An karɓo daga Anas Ibn Malik (Radiyallahu anhu) ya ce:
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Ku yi Sahur saboda akwai albarka a cikin sahur”. (Bukhari 1823, Mualim 1095), An karɓo daga Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah Ta’ala da Mala’iku suna yin salati ga masu yin Sahur”.(Tabrani da Ibn Hibban/ Sahihul Targib; 1098).
Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.