Amfanin Ƙaho

0
1086

Taƙaitaccen Tarihin Ƙaho:

Ƙaho, abu ne mai asali da tarihi a Musulunci, domin kuwa, tun kafin yin hijira daga Makka zuwa Madina da kamar shekara guda a lokacin da aka yi Isra’I da Mi’iraji da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Mala’iku masu yawa sun nusar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da yin amfani da ƙaho da kuma bashi muhimmancin gaske. Don haka, Manzo (SallallahuAlaihi Wasallam) ya yi ƙaho; kuma ya biya wanda ya yi masa ƙahon lada.

Matsayin Ƙaho:

Ƙaho abu ne da yake da babban matsayi da gagarumar falala, wanda har hakan ya sa Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ƙaho ne mafi alherin abin da mutane suke yin magani da shi”.

Ranakun da Ake Yin Ƙaho a Cikin Wata:

Ga mai son ya ci cikakkiyar gajiyar yi ƙaho, to, ya yi shi a ranar sha bakwai (17) ko sha tara (19), ko kuma ranar ashirin da ɗaya (21) ga watan shekarar Hijira. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “wanda ya yi ƙaho a ɗaya dagacikin waɗannann ranakun; da izinin Allah ƙahon zai zamar maganin duk wata cuta”.

Ranakun da Ake Yin Ƙaho Cikin Sati:

Ga mai son ya yi ƙaho a ranakun da suka dace daga cikin ranakun sati, to ya yi a ɗaya daga cikin waɗannan ranaku uku masu zuwa: Ranar Litinin, Talata da Alhamis.

Ranakun da ba a Yin Ƙaho a Cikinsu a Sati:

An karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda da su, ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku nisanci yin ƙaho a ranar Laraba, da Juma’a, da Asabar da kuma ranar Lahadi…”.

Fiyayyen Lokacin da Ake Yin Ƙaho a Cikinsa:

Yin ƙaho da safe kafin Karin kumallo shi ne fiyayyen lokacin da ake yin ƙaho a cikinsa.
Guraren da Ake Yin Ƙaho
Ana yin ƙaho a sassa daban-daban na iki, kamar yadda aka rawaito cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ƙaho a ƙafa da kafaɗu da gyaffan wuya ko mahaɗar wuya da baya, kuma ya yi ƙaho a ka.
Kuma ana iya gudnar da ƙaho a wasu guraren daban daga waɗanda aka ambata a sama, gwargwadon buƙata.

Amfanin ƙaho:

 Ƙara hankali.
 Ƙara kaifin hadda.
 Maganin cututtukan jiki.
 Rage yawaitar jinni don daidaita gudanarsa
 Rage maiƙon cikin jinni
 Maganta matsanancin ciwon kai.
 Rage yawan majinar jiki.
 Kara wa sinadaran yaƙar cututtukan jiki ƙarfi
 Raba jiki da guba

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceHaƙƙoƙin Da Ma’aurata Suke Tarayya A Kansu
Labarin na GabaHaƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata