Hawan Jini Ga Mace Mai Juna

0
18

Hawan jini yayin da mace ke da juna biyu ba lallai bane ya zama wani abu da ke da hatsari a ciki musamman idan aka ba shi kulawan da ya dace.

 Ga abubuwa da ya kamata mace ta sani domin ta kula da kanta da kuma jaririnta. 

Yayin da mace ta san ta na da hawan jini a lokacin da ta ke dauke da juna biyu to ya kamata ta kasance a cikin kula na likitoci / ma aikatan lfy wato (close monitoring) ke nan a Turance.

Ire_iren hawan jini ga mai ciki 

Wani lokacin mace na kancewa ta na da hawan jini kafin ma ace ciki ya shige ta. Wasu lokutan kuma hawan jinin na samuwa ne lokacin da ta rigaya ta yi cikin, wato bayan ta dauki cikin ke nan.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

  1. Gestational hypertension . Mata da ke da irin wannan hawan jini sukan same shi ne bayan sun dauki ciki da sati 20. Ba a samun furutin (protein) fiye da kima a fitsarinsu ko wani alamu na lalacewar wani daga cikin muhimman gabobin jikinsu (organ damage).
  2. Chronic hypertension. Chronic hypertension wato hawan jini ne da ya tsananta wadda kuma yana nan ne a jikin mace kafin ma a ce ta sami juna biyu ko kuma kafin cikinta ya kai sati 20. Sabo da ita cutar hawan jini ba kasafai ta ke nuna alamunta ba, to yana da wuya a san lokacin da cutar ta shigi mutum.
  3. Chronic hypertension with superimposed preeclampsia . Wannan yanayi na faruwa ne ga matan da suke da chronic hypertension kafin shigan ciki wadanda suke fama da tsananin hauhawar jini (worsening high blood pressure) da kuma furutin a fitsarinsu ko kuma wasu matsaloli na daban da hawan jini ke kawo wa a lokacin juna biyu.

_hatsarurukan hawan jini gamai juna2

_yaya zaki gane kinada hawan jini

_matsayin shan maganin hawan jini ga mai juna biyu

_abubuwan da mace mai hawan jini ke bukata wajen likita

_hanyar kariya

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wuceShin Mutum Na Da Buƙatar Gyara Don Zai Aure
Labarin na GabaDamar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata