Yadda Za Ka Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka

0
1074

Kowanne namiji yana tsananin son ya zama shi ne yake burge matarsa.

Domin haka ne zai sa ya taka Babban Matsayi, Ta zama dukkan ƙoƙarinta da tunaninta shi ne faranta wa mijin nata, yi ma ka biyayya da yabawa hidimarka, Sai dai hakan zai kasance ne, Muddin ka dage kana ƙoƙari kan kulawa da ita.

Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka
Burge Matarka Ta Zama Masoyiyarka
HANYOYIN DA ZA KA BIRGE MATARKA SU NE :

1 – MATSAYI: Ka zama ka ba wa matarka matsayi mai girma. Ka dinga jaddada matsayin. FaÉ—a mata da nunawa a aikace mutuwa ce kaÉ—ai za ta raba ku. Ko ka ce: komai yawan matana, Wallahi ba ni da tamkar ki. Duk abin da na samu , ke nake fara tunani.
Kuma ba za ka bari wani ya wulaƙanta ta ba, ko da ƙannenka ne .

2 – KALMOMI SOYAYYA:

Ka shirya waɗansu Kalmomi na irin soyayya da kake mata. A koda yaushe Mace na buƙatar kulawa da soyayya.

3 – GIRMAMAWA:

Ka girmama dukkan mu’amalarka da ita. Ban da zaginta, wulaÆ™anta iyayenta , ko da ‘yan uwanta. Kar ka jefe ta da kaya: kana nufin ba ta kayan. Kar ka zage ta, komai yadda ta É“ata maka rai kuwa.

4 – FITA:

Ka fita tare da ita wajen cin abinci, gidan zoo , wajen wasanni . Domin ku É—an É—ebe wa juna kewa. Ku ci wani abin, ku yi hira. Wannan irin fita na burge mata sosai. Ya zama ko da sau É—aya ne a wata biyu.

5 – MAGANCE MATSALARTA:

Yin ƙoƙari ka magance matsalar da take ta kokawa. Wato ka lura sosai ka ga tai ta faɗar abu: Ba ka ga kwalliyata ba? Kai kullum ba za ka dawo ba sai can dare?
Ina son in dinga ma kwalliya, amma É—inkinka daga sallah sai wata sallah(Eid).

6 – KULAWA DA HAƘƘOƘINTA: Ka zama ka tsaya sosai wajen abinci, lafiya, tarbiyya yara, kuÉ—in makarantarsu, gamsar da ita a shimfida, Kar ka dinga barinta da sha’awa.

7 – SUMBA: Ka yawaita rungumarta da sumbatar matarka. Lokaci zuwa lokaci ba wai sai za ku haÉ—a shimfida ba.

A takaice idan kana waɗannan abubuwa. Matarka za ta amince ta yarda da kai mijinta ne. Ta ji sonka ya lulluɓe ta, kana burge ta sosai. Sai kuma ka ga ita ma tana himma wajen sallama wa mijinta.

LITATTAFAI Da aka duba:
Fiqh of love
Shaikh Yaser Birjas