Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

0
483

A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa; zaɓar abubuwan da za su taimaka wa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kin san yanayin fatarki, sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum.

Ga misalan yadda za ki kula da fatarki:

1. Goge Kwalliya Kafin Bacci

Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani, to yana da kyau ki samu abin da za ki goge ta tas, kafin ki kwanta barci. Koda wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa, amma idanuwa da laɓɓa suna buƙatar kula ta musamman, saboda haka; sai ki samu abin goge kwalliya (wiper) jiƙaƙƙiya, ki sake gogewa a hankali.

2. Wanke Fuska

Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya, sai kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi, ba mai zafi ba; sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska, sannan a sake ɗaurayewa.

3. Amfani Da Toner

Bayan an wanke fuska, ana so a shafa toner. A samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan, sai ana shafawa a hankali ban da gurin ido sannan ba a wankewa.

4. Amfani Da Moisturizer

Bayan toner ta bushe a kan fuskarki, yana da kyau a yi amfani da moisturizer a kan fuska, hadda tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido, sai ki samu wani mai na musamman.

5. Yin Murza (Scrubbing)

Ana iyayin murza ta, musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati, za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa, sai kina dangwala da hannunki, kina murzawa a hankali a kan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

6. Yin Amfani Da (Sunscreen)

Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska, ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana, ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau danna nan

labarin da ya wuceWajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah
Labarin na GabaYadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah