Tag: ilimin lafiya

  • Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon Suga (Diabetes)

    Ciwon suga sinadari ne mai matuƙar amfani a jikin mutum. Ana samun sa daga abincin da muke ci da kuma abubuwan da muke sha.

    Idan suga ya yi yawa, ko kuma ya yi kaɗan a jikin mutum, ana iya kamuwa da rashin lafiya wadda za ta iya sanadiyar mutuwar mutum idan ba a ɗau mataki ba.

    Akwai wani sinadari da ake kira insulin a jikin ɗan Adam. Sinadarin insulin shi ne yake kula da daidaituwar sinadarin suga a cikin jini. Idan mutum ya ci abinci mai dauke da sinadarin suga (carbohydrate), sai sugan ya koma cikin jini bayan ya narke. 

    Sai sinadarin insulin ya zo ya daidaita suga, domin kada sugan ya cutar da jiki. 

    Ma’anar ciwon suga, cuta ce wadda take faruwa sanadiyyar ƙaruwar yawan sinadarin sikari (suga) a cikin jini na tsawon lokaci. Cutar tana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin, ko kuma insuin ɗin ya daina aiki gaba ɗaya.

    Rabe-raben Ciwon Suga

    Rabe-raben ciwon suga suna da yawa, amma za mu yi magana a kan guda uka kawai:

    1. Type I Diabetes

    Wannan nau’in ciwon sugan, yana faruwa ne idan jikin mutum ya daina samar da sinadarin insulin.

    Idan sugan  mai wannan nau’in ciwon sugan ya ƙaru, ba zai sauka ba, saboda babu insulin. Idan kuwa ana so ya sauka, to dole sai an yi allurar insulin.

    Wannan nau’in  ya fi kama yara. Haƙiƙanin abin da yake janyo wannin  nau’in ciwon ba a san shi ba, amma dai an tabbatar da cewa ana iya gadon ciwon daga wurin mahaifa(iyaye)

    2. Type 2 Diabetes

    Wannan nau’in yana farawa ne idan sinadain insulin ya daina aiki, ko kuma aikinsa ya ragu. Idan sugan mai wannan nau’in ya ƙara, ba zai sauka ba, har sai an sha maganin da zai dawo da aikin insulin.

    Wannan nau’in ya fi kama manya.

    Abubawan da suke janyo haɗarin kamuwa da wannan nau’in sun haɗa da:

    Ƙiba: Ƙiba mara misali, musamman wadda ta haura ma’aunin Body Mass Index (BMI) 3okg/M2.

    Rashin kazar-kazar: Waɗanda ko yaushe a zaune suke, ba sa kai-kawo, ba sa aiki kuma ba sa son aiki.

    Cin abincin da ba shi da inganci a likitance: Yawan cin abinci, musamman wanda yake ɗauke da sinadaran cholesterol, suga, fat masu yawa a cikin su. Misali butter, chees, lemukan roba da na gwangwani, Askirin (lce cream) da sauransu.

    Shan giya

    Gado: Idan mahaifi ko mahaifiya suna da ciwon suga.

    3. Gestational Diabetes

    Wannan nau’in ciwon suga yana faruwa ne ga masu juna biyu (ciki).

    Yanayin su ɗaya da Type 2 Dm. Sai dai ana warkewa daga wannan nau’in bayan an haihu. Ana iya ba su magani su sha, ko kuma a yi musu allurar insulin idan ana so suga ya daidaita.

    Alamomin ciwon suga

    i. Yawan fitsari  fiye da misali.

    ii. Yawan shan ruwa fiye da misali.

    iii. Yawan cin abinci fiye da misali.

    Illolin ciwon suga

    Masu gajeren zango: Su ne waɗanda suke faruwa a ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma suna iya sanadiyyar mutuwar mutum nan take. Sun haɗa da:

    a. Suga ya yi yawa sosai a jinin mutum, yawan da ya wuce hankali; irin wannan matsalar tana janyo mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma mutum ya rasa ransa a nan take.

    b. Suga ya yi ƙasa; wannan idan mutum yana shan maganin suga ko allurar cutar suga (insulin) fiye da yadda jikinsa yake buƙata; yana iya janyowa mutum ya yanke jiki ya faɗi ko kuma ya fita daga hayyacinsa.

    Masu dogon zango: Su ne waɗanda suke faruwa bayan mutum ya daɗe da ciwon suga a jikinsa.

    Misali:

    Ciwon ƙoda.

    Ciwo ko kuma gyambon ƙafa, wanda zai iya janyowa a yankewa mutum ƙafa.

    Ciwon ido wanda zai iya janyowa mutum ya makance.

    Ciwon zuciya.

    Cutar shanyewa ɓarin jiki

    Da sauransa.

    Magani/Shawarwari

    Magungunan ciwon suga, kala biyu ne. Akwai na ƙwaya da kuma allura.

    Idan mutum yana da ciwon suga, yana da matuƙar muhimmanci ya dinga yin waɗannan ababuwan:

    Shan magani ko yin allura a kan ƙa’ida.

    Yawan duba sinadarin suga akai-akai.

    Yawan motsa jiki a ƙalla san huɗu a sati kamar tafiyar ƙasa ta tsawon minti talatin.

    Daina shan giya

    Rage shan kayan zaƙi masamman lemukan gwangwani ko na roba.

    Rage cika ciki da abinci mai sinadain sikar (carbohydrate) a ciki kamar shinkafa, tuwo, masara, doya da sauransu.

    Yawaita cin ganyayyaki kamar su alayyahu, zogale, rama, ganyan salak da sauransu.

    Kammalawa

    Ciwon suga ciwon ne mai haɗarin gaske. Har yanza babu maganin da yake warkar da ciwon gaba ɗaya.

    Amma ana iya shan magani ko ayi allura domin a zauna lafiya. Don haka shan magani da zuwa asibiti ya zama wajibi ga duk mai cutar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Ciwon Sikila (SICKLE CELL DISEASE) danna nan.

  • Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.

    Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.

    1. Kuɗi

    Waɗansu mutanen gani suke yi, ba mai more rayuwa a duniyar nan da samun natsuwa sai mai kuɗi. Shi ne kawai yake iya huce haushin duniya, ai in ka sami kuɗi ka sami komai, ka haye ka wuce tsara, ka fi ƙarfin raini, haka suke gani.

    To amma shin kuwa abin haka yake mai kuɗi shi ne yake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali?

    Bari mu ga waɗannan ‘yan misalai guda biyu:

    Ƙaruna biloniyan biloniyoyin duniya.

    Tun da Allah ya yi duniya ba a taɓa mutum mai mahaukaciyar dukiya ba irin Ƙaruna.

    Alƙur’ani ma da kansa ya jinjina irin tarin dukiyar da Allah ya mallaka masa. Ya zama tauraron duniya son kowa ƙin wanda ya rasa. Duk inda ya yi, sai sha’awarsa ake yi, ana haɗiyar yawu, ana ina ma ni ne Ɗanƙaruna. Yana takawa ɗaiɗai, yana hura hanci yana ganin ya fi kowa, babu wanda ya isa sai shi.

    Amma a ƙarshe kuɗinsa ne suka jawo masa halaka. Saboda irin girman kai da ɗagawa da ya rinƙa yi Allah ya halakar da shi da dukiyarsa. Karanta sura ta 28, suratul Ƙasas ka sha labari.

    Christina Aunasis

    Wata hamshaƙiyar biloniya ce yar ƙasar Jamus, wacce ta gaji dukiya ta fitar hankali daga iyayenta. Ubanta ya mutu ya bar mata tsabar kuɗi wuri na gugar wuri Dala miliyan dubu biyar da jiragen ruwa maka-maka, da na sama jibga-jibga, kai har tsibirai ubanta ya bar mata, ba a ma maganar gidaje gonaki da filaye. To shin wannan dukiya ta kawo mata zaman lafiya da kwanciyar hankali?

    Ga taƙaitaccen labarinta. Uwarta dai ta mutu cikin baƙin ciki da mummunan yanayi, bayan ubanta ya wulaƙanta ta ya sake ta. Yayanta kuma jirginsa na sama ya hau yana ta wasan asha-ruwan-tsintsaye a kai, sai kawai ya rikito da shi ya mutu. Shi Kuma ubanta neman suna ne ya kai shi ya auri tsohuwar matar tsohon shugaban Amurka “John Kennedy”. Duk da ta kafa masa sharaɗin ba za ta yarda ya kwanta da ita ba, kuma ba wani umarni nasa da za ta ɗauka ga kuma miliyoyin daloli da ya kashe-kashe, amma ka san mai jan kunne da neman suna….. duk da haka zaman bai yi daɗi ba ya sake ta. Haka dai ya mace cikin damuwa da alhini.

    Yanzu saura “Christina” ita kaɗai tare da ɗimbin dukiyarta. Da farko ta auri wani ɗan Amurka, amma ba a shekara ba ta sake shi. Sai ta tafi “Grecce” ta sake yin aure, shi ma abin bai yi daɗi ba, ta sallame shi.

    Daga nan sai ta nufi Rasha Kasar gurguzu, inda ba a yarda mutum ya zamo mai kuɗi ba, duk da haka ta yarda ta auri wani ɗan Rasha ta zauna ita kaɗai, ko yar aiki ba ta da ita, da ‘yan jarida suka tambaye ta yaya haka kuma? Sai ta ce, “Lalube nake ko na sami kwanciyar hankali”. Shekararta ɗaya a Rasha ta saki wannan miji. Sai ta nufi Faransa.

    A can ta auri wani Bafaranshe, aka yi gagarumin biki, ‘yan jarida suka tambaye ta game da dukiyarta sai ta ce: “Ni ce macen da ta fi kowa kuɗi a duniya, kuma ni ce macen da ta fi kowa hankali a duniya!”

    Bayan sun haifi ‘ya mace da wannan bafaranshe sai ta sake shi. Kai a ƙarshe dai tsintar gawar ta aka yi a Ajantana har yau ba a san dalilin mutuwarta ba.

    A gaskiya kuɗi dai shi kaɗai bai isa ya tabbatarwa da mutum zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Shi dai neman sa wahala, in an samu ba hutu, saboda tsoron kada su ƙare. Ga yawan tunani da damuwa. Ga tsoron ‘yan fashi ɓarayi da ‘yan ina-da- kisa, da zalunci a gwamnati, ba cikakken zama, ballantana isasshen barci, abinci ma ba shi da cikakken lokacinsa, ballantana iyali. Kai tashin hankalin yana da yawa. Allah ya kyauta, ya kuma ba mu na rufin asiri.

    2. Suna

    Waɗansu kuwa sukan ɗauka cewa kwanciyar hankali yana cikin yin suna. A ɓangaren wasan kwaikwayo da wasannin motsa jiki kamar ƙwallon ƙafa kokawa da sauransu. Masu irin wannan tunani za ka ga suna matuƙar sha’awar taurarin ‘yan wasa da shahararrun gwanaye a ɓangaren wasannin motsa jiki.

    To amma masu wannan tunani sun tafka kuskure, saboda babu waɗanda suka fi taurarin ‘yan wasa tashin hankali da rashin zaman lafiya. Ka ɗauki ƙwallon ƙafa, misali irin faman wahala da suke sha wajen gwaji (training) da wulaƙanta da suke kafin su cancanci zama zakaru, ga rashin zama wuri ɗaya, da dama daga cikinsu sukan salwantar da karatunsu saboda ƙwallo. Sukan shiga halin tsoro da faɗuwar gaba duk lokacin da za su kara da wani kulob. Idan kuwa ba su yi nasara ba, ai sun shiga uku a wajen magoya bayansu, za su sha la’ana da zagi, wani lokacin ma har da duka.

    Kuma ba wuya an mance da mutum, an koma kan wani gwarzon, shi kuma an jefa shi a kwandon shara. Daga nan sai ya shiga rayuwar takaici da ɓacin rai, musamman ganin ana yi babu shi. Haka dai zai ƙare ya mace a wulaƙance.

    To don Allah ɗan uwa ina abin sha’awa a nan.

    To in ka ɗauki ‘yan wasan kwaikwayo su ma haka suke, farkonsu shaye-shaye da lalata da rashin zama wuri ɗaya, rashin mutunci, rashin kunya ga zunubin ɓata tarbiyya, sannan kuma da tauraron mutum ya disashe, sai a tattara shi a koma wani. Ya mutu a banza ba addini ba adila. Shin yau ina su Pele James Brown, Amita, Dram, Danhaki, Gaso-rogo da sauransu?

    To haka ma kwanan nan za ka daina jin su wane da wance, an koma gefe ana nadama marar amfani. A gaskiya babu wata nutsuwa da kwanciyar hankali cikin waɗannan wasanni. Allah ya ganar da mu amin.

    3. Mulki

    To ko a cikin mulki da riƙon muƙamai sirrin zaman lafiya yake?

    Waɗansu da dama suna ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali na ga mulki, haka suke gani. Amma ga mai lura ya san abin ba haka ba ne. Ɗauki masu riƙe da muƙamin siyasa a yau, ga dai kuɗin kamar na Ƙaruna, ga su ɓulɓul da manyan riguna, gidaje da motoci da sauran kayan alatu. Amma shin suna iya watayawa cikin ‘yanci kamar kowa?

    Ai ko wawa ya san wannan guje-guje da rundunar yaƙi da take biye da su, ba na lafiya ba ne. Kuma wace irin wahala ce ba a sha ba kafin a samu mulkin? Sannan in an samu, sai a kasa zaune a kasa tsaye ana tsoron sharrin ‘yan adawa da kuma gushewar mulkin. Daga nan sai cutar tazarce ta kama mai mulki.

    Sai hauma-hauma da danniya ko ta-zarce ko ta-kauce. In ta-zarce ƙarin matsala in kuwa ta-kauce to sai dai a lallaɓa “Chairman” domin har hauka ta-kauce kan haifar, komai zai iya faruwa.

    Akwai ɗimbin misalai a kan wannan batu nawa. Shin ina su Fir’auna da Hamana? Ina su Shah na Iran, Ferdinand Marcos na Filfin, da Mabutu na Zaire da Abacha na Nijeriya. To ai duk ba a nan take ba, in fa ba a shimfiɗa adalci ba, to tashin hankali sai an je lahira. Allah ya tsare mu. Amin.

    To kaga dai zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaskiya babu shi a cikin mulki sai in a lahira ga shugaban da ya yi adalci.

    4. Wayewar kai da ci gaba

    In haka ne za mu iya cewa wayayyun mutane waɗanda suka ci gaba suke da fasahar ƙere-ƙere da ƙirƙire-ƙirƙire su ne masu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wato dai kamar irin su Amerika da ƙasashen Turai da ‘yan boko-addini. To amma bari mu yi nazarın su, su ma mu gani.

    A gaskiya duk ɗan boko da ya amsa sunansa ya san irin firgici da tashin hankali da Turawan yamma da na gabas suke ciki abin sai su. Tarbiyya ta daɗe da yin ƙaura daga wannan yanki har an mance da sunanta. Mutunci ba a yayin sa. Tuni mutanensa suka faku. Rayuwar ƙunci kuwa da fatara da rashin sanin inda aka dosa, sai wanda ya zauna da su ko yake karanta littattafai da mujallu da suke fitowa daga can.

    Wannan shi ne ya sanya a koda yaushe suke kashe kansu ta hanyar rataye kai, ko shan guba ko kuma bindige kai, to don Allah ɗan uwa ina zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan rayuwa.

    Mai karatu ruɗani game da hanyoyin samun nutsuwa yana da yawa ta yadda waɗansu Wawayen ma gani suke yi ta hanyar shaye-shaye da aikata miyagun laifuka kamar zina, liwaɗi, fashi da sauransu, wai ta waɗannan hanyoyi za su iya cimma burinsu. Amma ina! Sai ka ga waɗannan mutane su suka fi kowa shiga tasku cikin rayuwarsu. Haka nan sukan rayu cikin tsiya da wahalar zuciya kuma su yi mummunar mutuwa, su je su tarar da mummunar makoma.

    Allah ya tsare mu.

    To mai karatu tun da dai mun ga babu ci cikin waɗannan abubuwa to mene ne haƙiƙar abin da ya ke hana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? Karanta waɗannan babi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Su Ke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Akwai abubuwa da dama waɗanda suke kawo tabbataccen da dauwamammen zaman lafiya da tabbataccen kwanciyar hankali ga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi, kai har da duniya ma gaba ɗaya.

    Amma duk waɗannan abubuwa in aka dunƙule za su iya zama abu ɗaya tak, shi ne imani da bin dokokin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wannan shi ne zai yi wa mutum jagoranci domin samun nutsuwa da hutun zuciya maras misalı, kuma ya zauna da kowa lafiya ta hanyar bai wa kowa haƙƙinsa.

    Ga kaɗan daga cikin waɗannan abubuwa:

    1. Imani da aiki nagari

    Allah Ta’ala ya ce: Duk wanda ya aikata aiki nagari, namiji ne ko mace, kuma yana mai imanı, to za mu raya shi rayuwa mai daɗi. (Suratun Nahl: 97). Kuma Allah yana cewa: “Waɗanda suka yi imani da Allah da ranar lahira, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba” (Sura Mai’da” 69).

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce, “Lamarin mumini yana da ban mamaki, komai nasa alhairi ne, in ban da mumini babu mai samun haka. Idan alheri ya same shi, sai ya gode wa Allah, sai ya zama alhairi, in kuma sharri ya same shi, sai ya yi haƙuri, wannan sai ya kasance alhairi a gare shi” (Muslim 18/125).

    Wannan hadisi yana nufin in dai akwai Imani a zuciyar mutum, to babu wani abu a duniyar nan da zai dagula masa lissafi, ya hana shi sakat, ballantana ya tayar masa da hankali.

    Mu ɗauki misalin wani mumini guda ɗaya, shi ne Shaihul Islam Ibn Taimiyya. Wannan bawan Allah ya shiga tasku iri-iri, ya sha ɗauri da duka da korar kare daga garinsu, laifinsa kawai shi ne, dagewa da matsanancin naci kan gaskiya, kai a ƙarshe dai a kurkuku ya mutu. A dab da mutuwarsa, yake faɗa a cikin kurkukun Dimashƙa: “Babu fa yadda maƙiyana za su yi da ni, ni aljannata da lambuna yana cikin zuciyata, duk inda na je, ina tare da ita ba na rabuwa da ita, ɗaure ni, halwa ce, kashe ni shahada, in kuma an kore ni, na samu damar yawata duniya domin nazarin ayoyin Allah da ikonsa.

    Allahu Akbar! Allah ya jiƙan maza, maza sun faɗi.

    2. Imani da ƙaddara

    Ya ɗan’ uwa mai karatu, in kana fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka yarda da cewa duk abin da ya faru a duniyar nan, gare ka ko ga waninka, mai daɗi, ko marar daɗi, to haka Allah ya nufa, haka ya so, haka ya ƙaddara, kuma in duk duniyar nan za ta haɗu a kan a canja wannan abu, ba zai yiwu ba. To in ka yarda da haka, sai ka huta wa zuciyarka, ka sami nutsuwa.

    Ga wani misali mai ƙayatarwa, ciwon daji ya fito a ƙafar Urwatu Ibnuz Zubair (Radiyallahu Anhu ) sai Likitoci suka ce za su ba shi giya ta bugar da shi, domin a guntule ƙafar cikin sauƙi. Sai ya ce atafau ba zai yarda ya sha giya ba ta kowane hali. Sai ya ce, “In so kuke sai lokacin da hankali na ya gushe za ku guntule min ƙafa, to ku bari sai na fara sallah”.

    Hakan kuwa aka yi, yana sallah aka guntule ƙafar, bai ko motsa ba, sai da aka tsoma dungulmin cikin tafasasshen mai, sai ya suma. Can cikin dare sai ya farka, ya ji ana yi masa jajen kafarsa da kuma ta’aziyyar mutuwar ɗansa a wannan ranar! Amma saboda tsabar imani sai ya ce “Alhamdu lillahi tun da Allah ya ba ni lafiya kuma ya bar mun ɗaya ƙafar da ragowar ‘ya’yan.

    Allahu Akbar! ka ji salaf na gaskiya, to yanzu wane abu ne zai iya tayar da hankalin wannan bawan Allah?

    3. Ilmin Addini

    Ilmi shi ne gishirn rayuwa, shi ne fitila mai kau da duhun jahilci da talauci da ɓacin rai da duk wata damuwa. Mai ilmi yana cikin farin ciki da daɗin da ba wanda zai iya siffanta shi, sai wanda ya shige shi, saboda babu tsoron kowa a zuciyarsa, sai na Allah.

    An yi wani azzalumin sarki a Masar mai suna Ahmad Ibn Tuluna, wanda aka ce ya kashe sama da mutum dubu goma sha takwas (18,000) ta hanyar hana su ci da sha, har sai sun mutu.

    Kowa yana tsoron wannan mamuguncin sarki, amma wani malami mai suna Abul Hasan Zahid (Radiyallahu Anhu) ya yi ta maza, ya yi shahada ya fuskance shi, ya je ya yi masa wa’azi kan irin ta’asar da yake aikatawa. Ai fa nan da nan ya harzuƙa, ya kufulo, ya sa aka damƙe wannan malami aka jefa a kurkuku. Ya sa aka kamo zaki, aka hana shi abinci kwana uku, sannan aka tura shi ɗakin da malam yake.

    Wayyo! Ɗan uwa me kake zato zai faru? Ai malam ko a jikinsa, yana zaune ya fuskanci alƙibla, ya Sunkuyar da kansa kamar mai tunani. Shi kuwa zaki sai ya yi ta kewaya malam yana kaɗa jela kamar kare ya ga uban gidansa. Da ya gaji sai ya fito ya kama gabansa.

    Wannan abu ya bai wa kowa mamaki musamman wannan azzalumi (Ɗan Tuluna), waje ya ruɗe da kabbara da godiya ga Allah, saboda kuɓutar malam Abul Hasan. Shi da kansa Sarki ya zo ya ba shi haƙuri, ya ce, “Don Allah wai tunanin me kake yi lokacin da zakin nan ya yiwo kanka, na ga kai ko damuwa da shi ba ka yi ba?

    Sai ya ce, “Ai ni a lokacin tunanin hukuncin miyan zaki nake yi idan ya taɓa ni, shin najasa ne ko tsarkakakke? Sannan ya ce to ba ka ji tsoron zakin ba? Sai ya ce sam Allah ya yaye min wan nan. Kai ɗan uwa in ka na son jin daɗi na gaskiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali to ka nemi ilimin addini saboda Allah kuma ka yi ƙoƙarin aiki da shi. Allah ya sa mu dace.

    4. Yawan ambaton Allah da karatun Ƙur’ani

    Allah Ta’ala ya ce: “Ku faɗaka da ambaton Allah ne zukatu suke nutsuwa (Suratur Ra’adi:28).
    Duk mutumin da yake yawaita zikiri, zai rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wanda kuwa bai damu da zikirin ba, ya shiga uku.

    Allah Ta’ala ya ce: “Wanda ya kau da kai daga ambaton Allah, za mu hore masa wani shaiɗani ya kasance tare da shi (Suratu Zukhruf: 86). Kuma ya ce: “Duk wanda ya kau da kai daga Ambato na, to haƙiƙa rayuwar ƙunci za ta tabbata a gare shi, kuma za mu tashe shi ranar ƙiyama makaho (Surat Taha: 124).

    Kuma Allah ya ce: “Bone (azaba, wahala, tashin hankali) ya tabbata ga masu busasshiyar zuciya daga ambaton Allah, waɗannan suna cikin ɓata bayyanan ne” (Surat Zumar:22).

    Waɗannan ayoyın suna nunı ga tasirin da zikiri ya ke da shi wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma ya kamata ka sani cewa, zikiri kala-kala ne, wannan ya haɗa da karatun Ƙur’ ani da hadisi da ilmin Musulunci da addu’o’in ma’aiki, tun daga wayewar garı, har kwanciya barci, tunani kan ikon Allah da hikimominsa, tuna Allah lokacin aikata alhairi ko sharri, hailala, tasbihi, istigfari salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da sauransu.

    Sannan ka sani cewa zikiri da duk wata ibada ba za su yi amfani ba, sai an yi su saboda Allah kuma daidai da yadda Allah da Manzonsa suka yi umarni, babu ƙari, babu ragi. Allah ya ganar da mu.

    5. Sakin rai

    Ya ɗan’uwa, in kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka saki ranka ka tsarkake Zuciyarka daga duk wani dagwalo da tsatsa, waɗanda suke tayar da hankali irinsu hassada da girman kai da gaba da ganin ƙyashi da riya da jiji da kai da sauransu.

    6. Kyautata wa mutane

    Kyautata wa mutane ta hanyar nuna musu ƙauna da fatan alheri, da taimakonsu, da ba wa kowa haƙƙinsa, da girmama su, yana da tasiri mai ban mamaki wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Mutum mai alhairi yakan samu karɓuwa da farin jini a cikin al’umma, kai yakan fi waɗanda ya kyautatawa jin daɗi da farin ciki. Wannan abu an gwada an gani, yi ƙoƙari ka shiga cikin ayarin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    7. Ka hangi na ƙasa da kai, ka daina hangen na sama da kai

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Ku rinƙa duban na ƙasa da ku, ku dai na hangen na sama da ku, saboda kada ku raina baiwar Allah a gare ku”. (Muslim ne ya rawaitoshi).

    Wannan Hadisi ya shimfiɗa ƙa’idar zaman lafiya da kwanciyar hankali, wato a kullum kada ka raina baiwar da Allah ya yi maka, duk halin da kake ciki ko mai muminsa, in ka duba ƙasa za ka ga ka fi waɗansu da dama, ka ga sai ka ji daɗi ka gode wa Allah, hankalinka ya kwanta. Amma idan kana hangen waɗanda suka fi ka, to ka shiga cikin taskar wahala da tashin hankali ke nan.

    Sai dai kuma wannan ya shafi abin duniya ne kawai, amma a harkar ilmi da addini, so ake yi kullum ka rinƙa hangen na sama da kai, domin ka yi himma ka yi koyi da su. In kuwa kana duban na ƙasa da kai a ilimi da ibada, sai lalaci da girman kai ya kama ka, shi ke nan kuma sai komai ya ruguje.

    8. Gajarta buri

    Ka sani cewa rayuwar nan ta duniya taƙaitacciya ce, saboda haka, kada ka sake ka taƙaice ta da yawan tunane-tunane da damuwa kan abin da bai zo ba ko kuma wandą ya riga ya wuce. Ka sani cewa rana da wata ba za su tsaya jiran ka ba, yi ƙoƙari ka amfani lokacinka da ayyukan alhairi, kada ka rinƙa dogon buri.

