Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman

0
6791

Gyaran Gashi na da muhimmanci sosai wajen ƙara wa mace kyau, da cikar darajarta ta mace.

Gashi halitta ce, kyauta daga ubangiji ya ba wasu baƙi, da mai yawa, da mai tsawo, da kyau. Ya ba wasu ja, da kaɗan, da ƙarfi, ko da laushi sannan kuma yardar Allah ne, ya ba mu dama ta iya gyara shi.

Ya zama an samu ci gabansa, Kuma ya zama cikar kyawunki ko da kuwa ba shi da yawa,  Idan kin iya gyara shi wato yana samun kyakkyawar kulawa.

HANYOYIN GYARAN GASHI:

1- Wanke gashi da ruwan sabulun wanki kai.

2- Amfani da man gashi da ya dace da irin yanayin gashinki.

3- Turara gashi (steaming) da haɗe-haɗen gargajiya. Ko kuma da mayukan zamani .

4- Kitso akai-akai, tare da lura da makitsiyar da hannunta ya karɓe ki.

5 – Yi ma gashinki addu’a .

6 – Cin lafiyayyen abinci, kayan marmari .

7 – Idan kina gyaran gashi na konawa (Relaxer). To dole ne yawan zuwa gidan gyaran gashi akai-akai.

YADDA AKE MAI NA GYARAN GASHI :

Man Zaitun
Man kaɗanya

Habbatus sauda
Kanunfari kaɗan
Garin Habbatus sauda
Mai Alayyadi

Za ki daka kaninfari da Habbatus sauda, Sai ki zuba su cikin Roba. Ki ɗauko dukkan mayukanki na Zaitun, Habbatus sauda, Alayyadi, kaɗanya su hade su. Ki yi ta juyawa , har dai su haɗe jikinsu sosai.

Idan kina bin hanyoyin can na gyaran gashi. Za ki ga gashin kanki na tsawo da laushi. danna koren rubutun nan domin karanta yadda ake gyaran jiki ya yi kyau da laushi

labarin da ya wuceYadda Ake Shagwaɓa Mai Gida A Lokacin Hutu
Labarin na GabaYadda Ake Gyaran Kafa Na Musamman (kaushi ko faso)
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.