Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Magancesa 

0
44

Kowane mutum nada ciki,wanda a kusan kowane lokaci mutum kan samu ciwon ciki da ke da nau’i daban-daban. Akwai wasu nau’in ciwon ciki da idan mutum yana jin su to lallai ya hanzarta ganin likita, domin kuwa wannan suna nuni da cewar akwai matsala da kan iya haifar da matsalololi.

Masana sun gudanar da wani bincike akan jerin alamu na ciwon ciki da keda matukar hatsari ga rayuwar ɗan adam. Sukace idan mutum yana yawan jin kunar zuciya, kamar zuciyar mutum daga tsakiya tana zafi, musamman idan mutum ya gama cin abinci, to lallai wannan idan ya dauki lokaci mutum nasamun haka to ya garzaya asibiti mafi kusa dashi.

Idan kuma cibiyar mutum na yawan ciwo, koda kuwa mutum yaci abinci ko kuwa, haka idan mutum yana samun kunar ciki idan yaci abinci mai zafi ko mai yaji to hakan kan iya zama wata cuta da shan wasu maguguna bazai magance ba, akwai buƙatar mutum ya ga likita don ya duba yaga abun da ke damun mutum.

Hakama idan mutum kan samu ciwon gefen ciki akai-akai to shima yana da buƙatar ganin likita, domin kuwa ana iya dace da hanjin mutum sun sauka daga kan layin da yakamata, shi yasa mutum ke samun ciwon. Sai kuma wasu lokuta mutane kan zauna da cutar nan da ke kira dattin ciki, idan kuma ba’a gaggauta aiki don cireta ba, to tana iya haifar da wasu matsaloli da dama a cikin cikin mutum.

Domin karantaLarurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction) shiga nan 

Menene Kurajan Al’aura Da Yadda Za’a Magancesu

Kuraje al’aura wani irin cuta ko matsala da ke addaar fatar al’aurar dan adam mace ko namiji. Kamar yadda ku ka sani ne kallar kuraje ja ne, sannan wata sa’a ya kan hada da yiwa mutum zafi ko ka ƙaiƙayi tare da dan kunbura a daidai inda ya fitowa mutum. Idan mutum ya kamu da duk wani cutar kuraje wanda bai san da irinsa ba, yayi kokari ya garzaya zuwa wurin likita domin ya duba lafiyarsa.

Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Azzakari Ko Al’aura

Abubuwa da dama kan janyowa mutum kurajen al’aura/azzakari daga cututtuka da ake kamuwa da su musamman a bandaki, wadannan cututtukan a kan kamu da su hanyar jima’i ko kuma ta matsalar rashin isashen karfin sinadarin kariya a jikin bil-adama wato autoimmune disorders. ga kadan daga cikin.

 Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Al’aura

Cutar Kaikayin Al’aurar mace (VAGINAL Yeast Infection):

Irin wannan kurajen ya kan addabi mata ne a al’aurar su musamman idan suna da wata matsalar infection, yana sa kaikayi, a kan fata yayi ja, ya kansa fatar gaba ya kwaye sannan ya kansa mace ta rinka fitar da wani irin farin ruwa gabanta.

Cutar Molluscum Contagiosum:

Wannan cutar ya kan addabi fatar mutum, kurajen kan fito kananun zagayayyun kuraje a al’uarar dan adam. Wani lokacin su kan yi kaikayi sannan kuma ta yiwa mutum zafi.

Cutar Balantis:

Wannan ya kan fito a fatar al’aurar dan Adam ko a bisa kan alkalamin azzakirin, Abun da ya kan kawo irin wannan cutar shine rashin tsabta. Yana kawo kaikayi, ya kan sa fatar wurin yayi ja tare da saka al’aura ta fidda wani irin farin ruwa.

Domin karanta Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

labarin da ya wuceLarurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty)
Labarin na GabaƘurajan Pimples