Falalar Adalci, Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

0
299

Hadisi Na Ɗaya A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Jarir ɗan Abdullahi (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ba ya tausayin mutane, Allah ba zai tausaya masa ba”.

Bukhari da Muslim da Tirmizi ne suka rawaito shi. Ahmad ma ya rawaito shi ya ƙara da cewa: “Wanda ba ya afuwa, Allah ba zai yi masa afuwa ba”.

Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

Hadisi Na Biyu A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Anhuma) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Masu tausayi Allah mai rahama zai tausaya musu. Ku tausayawa na ƙasa da ku, wanda yake sama da ku zai tausaya muku.

Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji mai gaskiya abin gaskatawa mai wannan ɗakin baban Alƙasim (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ba a cire tausayi sai daga zuciyar mara rabo a lahira”.

Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

Hadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ya tare da mu wanda ba ya tausayawa ƙaraminmu, kuma ba ya girmama babbanmu, kuma ba ya umarni da kyakkyawan aiki, ba ya hani ga mummuna.

Tirmizi ne ya rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Waɗannan hadisai guda biyar suna bayyana falalar tausayawa mabiya da jinƙan su da sauran masu rauni da haramcin gallaza musu, suna nuna cewa duk wanda yake da jinƙai da tausayi Allah zai tausaya masa, kuma rashin tausayi alama ce ta rashin imani da rashin rabo a lahira, har ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ruwan sa da maƙetaci mugu maras imani da tausayi da kuma wanda ba ya girmama na gaba da shi” .

Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

Hadisi Na Biyar A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Aliyyu (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Maganar ƙarshe da Manzon (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ita ce: “Ku kula da sallah, ku kula da sallah, ku ji tsoron Allah ku kula da haƙƙoƙin waɗanda suke a ƙarƙashinku”.

Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Wannan hadisi yana daga cikin wasiyyoyin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bar wa al’ummarsa dab da wafatinsa. Ya yi wasiyyar a kula da sallah kuma a kula da haƙƙoƙin bayi da barori; da kuma duk waɗanda suke ƙarƙashin mutum.

Hadisi Na Bakwai A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Ahuma) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa masu adalci za su kasance a kan mimbarai na haske a daman Allah mai rahama; kuma duk hannayensa biyu dama ne. Su ne waɗanda suke yin adalci a cikin hukuncinsu da iyalansu da waɗanda suke jagoranta.

Muslim da Nasa’i ne suka rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Haƙiƙa masu yin adalci da gaskiya a shugabancin da yake kansu da iyalansu suke kaucewa zalunci da nuna bambancin a tsakanin waɗanda suke jagoranta, za su samu babban matsayi a wurin Allah ranar lahira.
Hannun dama da ya zo a wannan hadisin sifa ce daga siffofin Allah Ta’ala waɗanda ake yin imani da su kamar yadda suka zo, ba tare da an yi musu tawali ko canja su, ko kore su ba, ko kuma kamanta su da sifofin halittu ba.

Hadisi Na Takwas Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Iyad bin Himar (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa; “Yan Aljanna guda uku ne: Mai mulki mai adalci mai dacewa da gaskiya; da mutum mai tausayi mai taushin zuciya ga dukkanin ‘yan uwansa da dukkan musulmi da kuma mutum mai iyali, mai kame kai da wadatar zuci.

Muslim ne ya rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Falalar da darajar waɗannan mutane uku ta sanya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya taƙaice ‘yan Aljanna a kansu. Saboda duk wani wanda yake riƙe da wani jagoranci tun daga mai gida da uwargida har zuwa kan shugaban ƙasa ya yi ƙoƙari ya yi adalci ya nemi gaskiya kuma ya yi aiki da ita.

Kowa ya fitar da mugunta da ƙeta da gaba da ganin ƙyashi daga zuciyarsa, mu kasance masu tausayi da taimako da ƙauna ga dukkan ‘yan uwanmu da gabaki ɗayan musulmi.

Kowa ya zage damtse ya nemi halal ya kula da iyalansa kuma ya wadatu da abin da Allah ya ba shi ya kasance mai godiya ga Allah ya rinƙa hangen na ƙasa da shi, kada ya rinƙa hangen na sama da shi.
Waɗannan halaye za su sa mu cancanci shiga Aljannah, kishiyoyinsu kuwa, babu abin da za su jawo mana sai shiga wuta tun daga duniya kafin ta lahira.

Hadisi Na Tara A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Allah Ta’ala yana ƙin mutane huɗu: Ɗan kasuwa mai yawan rantsuwa, da talaka mai girman kai, da tsoho mazinaci da kuma azzalumin shugaba.

Nasa’i da Ibn Hibban ne suka rawaito shi; Muslim ma ya rawaito makamancinsa, sai dai a ruwayarsa ya ce; “Da talaka mai girman kai da shugaba maƙaryaci”.

Hadisi Na Goma A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Mu’awiyya (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba za a tsarkake al’ummar da ba hukuncin gaskiya a cikinta ba, kuma mai rauni ba ya iya karɓar haƙƙinsa daga mai ƙarfi cikin daɗin rai”.
Ɗabarani ne ya ruwaito shi.

Ƙarin Bayani

Wannan hadisin Ibn Majah ma ya rawaito shi tare da wata ƙissa mai ban sha’awa kamar haka:

“Wani baƙauye ya zo wurin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) domin karɓar bashin da yake bin sa. Ya matsa masa har ya ce: “Ba makawa sai ka biya ni bashina”. Sannan sahabbai suka daka masa tsawa suka ce: “Kasan da wa kake magana kuwa? Sannan ya kada baki ya ce: “To ba haƙƙi nake nema ba? Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da su: “Don me ba za ku goyi bayansa ba?