    Wata rana waɗansu mutane masu tsoron Allah suna tattaunawa kan gajarta buri. Sai ɗaya ya ce: “Ni a yanzu in na kai loma ɗaya bakina, ba na sa ran zan sake kai ta biyu” . Ɗayan kuwa sai ya ce, “Cafɗi-jan! Kai kana da ɗauka da yawa. Ai ni duk yayin da na ja numfashi ba na sa ran zan sake jan wani!” Allah Akbar, ɗan uwa duk wanda bai ɗauki duniyar nan da zafi ba, to haƙiƙa shi ne cikakken mai zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    9. Yarda da cewa rayuwar lahira ita ce haƙiƙar rayuwa

    Duniya ba gidan zama ba ce, hanya ce kawai da mutum zai bi zuwa gidansa na rayuwa, wacce ba ta da ƙarshe, ko cikin daɗi ko wuya. Wanda duk wannan aƙida ta tabbata a cikin zuciyarsa, to haƙiƙa rayuwarsa ta duniya za ta zama mai sauƙin gaske, shike nan sai ya yi ta tanadin samun tsira ranar lahira a nan duniya, kuma sai ya zauna lafiya cikin kwanciyar hankali.

    Ga wani labari mai ban sha’awa na Al-Hafiz bn Hajar (Radiyallahu Anhu) a lokacin da ya ke alƙalin Misra. Wata rana ya fito cikin kwarjini da ado, sai wani Bayahude cikin tsummokara da jigata ya tsayar da shi, ya ce, “Ranka ya daɗe, tambaya nake”. Sai ya ce, “Bismillah”. Sai ya ce, “An ce Annabinku ya ce, “Duniya kurkukun mumini ce, kuma aljannar kafiri ce”, to yaya aka yi ni nake cikin wannan hali na tsiya, kai kuma ga ka cikin daula?

    Sannan Hafiz ya ce: “I, duk da wannan ni’ima da na ke a ciki, in an kwatanta da ni’imar aljanna, sai ka ga kamar a kurkuku nake.

    Kai kuma duk da wahalar da kake fama da ita yanzu, in an auna da azabar da za ka gamu da ita a lahira, sai ka ga yanzu kai a aijanna kake”. Sai ya ce, “Haka ne”? Sai ya ce, “Ƙwarai kuwa”. Nan take sai Bayahuden nan ya musulunta!

    Saboda haka, ɗan uwa duk halin da kake ciki, ka da ka mance da lahira, domin ta fi duniya nesa ba kusa ba a ɓangaren daɗi ko wuya.

    10. Zama da mutanen kirki

    Haƙiƙa mutanen kirki muminai, masana, masu aiki da saninsu, masu tsoron Allah, su ne suke cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. To saboda haka, idan kana so kai ma ka sami haka, sai ka yi fatali da lalatattun abokai, ka yi abota da mutanen kirki, waɗanda za su nuna maka hanyar Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce:”

    Misalin aboki nagari da lalataccen aboki, kamar wanda yake zaune ne da mai sayar da turare da wanda yake zaune da maƙeri. Shi dai wanda yake sai da turare, ko bai fesa maka ba, za ka shaƙi ƙamshi. Shi kuwa maƙeri ko dai ya ƙona ka, ko ka taso da ƙaurin wuta. (Buhari/Muslim). Wato dai zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.

    11. Yin afuwa da kyautatawa wanda ya ɓata maka

    Tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa, ballantana tsakanin mutum da mutum, kuma Duk wanda ya ce: “Zo mu zauna, ya ce zo mu ɓata. Waɗannan kalmomi ne na hikima, masu ɗauke da darussa na rayuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. To maganin saɓawa haƙuri da yin afuwa, saboda tilas sai ka ga yadda ba ka so, in kuwa ka ce duk abin da aka yi maka sai ka rama, to lallai wata rana za ka rame. Yin afuwa yana janyo wa mutum mutumci kwarjini, farin jini lada da farin ciki da kwanciyar hankali. Ga waɗansu ‘yan misalai:

    Waɗansu miyagun malamai sun taɓa haɗe wa Shaihul Islam Ibn Taimiyya kai, suka yi ta cutar sa, har suka yi masa sharri, aka jefa shi a kurkuku.

    Lokacin da aka sake shi, sai aka tambaye shi, ko kana tunanin ɗaukar fansa? Sai ya ce, “A’a, duk na yafe musu, ba komai, Allah ya saka musu da alhairi, wannan zaman kurkuku ya sa na yi nazarin Kur’ani na fahimci waɗansu abubuwa da dama, kuma ai su ne sanadi, na yi musu afuwa, ba wani abu”.

    Wani bawan Allah ya sami labarin cewa, wani mutum ya yi da shi, ya ci zarafinsa. Sai ya ɗauki goma ta arziki, ya tafi da kansa ya kai masa har gida. Sai mutumin ya tambaye shi dalilin wannan alhairi. Sannan ya ce, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi muku alhairi ku saka masa.” To kai ka ba ni kyautar ladan ayyukanka, ni kuma ba ni da wani abu da zan saka maka da shi, sai ɗan wannan abin duniyar. Allahu Akbar. Ɗan uwa ka ɗauki ɗabi’ar afuwa ga iyalanka, maƙotanka, da sauran al’umma, ka ga yadda za ka zauna lafiya, ka samu nutsuwa.

    12. Daddaɗar Magana

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya faɗi alhairi ko ya yi shiru”.
    Duk mutumin da yake aiki da wannan hadisi, haƙiƙa zai zauna lafiya da kowä, kuma zai samu kwanciyar hankali. Duk abin da zai fito daga bakinka ya kasance alhairi ne, magana ce ta gaskiya mai daɗi wacce ba za ta ɓatawa kowa ba.

