Zinariyar Awa Ga Jariran Mu

0
38

Zinariyar awar ita ce awa ɗaya ta farko a duniya ga jarirai bayan an haifo su wato “Golden hour” a turance, a nan ake tantance yanayin lafiya ko nakasa jikin jariri in ya zo da ita, wacce a da sam ba a iya gani ba sanda yake a cikin mahaifa.

Wannan awa guda ɗin ta farkon rayuwa duk matsalar da jariri ya zo da ita aka yi sakaci ba a iya gano ta ko an yi wani abu ba a cikinta to akwai yiwuwar kaso 99% cikin 100% na mutuwarsa, shi yasa aka kira ta da golden hour saboda muhimmancinta.

Ita awar na farawa ne da zarar kan jariri ya ɓullo duniya ko da sauran jikinsa bai kai ga ƙarasa fitowa ba. Hakan ke ba wa jami’an lafiya damar nazartar abubuwan da ka iya faruwa ga jariri masu yawan gaske kamar yadda na faɗa a baya.

A wannan lokacin za a lura da:-

– Ta yaya ma ya doso duniya,  a gicciye ko karkace?
– Kalar jikinsa walau ya zo a jansa wato pink color ko kuwa abinda ba a so wata bulu “bluish color,
– Yanayin kalar ruwan haihuwan da ya fito ciki walau clear kamar dafaffen zaƙi, ruwan ɗorawa (da ke nuna ya yi kashi a ciki wajen fitowa akwai yiwuwar ya sha ko ya shaƙa), ko kuwa kalar kore da ke nuna ya jima da kashi a ciki har ya galabaita.

– Haka yanayin ƙwallon ƙoƙon kansa
– Yanayin sautinsa
– Yanayin bugawar zuciyarsa,
– Yanayin numfashinsa,
– Yanayin ƙwarin jikinsa,
– Yanayin gaɓoɓin hannunsa,
– Yanayin yadda yake maido da martani in an taɓa wasu sassa na jikinsa da
– Kuma duk sauran jikinsa walau akwai nakasa a halittarsa ko babu.

Domin wasu kan zo cikin kashi, wasu ba hanyar numfashi, wasu da lanƙwasassar ƙafa, wasu da al’aura biyu ta mace da namiji, ko ta mata duk biyun, ko namiji duk biyun, ko babu dubura, ko ba hanyar fitsari, ko hanyar fitsari a toshe, ko ta ƙasa ko sama maimakon straight ta kan, ko kumburarren kai in an yi doguwar naƙuda saboda kaucewa jaundice.

Toh sai dai maƙasudin rubutun shi ne domin yin bayani game da muhimmancin wani abu ƙanƙani amma me matuƙar tasiri a jika. Wato RUNGUME JARIRI ko JARIRIYA ga uwa ba tare da shinge a tsakani ba, wato dai skin to skin contact.

Galibi ga wanda suka haihu a asibiti ko ɗaliban ilimin lafiyar da ke zuwa asibiti ko kallon video clips na naƙuda zuwa haihuwa, Ko C/S ba za ku rasa ganin yadda nan da nan da an haifo ko an ciro jaririn ake sa tissue kurum a goge jikinsa a ɗora shi jikin uwa ta rungume shi ko a saita shi ya kama nono ba. wani lokacin ma ko goge jaririn za ku ga ba a yi da ruwan haihuwar da komi a jikinsa za a ɗora shi jikin uwar.

Hakan shi muke kira da “Skin-to-skin contact” ko “kangaroo mother method” wannan abin na da matuƙar muhimmanci ko da a gida aka haihu ya dace unguwoyin zoma suke aikatawa saboda amfanin sa.

Domin kai tsaye in yaro ya hau jikinta yanayin sanyi da zafin jikinsa zai saitu, idan ya kama nono ko ya kama jikin uwar za ta zamo stimulated har cikin ƙwaƙwalwarta, wannan kama nonon zai sa mahaifarta (uterus) da jaririn ya fito ta harba (contracting) wannan harbawar ce matakin farko wajen taimakawa domin tsayawar jinin haihuwa, wanda galibin matan dakan mutu bayan haihuwa dalilin zubar jini wannan rashin harbawar mahaifa ne kan gaba da kaso tamanin 80% wajen jawo mummunan zubar jinin da matan kan mutu bayan ana murnar sun haihu lafiya da, (Uterine atony).

Dukkan bincike da nazarin masana a duniyar likitanci ya yi nuni tare da tabbatar da muhimmancin skin to skin ga jaririn tare da uwar baki ɗaya. Ɗora jariri jikin uwa fata na gogar fata ba tare da riga ko zani ya yi shamaki tsakani ba hakan na haɓɓaka ƙwaƙwalwar jariri nan da nan, tare da farkar da ita domin ta karɓi aikinta cewa an zo duniya kuma yanzu.

Wadda wannan farkowar ce ke nusar da shi cewa akwai buƙatar ya buɗe baki don numfashi da kansa tare da shirin shan nono ko ya sami ruwa da kuzari a jika, domin an yanke waccan hanyar da yake samun abinci a huce, wato an yanke cibiyarsa tunda ta nan yake samun abinci da ba tare da sai ya buɗe baki ya wahala ba.

Shi jariri in ya shigo duniya bakinsa ke fara amfani kafin ma ya kai ga buɗe ido ya ga a ina yake. Shi yasa ana ɗorashin za ku ga ba abinda yake fara yi sai buɗe baki, ko ido bai buɗewa sai ya fara da buɗe baki, wanda hakan shi ke nuna ya iso lafiya.

Amma a ce jariri ya zo ba ya kuka akwai matsala, shi yasa sai an ɗan bugi bayan sa domin ya koka, in ko duk da haka yaƙi kuka to akwai matsala gagaruma. Saboda ta kukan ne kurum huhunsa zai fara aikin da zai ba shi damar iya shaƙar iska ya yi numfashi da kansa.

Toh bayan buɗe bakin a matakin farko to abu na biyu da jariri ke yi shi ne buɗe idanuwa. Buɗe idon nan da zai abinda zai fara arba da shi shi ne fuska ko jikin mahaifiyar sa. Wanda wannan shi zai jawo shaƙuwa da jinta cikin ransa.

Toh daga sauran alfanun ɗora shi jikinsa shi ne sanya jikinsa fara aiki babu kama hannun yaro wajen:

✍- Ɗumama jikinsa tare da saisaita ɗumin jiki don samun nutsuwa.

✍- Taƙaita yawan koke-koke, hakan na sa jariri ya zamo mara fitina.

✍- Taimakawa jikinsa wajen amfana da sinadaran nutrients ɗin da ya haɗiya a nono

✍- Sa wa a ji sannu a hankali jariri na cigaba da ƙara nauyi.

✍- Saisaita ƙarfin tafiyar jini a jikinsa tare da saita bugun zuciyarsa cikin aminci, gami da ba shi dama shaƙar iska wadatacciya zuwa cikin huhu da jininsa.

✍- Haɓɓaka kwakwalwa tare da ƙulla alaƙa mai ƙarfi da uwa.

✍- Yana sa yaro samun isasshen bacci me nauyi cikin nutsuwa.

✍- Uwa uba tare da ƙarfafa masa garkuwar jiki.

Wannan duk za su cigaba da faruwa in kina rungume shi har tsawon watanni 3 a duniya in dai za ki dinga yi masa hakan a kai a kai. Idan kuma bakwaini ne a yi ta masa skin to skin har ya kai tsawon watanni 6 a duniya.

AMFANIN RUNGUMAR GA UWA KUMA SHI NE:

1- Kamar yadda na faɗa a baya idan daga haihuwa ne aka yi hakan to yana ba da kariya daga matsalar zubar jini bayan haihuwa (postpartum bleeding). Wato ɗaya daga abinda ke kashe mu ta dalilin haihuwa.

2- Hakan na sanya wa uwa ƙwarin guiwa da shauƙin son shayarwa, domin da wuya ka sami uwar da ke ɗora jaririn a fatar jikinta na gudun shayarwa ko tunanin zubewar nono.

3- Hakan na haɓɓaka yawan ruwan nono, ya zamto yana tsatstsafowa a kai-a kai.

4- Ya kan magance cutar damuwa da kan sami wasu matan bayan haihuwa musamman masu haihuwar farko, da wasu za a ga haka kurum ma kuka suke bayan ko tun kafin haihuwa, tare da jin tsoron jariran ko wurgi da su, ko ƙin ba su nono.

DON HAKA SKIN TO SKIN CONTACT

Abu ne ƙanƙani kamar wasa amma sai tarin muhimmanci. Kuma ba iya sanda aka haihu ba ne kurum a a lokaci-lokaci kike haɗa jikinki da nasa kina rungume shi in ya so ki sa abin rufa ki rufe kanku baki ɗaya amma fatar sa kan taki, haɗa jikinki da nasa babu tufafi ya fi duk wasu kayan sanyi da za ki sa masa ki murginar a gado.

Har kai uba ka dinga yi wa babynka haka zai amfana amma dai jikinka ya zamto a tsaftace ba bayan ka yi zufa ka bushe ba.

Don karanta Haifo Jarirai Cikin Rigar Sac danna nan

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceHani Akan Yin Gaba
Labarin na GabaAbubuwan Da Ke Haddasa Yawan Zubewar Juna Biyu