Jiga-jigan Magunguna

0
488

Ga abin da Allah (Subhanahu wata’ala) Ya ce game da mafificin littafinsa Alƙur’ani mai tsarki.“Kuma muna saukar da abin da yake waraka da jinƙai a wannan Alƙur’ani ga muminai kuma ba ya ƙarar azzalumai (wato kafirai) da komai sai taɓewa”.

Kuma Allah Ya ce da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam):“…. ka ce shi (Alƙur’ani) shiriya ce da waraka ga waɗanda suka yi Imani”.

A sakamako wannan bayani na Allah (Subhanahu wata’ala) Alƙur’ani waraka ce game da matsalolin zukata kuma magani ne game da cututtukan jiki.

Kuma shi ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa duk dare.
Kamar yadda Hadisi ya inganta cewa ɗaya daga cikin sahabbai ya yi wa wani mutum da kunama ta harba ruƙuya da fatiha ya warke nan take.

Kuma an karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Waraka na tare da abubuwa Uku:

1. Jinin da aka jawo da ƙaho
2. Maƙwararar zuma
3. Lalas (sakiya) da wuta. Sai dai ni ina hana al’ummata yin lalas.”
Bukhari ne ya rawaito shi.

Sannan kuma ƙwayoyin baƙin algaru (habbatus-sauda) suna bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawar da cututukan sanyi, kamar yadda bayani ya gabata.
Nonon raƙumi da fitsarinsa magani ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya yi umarni da a sha su don samun waraka daga cuta. Kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

Bayan haka, addu’a ma na maganta matsaloli da cututtukan da suka addabi bayi, kamar yadda bayani ya gabata cewa, Annabi Ayyub (Alaihis-Salam), ya roƙi Allah warakar ciwon da ya same shi, Allah ya amsa masa Ya yaye masa ciwon.
Haka kuma sadaka na maganta cututtuka; ta kuma tafiyar da zunuban bawa kamar yadda ruwa yake kasha wuta. kamar yadda hadisai tabbatattu suka tabbatar.

Amfani da ruwan Zam-Zam yana maganin cutar da aka sha shi dominta, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceDokokin Suturar Musulma
Labarin na GabaHaƙƙoƙin Da Ma’aurata Suke Tarayya A Kansu