    13. Addu’a

    Komai ya yi zafi maganin sa Allah. Kuma addu’a makamin mumini ce. Saboda haka bayan bin waɗannan mataki da sauran su, sai ka kasance kullum cikin roƙon Allah ya ba ka zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman ka riƙi addu’o’in zaman lafiya na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kamar wannan addu’ar.

    Allahumma aslih lii diini allazi huwa ismatu amri, wa aslih Ii dunyaa ya allati fiiha ma aashi wa aslih lii aakhirati allati fihaa ma aadii, waj alil hayaata ziyaada talli fii kulli hairin waj alil mauta raahatalli min kulli sharrin.

    Allahuma rahmataka arju fa laa takilni ila nafsi tarfata ainin wa aslih lii sha’ani kullihi laa ilaaha illa anta.

    Allahuma inni a ‘uzu bika mnial hammi wal hazani wa minal jubni, wal bukhli, wa min galabatid daini wa ƙahnimijaali.

    Waɗannan kaɗan ke nan daga abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A dunƙule za mu iya cewa bin Allah da Manzonsa sau da ƙafa da tsarkake zuciya da jiki da mazauni da baiwa ƙwaƙwalwa lafiyayyen abincin imani da kyakkyawar niyya, su ne kaɗai za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Allah ya sa mu da ce. Amin.

    Bayan waɗannan ƙa’i’do’ji, malamai musamman masana halin ɗan Adam, suna bayyana waɗansu ladabai ko dabaru domin zaman lafiya da mutane iri-iri. Ko da yake waɗannan ƙa’idoji da suka gabata, sun isa ga duk mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rayu da su, amma duk da haka akwai waɗansu abubuwa da masana suka yi bayani, Ina ganin ya kamata a kammala wannan littafi da su.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Wanna nan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

    Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

    Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne burin dukkan ɗan Adam maza da mata; manya da yara musulmi da kafiri babu wani saɓani.

    Za mu iya cewa, yanayin nutsuwa da jin daɗi da farin ciki, annashuwa da samun gamsuwa a zuci Ga kuma waje; ba tare da wani tsoro ko fargaba ko damuwa ba, a kan abin da ya wuce, ko tsoron abin da zai zo; waɗannan abubuwa in sun haɗu, ana iya kiran su zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Wannan an ɗan kusanto da ma’ana ce kawai, amma a gaskiya sanin haƙiƙanin zaman lafiya da kwanciyar hankali sai wanda yake cikinsa. Larabawa suna kiran sa “Sa’adah” kuma suna fassara shi da cewa kishiyar wato tsiya.

    Rukunan zaman lafiya da kwanciyar hankali guda uku ne:

    1. Ingantacciyar zuciya da jiki.
    2. ingantacciyar rayuwa.
    3. Kyakkyawar makoma.

    Duk mutumin da zuciyarsa ta gurɓata da kafirci da bidi’a da zalunci da sha’awa da sauran su, ko jikinsa ya yarda da lalaci da son hutu kowane lokaci da karɓa ba bayarwa, haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya, ballantana kwanciyar hankali.

    Haka kuma duk mutumin da ya ɗaukar wa rayuwa ta ƙarya, mara tabbas, mai cike da ruɗani da hauma-hauma, wacce ba ta da wani tushe ballantana makama, shi ma ba zai shiga cikin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

    Sanin kyakkyawar makoma da tabbacin inda aka dosa yana da muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Yanzu a haɗa musulmi da ya yarda da Allah da ranar Lahira da wuta da aljanna, da kafiri wanda shi kawai duniya ita ce farko ita ce ƙarshe a wurinsa?

    To amma wacce hanya ce mafificiya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? To mai karatu sai in ce maka nan fa ake yin ta; saboda duk mutumin da ka yiwa wannan tambaya, zai ba ka amsa saɓanin ta ɗan’uwansa. Mutane da yawa suna cikin ruɗani game da wannan amsa; kowa kuma aiki yake yi tuƙuru domin tabbatar da ita a kan kansa.

    Amma fa kashi casa’in bisa ɗari sun yi hannun riga da hanyar ba da amsa ingantacciya. Kafin na ba da amsa, bari mu yi nazarin kaɗan daga cikin ruɗu da mutane da dama suke ciki, game da hanyoyın samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita

    Yadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita

    Yayin da aka tabbatar da mayu sun kama mutum; ko kuma kambun baka ne ya kama mutum; akan umarce shi da ya yi wanka; sannan ya yi alwala sai ya karanta waɗannan ayoyin kamar haka;

    • Fatihatul kitab
    • Ayatul kursiyyu
    • Ƙarshen suratul ? Baƙarah wato Amanar rasul
    • Suratun Nas
    • Suratul Falaƙ
    • Sannan ya tofa a cikin ruwa ya sha sai kuma ya tofa a hannunsa ya shafe jikinsa. Sannan zai iya karanta su a cikin man zaitun sai ya rinƙa shafawa. Da yardar Allah nan take zai samu lafiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Kariya Daga Sharrin Maƙiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Farin Jini Da Kwar Jini A wajen Al’umma danna nan 

    Edita; Rumasa’u Muhammada Kallamu

  • Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka

    Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka

    Addu’ar Samun Lafiya – An ruwaito daga A’isha (Radiyallahu Anhu), ta ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance idan mara lafiya ya zo wurinsa da koke na rashin lafiya; yakan ɗauko hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa.

    Sannan ya dangwali ƙasa, sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo, sai ya karanta wannan addu’ar samun lafiya; kamar haka:

    “Bismillahir turbati ardina biriqati ba’dina yashfa taqmuna bi’izni rabbina”

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Da Haka Na Gagara wanda Yahaya Ishaq ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya danna nan

  • Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba

    Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba

    Addu’a Ga Cututtuka; Wannan kuma addu’a ce da aka ce a dunga karanta ta a duk lokacin da wata annoba ta shigo.

    Idan har kana karanta wannan addu’ar, Allah zai tsare shi daga ciwon annoba na zamani, wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Duk sanda mutum ya yi sallah ko wani aikin alkhairi, ya dunga karanta wannan addu’a (Addu’a Ga Cututtuka) kamar haka, Allah (Subahanahu Wata’ala) zai kare shi;

    Allahumma inni a’uzhubika minal barasi, wal jununi, wal juzami, wamin sayy’il asqam”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye-nauyen Rayuwar Aure danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya danna nan.

  • Abubuwan Da Ya Kamata A Sani Game Da Ciwon Sanyi

    Abubuwan Da Ya Kamata A Sani Game Da Ciwon Sanyi

    Shi ciwon sanyi wanda Bature ke cewa (S.T.D: Sexual Transmitted Disease) yakan haddasa wa mata matsala daban-daban.

    Kama daga rashin haihuwa, ɗaukewar sha’awa, wasu kuma yakan yi yawa ya taɓa musu ƙoda ya haddasa mata ciwon da Bature yake kira kidney infection; wasu matan kuma ya cire musu sha’awa kwata-kwata.

    Irin wannan matsalar takan iya kama maza su ma, ta haifar musu da wannan matsalolin kamar yadda take haifarwa da mata.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Da Haka Na Gagara wanda Yahaya Ishaq ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Maganin Damuwa danna nan

  • Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Akwai hanyoyi da mace za ta bi domin rabuwa da wannan mugun ciwon.

    Shawarar farko game da wannan ciwon za ta bi; ko da ma ba ki da wannan ciwon in har an kusa auranki tom ki guji tsarki da ruwan sanyi sannan ki rinƙa yawan yanke farcenki kina wanke hannunki; ko da zai kai ki sosa gabanki kin ga datti ba zai shiga ba.

    Ki samu waɗannan haɗin ki rinƙa wanke gabanki da su;

    • Gishiri
    • Ganyen magarya
    • Ganyen lalle
    • Kanunfari

    Waɗannan za ki rinƙa dafa su ki samo flask ki rinƙa kama ruwa da su a kodayaushe. Sannan pant ɗinki ki rinƙa dafa shi da ruwan zafi da gishiri da Dettol kina wankewa ki sanya a rana ya bushe ki goge su, sun zama sababbi kenan.

    Maganin Ciwon Sanyi

    Ki nemo waɗannan itatuwan ki dafa su dan kawar da ciwon sanyi, musamman ki fara yin su two months kafin bikinki. Da yardar Allah kin rabu da ciwon sanyi, in kin gan ki da shi to sai dai a jikin mijinki kika samu. Shi ma namijin zai iya waɗannan haɗin dan ya rabu da shi.

    Ga abubuwan da za a nema kamar haka;

    • Sayen zogale ma’ana saiwarsa
    • Kanunfari
    • Jema
    • Jar kanwa
    • Gogamaso
    • Kaimin ƙadangare ko kuma ciyawar wutsiyar ƙadangare
    • Cini da zuga, wasu na cewa bini da zugu

    Waɗannan su ne za a tafasa su sosai sai sun fita hayyacinsu sai a tace a zuba a kofi; a sa zuma a sha sau biyu a rana. In Sha Allah za a rabu da matsalar sanyi kowanne iri ne.

    Don karanta cikakken bayani akan Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection) danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

  • Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Akan kai wani mataki duk irin kulawar uwa ko kuma kulawar uba ya zamto yaransu ko yarinyarta ta fanɗare.

    Ka ga yaro ya jefa kansa cikin wannan hatsarin rayuwa, yaro ya rinƙa shaye-shaye sakamakon abokai da ya gamu da su.

    Ga matakan da ake bi In Sha Allah zai daina:

    1. Matakin farko raba shi da abokan hurɗarsa a sama masa wajen sana’a.

    2. Mataki na biyu shi ne ana ɗaukan ayoyin sakina na Al ƙur’ani gaba ɗaya da kuma ayatus Sam, a karanta su a tofa a ruwan sama ko na rijiya, sannan a samu za’afaran da ganyen magarya da muski ɗan kaɗan sai a ba shi ya rinƙa sha da safe da kuma dare.

    Sannan za a iya ɗaukan dukkan nau’in kayan mayen da yake sha a haɗa su guri guda; anemo garin kustul hindi cokali uku da kuma man zaitun da man habba da kuma man kwakwa da na tafarnuwa da na’a na’a a haɗa su guri guda da kayan shaye shaye sannan a rufe a bar su su kwana.

    In gari ya waye a girgizasu sosai, sai a tace sannan a ba shi kafin ya ci abinci. Ana so da ya sha ya yi amai. Wannan haɗin ana so a rinƙa ba shi duk bayan sati uku ko kuma wata ɗaya. Sannan a haɗa da wannan ruwan da aka yi tofin ayoyin a ciki. Insha Allah duk abinda yake sha zai fita daga ransa ya dawo cikakken mutum.

    Minhaj 274
    Ayatus Sakina: Minhaj 255

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Haddar Karatu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Manzon Allah danna nan

    Edita@rumasau-kallamu