Ciwon Kai Na Gado Wato [Migraine]

0
27

Wannan na daga cikin cutukan gado da suka fi addabar Mata.  Saide wasu lokutan yakan addabi wasu daga cikin Maza kalilan, amma dai Mata ne suka fi zuwa mana dashi asibiti.

Ciwon kai ne mai tsanani mai zuwa kusan wata-wata kamar al’ada. Yafi kama ɓari daya na kan mutum, kuma Mace zata rika jin alamu kafin yazo wadanda ke nuni da cewa ciwon ya kusa zuwa.

WAƊANNAN ALAMOMIN SUN HADA DA:

– Rashin son haske 

– Rashin son jin ƙarar komi

– Ganin walkiya-walkiya ko dishi-dishi.

– Riƙa jin ƙauri-ƙauri a hanci

– Yawan hamma ko miƙa. 

Sai sauran alamun ciwon sun haɗa da:

– Yawan tashin zuciya, ko amai.

Awasu lokutan kuma ba alamun sai dai kurum aji ciwon kan yazo lokaci guda 

WANI ABU DA IRIN WANNAN CIWON KAN SHINE:

Matsalar bata cika tafiya da magungunan kashe zogi na Panadol ko ibuprofen ba. Dole sai anba mutum magunguna masu karfi matsalar take lafawa musamman rukunin magunguna wadanda ke aiki a kwakwalwa. 

Don haka idan mutum na fama da irin wannan matsanancin ciwon kan dole sai yaje wurin kwararen likita musamman ɓangaren kwakwalwa (neurologist) ya rubuta masa magani mai karfi da kyau wanda ya dace da yanayin mutum. Domin ciwon a wasu yakan faru akai akai ba sau 1 a wata ba. 

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

MEKE HADDASA CIWON

Shi ciwon har yanzu ba’a tantance me yake kawo shi ba, amma andai san yana bin zuri’a wato uwa takan sawa ƴarta Ko ƴaƴan su ɗauka daga uba, ko kakanninsu na ɓangaren uwa da uba. 

Sauran abubuwan da akan danganta da matsalar sune:

– Shan kwayoyin rage haihuwa wato contraceptive pills da samun juna biyu da tsayawar al’ada a Mata idan sun manyanta ko tsayawarta kafin lokacin da ya dace ta tsaya. 

MEKE YAWAN TAYAR DA CIWON

Triggers Ma’ana: Wasu nau’in abubuwa dake yawan sashi tashi.  

– Daga ciki kwai ire-iren  abinci dakan tayar da ciwon wadanda su masu matsalar ya kamata su lura su guje musu saboda suna stimulating din kwakwalwa kamar masu halayyar cin tafarnuwa kullum, shan ruwan kanumfari kullum, shan coffee kullum

– Sai kuma rashin samun isasshen hutu ko bacci, da yawan kallon screen walau na waya ko a Tv. 

– Da yawan toshe kunnuwa da eyafis ko headphones na tsawon lokaci har ya zamo halayyar mutum. 

– Yawan shiga halin matsi, damuwa, da kuma gabatowar haila

– Yawan caccanza lokacin kwanciya bacci.

– Zama da yunwa, aqi cin abinci musamman breakfast sai wajen 10 ko 11 na safe. 

– Ko magungunan shaqawa a hanci, ko amfani da irinsu cocaine.

Duk an tabbatar suna sa saurin tashin ciwon.

ILLAR YIN WATSI DASHI

Likitoci na gargadi akan ya kamata mai ciwon ya rika ziyartar asibiti kada yake shan magungunan rage zogi agida kurum ko kuwa yake barin sa har yaci ya saki, domin MIGRAINE na iya haddasa abunda ake kira MIGRAINOUS INFARCTION

Wato Migraine kan iya haddasa strokes wanda hakan kan jawo shanyewar barin jiki koda mutum baida hawan jini saboda fashewar magunar jinin kwakwalwa da ciwon yasa hakan ya zai haddasa mutuwar kwayoyin halittun kwakwalwa na gurin da abun ya faru. Ko injury a cerebellum mutum ya riƙa tsima ko kyarma a hannu ko ƙafa ko duk wato (Tremor) 

Saboda sanda yake faruwa talewa jijiyoyin jini keyi tare da tsukewa cikin ƙarfi fiye da yadda ya dace, kamar yadda kake hura balloons abunda ake kira (Vaso-dilatation) kaga ba ƙwari in pressure tai yawa hujewa zafin jini zai jijiyar tayi asami matsala domin shi stroke ne hemorrhagic Mesa jini ya fantsama wanda galibi yafi kisa nan take saɓanin ischemic.

Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

WANI ABIN MAMAKI KUMA

Galibi a Mata masu shi in sukai ciki bai fiye tashi ba har sai bayan sun haihu. 

MATAKIN ƊAUKA

Kafin akai ga likita a iya shan paracetamol don asami relief amma kar azauna, saboda inka zauna kaita shan paracetamol tohfa shima zai lalata maka hanta. Cikin kwana 3 rabin hantarka na iya mutuwa. 

Sannan a iya a sami ruwan dumi adaddana sashin kan wato ai tausa, 

A sami guri mara hayaniya a kwanta a kuma kashe hasken dakin musamman in dare ne, mutum ya saki jiki ya samu yai relax. 

Sai kuma a garzaya ga likita in gari ya waye domin samun maganin sassauci. Domin migraine bashi da maganin warkewa kwata-kwata. Saide a sami sauki akuma kiyaye yawan tashin sa.

Idan mutum ya fahimci abinda ke tada masa shi wato triggers toh sai ya kiyaye su.

GA SADAKAR RIGAKAFIN SA

Ga wanda yake taso masa akai akai irin sau biyu a sati ko kusan ko yaushe yaje pharmacy ya nemi VITAMIN B2 (RIBOFLAVIN) 400MG yasai robar guda kullum ya rika shan kwaya 1 tsawon wata 4 zuwa 6 idan Allah ya taimakesa zaiji tsit ya dena yawan tashin. Vitamin B2 bawai B-complex ba…. A kiyaye. 

Allah ya sauwake.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki
Labarin na GabaMatsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya