Nauye-nauyen Rayuwar Aure

0
776

A musulunce, rayuwar aure bata kyautatuwa ta zama nagartacciya har sai idan an aiwatar da ita ta salon da Musulunci ya tsara, ta hanyar ɗa ma’aurata  orawa wasu nauye-nauye da ake buƙatarsu dasu sauke su kamar haka:

1. Haƙƙoƙin mace akan mijinta.
2. Haƙƙoƙin miji akan matarsa.
3. Haƙƙoƙin da miji da mata suke tarayya a kansu.
4. Haƙƙin wanda mutuwa ta raba shi da abokin zamansa daga cikin ma’aurata.

1. Haƙƙoƙin Mace a Kan Mijinta:
(a) Sadaki:
Wanda bayaninsa ya riga ya gabata.
(b) Ɗora iyali akan bin Allah tare da rainonta da kyawawan ɗabi’u:
Shi wannan haƙƙi na biyu da samuwarsa da kuma ɗorewarsa ne mace zata kyautata tsakaninta da ubangijinta, da kuma tsakaninta da bayisa.
Da farko Allah Mai girma da Buwaya yace:
” ka ambaci (labarin) Isma’il cikin wannan littafi (Alƙur’ani), haƙiƙa shi mai cika alƙawari ne, kuma Annabi ne Manzo. Ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsaida sallah da kuma ba da zakka, sannan kuma shi yardajje ne a wajen ubangijinsa ).
Abin nufi a nan, Annabi Isma’il yardajjen Allah, a zamansa da iyalinsa yana umartar su ne da su riƙa tsayar da sallah, kuma su riƙa bayar da zakka, domin alaƙarsu da Ubangiji ta kyautata.
Sannan kuma munji cewa shi mutum ne mai cika alƙawari, sanin kowa ne kuma duk wanda yake haka zaka tarar yana ƙoƙarin rainon iyalinsa da yin haka.
Sannan kuma Allah ya ce da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi):
“ka umarci iyalinka da tsaida Sallah kai ma kuma kayi haƙurin dawwama akan tsaida ita, ba zamu tambaye ka dukiya ba, mune ma zamu azurta ka, kuma kyakkyawan ƙarshe (duniya da lahira ) ga masu tsoron Allah yake”.
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya aiwatar da wannan umarni da Allah yayi masa kamar yadda Imamut- Tirmizi ya rawaito hadisi cewa, an karɓo daga Ummu- salama Allah ya yarda da ita tace: ya rage kwana goma ya ƙare, baya barin ko da mutum ɗaya daga cikin mutanen gidansa matu ” Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya kasance idan watan Ramadankar dai zai iya yin sallar dare face sai ya tashe shi (domin ya yi)”.

To, ‘yan uwa, idan Annabi bai bar sallar nafila ta wuce mutanen gidansa ba; ina kuma ga sallar farilla.
Sannan kuma Allah Maɗaukaki yace: “yaku waɗanda kuka bada gaskiya, ku tserar da kanku da kuma iyalanku (daga shiga ) wuta (wadda ) mutane da duwatsune makamashinta, kuma akwai wasu karfafan mala’iku masu kauri da suke tsaron ta, waɗanda basa saɓawa Allah abin daya umarcesu da shi, kuma suna aikata duk abin da aka umarce su da shi”.
A wannan ayar kuma kiran muminai gaba ɗaya Allah ya yi, sannan ya umarce su dasu dage su bi irin turbar da Annabawa suka bi, wajen ɗora kansu da iyalansu akan hanyar bin Allah da nisantar saɓa masa, domin su gudu tare su kuma tsira tare.
Har wa yau, Bukhari ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Malik ɗan Huwairis Allah ya yarda da shi yace: Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace da (ayarin) jama’ar Abdul- Kais da suka zo wajen “su kiyaye imaninsu da kuma ilimin ɗaya sanar dasu shi, sannan kuma yace dasu, “ku koma wajen iyalanku ku sanar da su”.
Saboda waɗannan dalilan da muka ji ya zama lallai akan miji ya sanar da matarsa ilimin yadda zata bautawa ubangijinta, ko kuma ya turata inda zataje ta koya, kamar yadda matan sahabbai suke zuwa wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) su koyo addini.
Bayan haka, an karɓo daga Amru ɗan Ahwas Allah ya yarda da shi yace, ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) a hajjinsa ta bankwana yana cewa: “ku saurara, kuyiwa mata wasici da alheri”. ( Tirmizi ne ya rawaito shi ).
Haka kuma an karɓo daga Aisha (Allah ya yarda ita ) ta ce: ” (wata rana ) Yahudawa sun zo wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) sai suka ce dashi: “Assamu alaikum” wato halaka ta tabbata akanku, a maimakon su ce: “Assalamu alaikum” wato amincin ya tabbata agare ku, jin haka, sai Aisha ta ce: Halaka akanku, Allah kuma ya tsine muku; yayi fushi daku. Sai Annabi yace da ita: ‘A’a Aisha, yi a hankali, ina umartarki da yin sauƙi, kuma ki kiyayi kausasawa da munanan maganganu. Sai kuwa tace da Annabi baka ji abin da sukace ba ne? Annabi yace: To ke bakiji abin dana ce dasu ba? Ai na mayar musu da martani da cewa a kansu dai. Sai Allah ya amsa mini addu’ar dana yi musu, su kuma ba zai amsa musu wadda suka yi mini ba. (Bukhari ya rawaito shi).
A nan idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa, waɗannan hadisai suna ɗora magidanta ne akan hanyar daya kamata su ɗora matansu akai, ta nusar dasu yadda ya kamata su zauna da mutane a cuɗanyarsu dasu. Allah dai yaba mu ikon kulawa da kuma aiki da wannan koyarwar ta Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi), amin.

(c) Samawa Mace Mazauni (Gida ko ɗaki):

Shi kuma wannan nauyi ya hau kan miji ne a sakamakon faɗar Allah Madaukaki daya ce:
“ku zaunar dasu (mata) a inda kuke zaune daidai halinku, kada ku cuce su don ku ƙuntata musu”.
Da kuma faɗar Allah Maɗaukaki cewa: ” kuji tsoron Allah Ubangijinku kada ku fitar dasu daga dakunansu, suma kada su fita, sai dai idan sun zo da mummunan aiki mabayyani, waɗancan iyakokin Allah ne, to haƙiƙa ya cuci kansa”.
Saboda haka, haramun ne mai gida yace da matarsa ta fice tabar masa gidansa,ko ɗakinta don ya saketa, matuƙar dai bata gama idda ba. Haka kuma itama mace bai halatta ta bar gidan mijinta ba don ya sake ta har sai bayan ta gama idda. Wannan sai ya tabbatar mana da cewa aihakin miji ne ya tanadar wa matarsa mazauni.

(d) Ciyarwa da Tufatarwa:

Haka ma ciyarwa da tufatarwa, hakki ne da mace take da shi akan mijinta. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki yace:
” ciyar da mata da tufatar dasu gwargwadon iko, wajibi ne akan wanda aka haifawa da, ba a ɗorawa (kowanne) rai sai gwargwadon ikonsa”. A wata ayar kuma Allah Maɗaukaki yace: ” Mai yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuma aka ƙuntata arzikinsa, (wato talaka), to, ya ciyar daga ɗan abinda Allah yaba shi, Allah baya ɗorawa kowacce rai sai abinda ya bata, da sannu Allah zai sanya sauƙi bayan matsi (tsanani)”.
A hadisance kuwa, an karɓo daga Hakim ɗan Mu’awiya daga babansa (Allah ya yarda da shi) yace: ” Na tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) cewa, menene haƙƙin matar kowannenmu akansa? Sai yace: ” Ka ciyar da ita idan kaci, ka kuma tufatar da ita idan ka tufata…”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi).
Sannan kuma sahabin Annabi Amru ɗan Ahwas ( Allah ya yarda da shi ) yace: Haƙiƙa yaji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) a hajjinsa ta bankwana yana cewa: ” ku saurara, hakika matanku nada haƙƙi a kanku, haƙƙinsu a kanku ku kyautata tufatar dasu, da ciyar dasu”.( Tirmizi ne ya rawaito).
Bisa dogaro da waɗannan dalilai, ya zama tilas akan miji ya ciyar da matarsa, ya tufatar ita gwargwadon irin halin da yake da shi.
Sannan kuma amana ce a wuyan miji ya ciyar da matarsa da halal bada haram ba.
Haɗarin Kuntatawa Iyali Wajen Ciyarwa
Musulmin da Allah yayi masa yalwar abin da zai ciyar da iyalinsa, da abin da zai tufatar dasu,amma sai ya zama yana ƙuntatamusu, ta hanyar ƙin wadata su da abin da zai ishe su, to, a zahirin gaskiya babu wanda yake cuta sai kansa, domin kuwa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “ya ishi mutumlaifi, ya rika tozarta wanda yake ci a ƙarƙashinsa”. (Abu Dawuda ne ya rawaito shi).
Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) yace: Haƙiƙa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) Yace: “Babu ranar da bayi zasu wayi gari a cikinta face sai wasu mala’iku biyu sun sauko, sai ɗaya daga cikinsu ya kama cewa: “Ya Allah ka bai wa mai ciyarwa”. Sai shi kuma ɗayan yace: “Ya Allah ka haɗa matsolo da asara”. (Bukhari da Muslimu ne suka rawaito shi). Don haka, ‘yan uwa sai ayi hattara.
Bayan haka, da Allah zai datar da iyalan malam matsolo da samun wata kafa dazasu riƙa ɗiban abin da zai ishesu daga cikin dukiyarsa, a shari’ance, basuyi laifi ba in sun ɗebi abin da zai ishesu, matuƙar dai baza suyi ɓarna ba.
An karbo daga Aisha (Allah ya yarda da ita) tace: “Hindu ‘yar Utba matar Abi Sufyanu ta shiga wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) sai tace: ” Ya manzon Allah mijina Abu Sufyan matsolo mutum ne, baya bani abin ciyarwa da zai isheni, kuma ya ishi ‘ya’yana, sai in na ɗebi wani abu daga cikin kudinsa bada saninsaba, shin ko ina da laifi game da hakan da nake yi? Sai Annabi yace: “kici gaba da ɗaukar abin da zai ishe ki ya ishi ‘ya’yanku daga kuɗinsa”. Wato yin hakan ba laifi bane. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).
Sannan dai ita wannan ta’ada ta matsolanci, haɗarinta yana da yawan gaske, domin kuwa tana sa mai yinta ya rasa samun alherin da masu ɗaukar abin hannunsu su bayar suke samu:
Na Farko: zai rasa samun addu’ar alherin da mala’ika yake yi wa masu ɗaukar abin hannunsu su bayar duk wayewar garin Allah, kamar yadda mukaji.
Na Biyu: Ya rasa kwarjinin da masu bayar da abin hannunsu suke samu a wajen waɗanda suke agazawa.
Na Uku: An karɓo daga Abu Huraira (Allah yayarda da shi) yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Hannun da yake bayarwa yafi hannun da yake karɓa. (In zaka bayar) ka fara da wanda nauyinsa ke kanka, kaba wa babarka, da babanka, da ‘yan uwanka, sannan wanda yafi kusa da kai, sai wanda yake da kusanci da kai”. (Nasa’i da Darakudni ne suka rawaito shi, kuma Darakudni da ibn Hibban suka inganta shi).

Domin karanta cikakken bayani akan Dokokin Suturar Musulma danna nan

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHaƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata
Labarin na GabaNasiha Tsakanin Musulmi