    (3) Haemoglobin SS (AbSS)

    • Wanda HbAA yana da lafiyayyun haemoglobin guda biyu.
    • Mai HbAS yana da lafiyayyen Haemoglobin guda ɗaya da kuma wanda ba lafiyayye ba (ba mai kyan ba) guda ɗaya
    • Mai HbSS yana da haemoglobin guda biyu marasa kyau.
    • Mai HbAA lafiya ƙalau yake. Ma’ana ba shi da ciwon sickler.
    • Mai HbAS shima lafiya ƙalau yake, ba shi da ciwon sickler, amma zai iya haifar ɗa/’ƴa mai sickler idan ya auri mai HbAS. Don haka, HbAS shi ake kira da ‚carrier‛
    • Mai HbSS, shi ne yake da ciwon sickler

    Lokacin da za a halicci mutum a cikin mahaifiyarsa, uwa tana ba da gudunmawar haemoglobin guda ɗaya, sannan uba ma yana bada gudunmawar haemoglobin guda ɗaya.

    Idan uba ya bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS) sannan uwa ma ta bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS), to tabbas ɗan da za’a haifa, zai kasance sickler ne (HbSS).

    Ga dai yadda za ta kasance idan aka yi aure.

    Iyaye (Uwa da Uba)

    Yanayin ‘Ya’Ya

    AA da AA AA a kowane Lokaci
    AA da AS AA, ko Kuma AS
    AS da AS AA ko AS ko SS
    AS da SS AS ko kuma SS
    SS da SS SS a kowane lokaci
    AA da SS AS a kowane lokaci
    Don haka, idan ana so a kauce wa cutar sikila, to kada a yi aure tsakanin.

    ‘AS’ da ‘AS’,

    ‘AS’ da ‘SS’,

    ‘SS’ da ‘SS’.

    Alamomin cutar sikila

    Suna bayyana ne tun yaro yana ƙarami a mafi yawancin lokaci. Alamomin sun haɗa da

    • Kumburin ƴan yatsu
    • Ciwon ƙashi mai tsanani
    • Ɗashewar jiki (ƙarancin jini)
    • Ƙanƙantar jiki
    • Da sauransu
    Illolin ciwon sikila

    Ciwon sickler yana haifar da illoli daban–daban, kamar:

    • Yawan rashin lafiya akai–akai kamar ciwon ƙashi, ƙirji, ciki da sauransu
    • Shanyewar ɓarin jiki (stroke)
    • Ciwon ƙoda
    • Rashin zuwa makaranta ko kuma yawan tangarɗar karatu
    • Yawan ƙarancin  jini
    • Shaye–shaye
    • Saurin mutuwa (mutuwa lokacin ƙuruciya da sauransu).
    Maganin ciwon sikila

    Babban maganin ciwon sickler shi ne kada a yi aure idan akwai yiwuwar a haifi ɗa mai sikila. Kuma ana iya gane haka ta hanyar yin gwajin genotype. Amma idan ciwon ya samu, to hanya ɗaya ce wadda ake iya maganin wannan cuta.

    Ita ce, dashen ɓargo (Bone marrow transplant), shi wannan dashen ɓargo yana tare da irin tasa matsalolin kuma ba kowane lokaci ake yin nasarar warkewa ba. Sannan kuma yana da tsada matuƙa da gaske.

    Ana ba wa masu sickler wasu magunguna domin samun sauƙin rashin lafiya akai-akai. Shi yasa ake so masu sickler su dinga zuwa wajen likita lokaci zuwa lokaci, koda babu abin da suke ji na rashin lafiya.

    Abubuwan da suke tayar da rashin lafiya ga masu ciwon sikila
    • Zafi mai tsanani
    • Zazzaɓi (ko na malaria ko kuma wani abu daban
    • Motsa jiki mai yawa
    • Ɓacin rai. Da sauransu

    Don haka yana da kyau a kaucewa waɗannan abubuwan.

    Kammalawa

    Ciwon sickler yana saka rashin lafiya akai–akai, yana hana jin daɗin rayuwa, sannan kuma yana sanadiyar mutuwar mutum yana ƙarami. Ana iya kaucewa ciwon idan aka bi shawarwarin likitoci ta hanyar yin gwajin genotype.

     

  • Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)

    Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)

    Akwai wani ma’auni da ake amfani da shi wajen kula da ƙarfin gudanar jini a cikin jijiyoyin jini. Wannan ma’auni ana kiransa da ‘Blood Pressure (BP)’.

    Yadda ake so BP ɗin babban mutum ya kasance shi ne:

    90 – 139/60 – 89 MMHg. ma’ana dai:

    (1) Ma’aunin sama ya kasance daga 90 zuwa 139. Kar ya yi ƙasa da 90, kuma ka da ya yi sama da 139.

    (2) Ma’aunin ƙasa ya kasance daga 60 zuwa 89. Kar  ya yi ƙasa da 60, kuma kada ya yi sama da 89.

    Ma’anar Hawan jini

    Hawan jini shi ne, BP ɗin mutum ya fi 139 (ma’aunin sama) ko kuma ya fi 89 (ma’aunin ƙasa)

    Abubuwan da suke janyo hawan jini.

    Hawan jini kala biyu ne:

    (1) Primary hypertension.

    (2) Secondary hypertension.

    Abin da yake janyo primary hypertension.

    Babu abu guda ɗaya, wanda bincike ya nuna cewa yana janyo irin wannan hawan jini. Amma dai akwai wasu abubuwan da suke da alaƙa mai ƙarfi da irin wannan hawan jinin. Waɗannan abubuwan sun haɗa da:

    • Gado: idan ɗaya daga cikin mahaifinka, ko mahaifiyarka ko kuma ɗan uwanka shaƙiƙi yana da hawan jini, to kai ma za ka iya kamuwa da hawan jini.
    • Shan giya: Idan mutum yana shan giya, to zai iya kamuwa
    • Shan taba sigari.
    • Jinsin baƙar fata: idan mutum shi baƙi ne (ɗan Afrika), to zai iya kamuwa da hawan jini.
    • Ciwon suga (diabetes)
    • Ƙiba.
    • Shekaru sama da 40.
    Abin da yake janyo secondary hypertension.
    • Ciwon ƙoda
    • Juna biyu (pregnancy)
    • Ciwon zuciya
    • Shan giya
    • Shan wasu ƙwayoyi kamar ‘Steroids’ da sauransu
    Alamomin hawan jini

    A mafi yawanci lokaci, hawan jini ba ya nuna wasu alamomi sai dai idan ya haifar, ko kuma ya fara haifar da matsala. Wannan dalilin ne ya sa ake kiran hawan jini da ‘Silent Killer’

    Matsaloli ko kuma illoli da hawan jini yake haifarwa
    • Cutar shanyewar ɓarin jiki (stroke)
    • Ciwon zuciya
    • Ciwon ƙoda
    • Matsalolin ido
    • Mutuwar farar ɗaya da sauransu
     Abubuwan Masu Muhimmanci

    A sani cewa, lokacin da jinin mutum ya hau ko kuma yake hawa, ba lallai ne mutum ya ji wata alama ta rashin lafiya ba. Shi yasa ake cewa hawan jini ‘Silent Killer’ ma’ana ‘mai kisa ba tare da an sani ba‛

    Don haka yana da kyau mutum ya dinga zuwa ana duba masa BP ɗinsa lokaci zuwa lokaci

    Maganin hawan jini

    A likitance, babu wani magani guda ɗaya wanda idan mutum ya yi amfani da shi zai warke daga hawan jini, musamman ‘primary hypertension‛.

    Amma idan mutum yana da ‘secondary hypertension‛ to zai iya samun waraka idan aka yi maganin abin da ya janyo masa hawan jinin.

    Magungunan hawan jini, suna daidaita ‘BP‛ ne amma ba sa warkar da hawan jinin. Shi yasa ake shan maganin a kowace rana muddun mutum yana da rai.

    Idan mutum ya daina shan maganin ba tare da shawarar likita ba, to jinin nasa zai iya ci gaba da hawa kuma ya haddasa masa matsalolin da aka lissafa a baya.

    Shawarwari
    • A rage gishiri a abinci: gishiri ya kasance ɗan kaɗan, sannan kuma a daina barbaɗa gishiri a abinci
    • A daina shan taba sigari
    • A daina shan giya
    • A rage amfani da kayan da suke ƙarawa miya zaƙi, sai wanda likita ya bada shawara. A daina shan magunguna barkatai ba tare da shawarar likita ba
    • A yawaita motsa jiki
    • A rage ƙiba ta hanyar motsa jiki da kula da abinci
    • A rika zuwa wurin likita lokaci zuwa lokaci domin duba BP
    Kammalawa

    Mutane masu hawan jini suna da yawa a cikin al’ummarmu, kuma yana janyo illoli da suke da wahalar magani. Idan mutum yana shan magani, kuma yana bin dokokin likita, to zai iya samun sauƙi ko kuma kariya daga Waɗannan matsaloli.