Ciwon Zuciya

0
14

Ciwon Zuciya: Na nufin gazawar zuciyar wajen aika jini ga sassan jiki kamar yadda sassan jikin ke buƙata,ciwon zuciya kan iya samo asali daga hawan jinin da ba a bashi kulawar da ta kamata ba.

Abubuwan Dake Saka Mutum Ya Kamu Da Wannan Matsalar 
 • Kibar data wuce kima
 • Hawan jini
 • Shan giya
 • Gadon ciwonzuciya
 • Cin abinci marar tsafta
Alamomin Da Zakaji Bayan Ka Kamu Da Ciwon

Numfashin Dake Bayar Da Sauti

 • Saurin gajiya
 • Daukewar jin yunwa
 • Kumburin fuska da kafafu 
 • Wahalar shakar numfashi yayin kwanciyar rufe da ciki
 • Faduwar gaba ko saurin bugawar zuciya

Numfashi Sama-Sama

 • Kake jin kan ka tamkar ba nauyi
 • Rashin jurewa motsa jiki
 • Tari; matsakaici ko mai tsanani

Domin gujewa kamuwa da wannan ciwo sai mutum ya guji wadancen abubuwan dana lissafa a  sama wadanda ke haddasa ciwon sannan da zarar mutum yaji yanajin wadannan alamomin saiya hanzarta zuwa asibiti domin yaga likita

Domin karanta bayani akan abubuwan dake haddasawa mace ganin ruwa clear ko ruwan nono na zuba daga nonuwanta ko saurin inzali (premature ejaculation)

Domin karanta Ƙarancin Bacci (Sleep Deprivation) Danna nan

labarin da ya wuceƘarancin Bacci (Sleep Deprivation)
Labarin na GabaAbubuwan Dake Haddasawa Mace Ganin Ruwa Clear Ko Ruwan Nono Na Zuba Daga Nonuwanta