Ambaton Abin Da Ake Sanin Zuwan Jinin Al’ada Da Shi Da Yankewar Sa

0
400

Da me ake sanin zuwan jinin Al’ada?

Jinin Al’ada – Ana sanin zuwan jinin haila ne da zubowar sa a lokacinsa;

Da kuma abin da yake riga shi wani lokaci na ciwon kai ko ciwon mara.

Kuma da me ake sanin yankewar sa?

Ana sanin yankewar sa da tsabtatar abin da aka toshe shi da shi;

Shi ne tsabtatar abin da mai haila take toshe gabanta da shi na auduga ko yanki don hana zubar jinin ko da zubar wani farin ruwa a ƙarshen jinin a ƙarshen haila shi ne ake kira da ƙassa fara.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Maimaituwar Jinin Haila A Wata Ɗaya danna nan.

Don karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya? danna nan.

labarin da ya wuceMaimaituwar Jinin Haila A Wata Ɗaya
Labarin na GabaBayanin Mafi Yawancin Kwanakin Jinin Biƙi