Abubuwan Dake Haddasawa Mace Ganin Ruwa Clear Ko Ruwan Nono Na Zuba Daga Nonuwanta

0
52
  • Yawan shafawa ko tattaɓa nono,ko kuma ya zamto me gida na yawan wasa dasu ko sanyasu a baki.
  • Ko kuwa sanya rigar nono mai santsi da zai zamto ita da kanta tamkar tana yiwa mace waiwayi
  • Ko shan magungunan ulcer da ƙwarnafi musamman wanda ake kira da CIMETIDINE.
  • Ko Macen da aka dorata akan maganin hawan jini me suna methyldopa ko aldomet,da wacce ke shan magungunan damuwa wato depression ko rangwamen hankali antipsychotics.
  • Da wacce ke haɗiyar ƙwayoyi ko shan garin hulba,ko shafa mata din jikin nono,ko riƙa yin massage da ruwanta wato fanugreek.
  • Ko macen dake amfani da maganin bada tazarar haihuwa na sha ta baki wato oral pills,ko wacce ta hadu da larurar data shafi lakar gadon baya spinal cord 
  • Ko macen da aka taɓa yiwa aiki a nono,ko me larurar ƙoda.
  • Ko macen da haila ke rikece mata tare da fuskantar canzawar gani zuwa dususu lokaci-lokaci gami da ciwon kai,ko harma da rashin samun juna biyu in me aure ce….wanda kan faru a sakamakon wani ƙaramin ƙari da ya fito a wani sashi na cikin ƙwaƙwalwarta da ake kira firolaktinoma da batasan dashi ba……..

Duk wadancan ababen dana lissafa a sama na iya haddasawa mace ganin ruwa clear ko ruwan nono na zuba daga nonuwanta walau guda ɗaya ko duk biyun… alhalin budurwa ce ita ko matar auren da bata shayarwa kuma tasan bata da ciki.

Domin sanin menene Ciwon Zuciya Danna nan

Don haka inkina daga cikin masu fuskantar wannan al’amrin saiki tsaya ki nazari kiga cikin abubuwan dana lissafa ina kika faɗo? wanne abu kike tunanin shine ke kawo miki wannan matsalar,ko da kuwa wasa da kai ake wajen rage sha’awa saboda takura… hakan na iya kawowa musamman idan anashafa kirjin,kuma wannan al’amarin shi ake kira GALAKTORIYA a likitance! wato zubar ruwan nono walau fari fat ko kalar ruwa-ruwa daga nonon macen da bata shayarwa,bata da ciki ko bama ta da aure.

Hakazalik akwai wanda basu da ko guda ko basa aikata ko guda cikin wadancan abubuwa amma kuma suna fuskantar matsalar,irin wannan sune masu IDIYOFATIK GALAKTORIYA, Ma’ana Allah ne ya barwa kansa sanin dalilin matsalarsu.

Don haka wannan bawani abin damuwa bane yakan tafi da kansa,ko kuwa idan aka daina yawan stimulating na nonon,kar kurum don mace na fuskantar haka ace za’a fassarata. 

Ba abin damuwa bane,amma idan ya zamto yana fita da yawa,kuma hakan na sanya mace takura gaki da damuwa to tana iya zuwa taga likita a binkita domin gano tushen matsalar a maganceta.

Domin sanin matsalolin Ƙarancin Bacci (Sleep Deprivation) Danna nan

Musamman a mace me auren da samun ciki yai wahala ga yawan ciwon kai lokaci lokaci,da canzawar gani,da rashin ganin haila a kowanne wata kamar sauran mata to koda bata ganin komi na fita daga nononta wannan na buƙatar ganin likita kwai buƙatar ai brain scan domin gano matsalar idan firolaktinoma ne abata maganin matsalar,ba’a aiki domin maganceta, maganin sha yana wadatarwa.

Sannan wannan matsala ce da har a maza tana iya faruwa mutum yaga inya matsa nononsa ruwa na fita,hakan kan faru ga masu karancin sinadaran jima’i,sau tari ma irin wannan dama basu da sha’awa

Hakanan ana iya ganin haka ko a jariri musamman idan sinadarin istirojin na uwa ya ratsa ta mahaifa ya shiga jikin jariri ko jaririya kafin haihuwa.

Karanta Dalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace

labarin da ya wuceCiwon Zuciya
Labarin na GabaSaurin Inzali (Premature Ejaculation)