Sannan ya aika wajen Khaulatu ‘yar Ƙaisu ya ce da ita: “Idan kina da dabino ki ba ni rance, kafin a kawo mana dabino mu biya ki”. Sannan ta ce: “An gama ya Ma’aikin Allah, uwata da ubana su zama fansa a gare ka”. Sai ta ba shi ya biya baƙauyen, har ya ba shi wani ya ci, ya ji daɗi, ya ce ka cika min Allah ya cika maka.

Sai ya ce: “Ai waɗannan (masu cika wa mutane haƙƙoƙinsu) su ne zaɓaɓɓun mutane, haƙiƙa ba a tsarkake al’ummar da mai rauni ba ya samun haƙƙinsa cikin sauƙi daga mai ƙarfi”.

Allahu Akbar! Ɗan’ uwa yi nazari kan wannan ƙissa dubi matsayin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) dubi kuma wane ne wannan Baƙauyen? Sannan ka dubi abin da ya faru tsakaninsu da kuma abin da ma’aikin Allah ya faɗa, lallai za ka fahimci darussa masu yawa.

Duk al’ummar da ake rayuwar kashin dankali a cikinta, ake rayuwa irin ta rabon kura; rayuwar da uwa ba kwaɓa, uba ba harara, sai dai kowa ƙarfinsa ya ƙwace shi; maras ƙarfi kuwa sai dai ya yi Allah ya isa, to haƙiƙa wannan al’umma ko ƙasa ko gwamnati ba za ta yi wata daraja da mutunci da kwarjini ba, ballantana ta samu wani tsarki da yabo a wurin Allah da kuma mutane. Wannan zai gaggauta rushewar wannan al’umma da ci bayanta. Auna rayuwarmu a yau da wannan hadisi anya ba mu shiga cikinsa ba kuwa?

Hadisi Na Goma Sha Ɗaya A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abu Buraida daga mahaifinsa haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Alƙalai iri uku ne: alƙalai biyu ‘yan wuta ne, alƙali ɗaya ɗan Aljanna ne. Alƙalin da ya yi hukunci ba na gaskiya ba, yana sane wannan ɗan wuta ne. Kuma Alƙalin da ba shi da ilmi ya yi hukunci ya halaka haƙƙoƙin mutane shi ma ɗan wuta ne. Alƙalin da ya yi hukunci na gaskiya wannan ɗan Aljanna ne.
Abu Dawud da Tirmiz da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Wannan hadisin yana bayanin matsayin alƙalai a lahira. Duk alƙalin da ya yi zalunci saboda son rai ko wata buƙata ko rashawa da aka ba shi, da kuma alƙalin da bai nuna ba, ba shi da ilmin cancantar alƙalanci aka yi abin da aka yi aka ba shi alƙalanci ya zo yana taɓargaza, waɗannan biyun ‘yan wuta ne.
Shi kuma alƙalin da ya cancanta kuma yana adalci da gaskiya wannan ɗan Aljanna ne.
Saboda haka alƙalai su ji tsoron Allah, su yi gaskiya da adalci, su kasance cikin karatu da bincike a kowane lokaci. Su ma masa na da alƙalai su ji tsoron Allah su rinƙa naɗa waɗanda suka cancanta su guji naɗa jiƙaƙƙun mutane don kawai sanayya ko rashawa da sauransu.

Hadisi Na Goma Sha Biyu Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Ibn Abi Aufa (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah yana tare da alƙali matuƙar bai yi zalunci ba, idan kuwa ya yi zalunci sai Allah ya rabu da shi sai shaiɗan ya naniƙe masa.
Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi. Sai dai a ruwayar Hakim ya ce: “idan ya yi zalunci sai Allah ya yi watsi da shi”.

Ahmad da Bazzar da Tabarani ne suka rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Allah Ta’ala yana taimaka wa shugabanni da alƙalai masu adalci yana ba su kariya; yana rufa musu asiri ya ɗaukaka su matuƙar sun kama hanyar zalunci da rashin gaskiya; sai Allah ya yi watsi da su ya bar su da dabararsu, su yi ta ɗimuwa da shirme, ga rashin ƙima a idon mutane; sannan in suka tafi a haka, a lahira su haɗu da matsananciyar azaba.

Hadisi Na Goma Sha Uku Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Duk wanda ya shugabanci mutane goma za a kawo shi ranar ƙiyama a ƙuƙume (ɗaure) kodai adalcinsa ya kwance shi ko kuma zalunci ya halakar da shi.

Ahmad da Bazzar da Tabarani ne suka rawaito shi.

Ƙarin Bayani

Lallai wannan hadisin tsoratarwa ne mai girma ga shugabanni da masu neman shugabanci. Babban abin tsoron shi ne; hadisin bai taƙaita a kan shugaban ƙasa ko gwamna ko sarki ba, a’a duk wanda ya yi shugabanci daga mutane goma zuwa sama, to za a zo da shi a ɗaɗɗaure ranar ƙiyama cikin kukumi wato za a haɗe hannayensa a kan wuyansa a ɗaure. A haka za a yi masa hisabi in ya yi adalci a kwance shi; in bai yi adalci ba a hakan za a nutsa shi a wuta. Allah ya kiyaye mu Ameen.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci); wanda Shehu Mansur Dala ya waallafa shi. Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Mazajen Da Nana Khadija Ta Aura Kafin Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

labarin da ya wuceHadisai A Kan Kada A Goyi Bayan Mai Laifi
Labarin na GabaAddu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai