Maganin Farin Jini

0
35

Mutane sukan bi hanyoyi daban-daban don samun farin jini da muhibba a cikin al’umma, Ka da ma mata su sami labari. To shin bayan rubuce-rubucen sha da layu da sauran su, akwai waɗansu abububwa a aikace waɗanda za su iya sanya mutum ya sami farin jini? 

Amsa a nan ita ce, eh, kwarai kuwa, karanta waɗannan ƙa’idoji, ka yi aiki da su, ka ga irin farin jinin da za ka samu: 

  1. Ka ɗauki kowane mutum da muhimmanci, ka girmama shi, ka nuna damuwarka ga abin da ya dame shi, ka yi murna ga abin da yake yin imani da shi, ka mutuntá ra’ayinsa. 
  2. Ka saki fuska ga mutane, ka da ka zama mai fuskar shanu. 
  3. Yi ƙoƙari ka san sunan da matum ya fi so ka rinƙa kiran sa da shi. Yana daga shirme kana hulɗa da mutum amma ba ka san sunansa ba,sai dai malam ko alhaji ko ustaz. Kada ka katse wa mutum hanzari lokacin da yake magana. Ka saurare shi cikin haƙuri da nuna muhimmanci ga abin da yake faɗa. 
  4. Ka da ka faɗi abin da zai ɓata wa abokin maganarka rai. Faɗa masa kalmomi na alkhairi masu kwantar da hankali da faranta rai. 

5. Ka yaba wa mutum kan abu na gaskiya da ya yi ko ya faɗa. Amma ka da ka zaƙe cikin yabo, yadda har za ka faɗi abin da ba haka ba. Ya kai/ke mai karatu ka fara gwada wannan maganin farin jinin daga yau ka ga abin mamaki.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceYin Afuwa Da Kyautatawa Wanda Ya Ɓata Maka
Labarin na GabaMaganin Mallaka