Tag: magani

  • Maganin Mallaka

    Maganin Mallaka

    Kamar yadda kowa yake fafutukar neman maganin farin jini, haka kuma ake ta faman neman maganin mallaka, mace tana so ta mallake mijinta, shi ma yana so ya mallake ta, abokan ciniki kowa so yake ya mallake abokin huldarsa. 

    Garin neman buƙatar waɗansu, har shirka su ke yi. To ɗan uwa ga maganin mallaka a taƙaice: 

    1. Ka guji musu da jayayya da mutane. 
    2. Ka girmama ra’ayin mutane da fahimtarsa, ka da ka ƙaryata kowa, ka da ka yawaita bayyana kura-kuran mutane. 
    3. Idan ka yi kuskure ka yarda ka yi. 
    4. Kasance mai sauƙin kai, ka bar fushi da tsananta wa mutane. 5. Yi ƙoƙari ka toshe duk wata kafar sabani tsakaninka da mutane. 6. Ka da ka ba da umarni kai tsaye, a a yi umarni a fakaice, kamar “don Allah miƙo min” ko kana da lokaci ka raka ni da sauran su. 
    5. Idan za ka ba da umarni ka fara da godiya da yabo. 
    6. Ka ganar da mutum kuskurensa a fakaice. 
    7. Kafin ka faɗi kuskuren mutum, ka yi shimfiɗa da fara faɗar naka kuskuren, ka yarda kai ma mai kuskure ne. 
    8. Yayin jayayya, ka ba da dama ga mutum ya kare kansa. 
    9. Ka tabbatarwa da mutum kan amfanin aikin da kake so ya aikata. 12. Kasance mai sauƙin kai da ƙaskantar da kai. 

    Ɗan uwa waɗannan ƙa’idoji in ka bi su, za ka mallaki kowa ba tare da ka ɓata masa ba, kuma cikin sauƙi da raha. Sai fa an gwada akan san na ƙwarai. A nan zan dakata, da fatan Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da Lahira. Amın summa Amin.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Cikin suratul Yasin aya ta (68) Allah (Subhanahu Wata’ala) ya ce: 

    Duk wanda muka tsawaita rayuwarsa za mu tauye shi a halitta shin ba sa hankalta ne”. 

    Don haka, duk wanda shekarunsa suka zarce shekarun ganiyar ƙarfi (wato shekara arba’in (40) ), to fa baya zai rinƙa yi ba gaba ba. 

    An karɓo hadisi daga Usamatu ɗan Sharik Allah ya yarda da shi ya ce: ƙauyawa sun ce: Ya Manzon Allah! (Sallallahu alaihi wa sallam), ko ma yi magani? Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa sallam) ya ce; E, ku bayin Allah ku yi magani, haƙiƙa Allah bai sanya wata cuta ba, face sai da ya sama mata waraka (da magani), sai dai ciwo ɗaya, suka ce wane ciwo ne? ya ce tsufa.” Ahmad, Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi. 

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Maganc Shi

    Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Maganc Shi

    Kowane mutum na da ciki, wanda a kusan kowane lokaci mutum kan samu ciwon ciki da ke da nau’i daban-daban. Akwai wasu nau’in ciwon ciki da idan mutum yana jin su to lallai ya hanzarta ganin likita, domin kuwa wannan suna nuni da cewar akwai matsala da kan iya haifar da matsalololi.

    Masana sun gudanar da wani bincike a kan jerin alamu na ciwon ciki da ke da matuƙar hatsari ga rayuwar ɗan Adam. Suka ce idan mutum yana yawan jin ƙunar zuciya, kamar zuciyar mutum daga tsakiya tana zafi, musamman idan mutum ya gama cin abinci, to lallai wannan idan ya ɗauki lokaci mutum na samun haka to ya garzaya asibiti mafi kusa da shi.

    Idan kuma cibiyar mutum na yawan ciwo, ko da kuwa mutum ya ci abinci ko kuwa, haka idan mutum yana samun ƙunar ciki idan yaci abinci mai zafi ko mai yaji to hakan kan iya zama wata cuta da shan wasu maguguna ba zai magance ba, akwai buƙatar mutum ya ga likita don ya duba ya ga abun da ke damun mutum.

    Haka ma idan mutum kan samu ciwon gefen ciki a kai-a kai to shi ma yana da buƙatar ganin likita, domin kuwa ana iya dace da hanjin mutum sun sauka daga kan layin da ya kamata, shi yasa mutum ke samun ciwon. Sai kuma wasu lokuta mutane kan zauna da cutar nan da ke kira dattin ciki, idan kuma ba a gaggauta aiki don cire ta ba, to tana iya haifar da wasu matsaloli da dama a cikin cikin mutum.

    Domin karanta Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction) shiga nan 

    Menene Ƙurajan Al’aura Da Yadda Za A Magance Su

    Ƙurajen al’aura wani irin cuta ko matsala da ke addabar fatar al’aurar ɗan Adam mace ko namiji. Kamar yadda kuka sani ne kalar ƙuraje ja ne, sannan wata sa’a ya kan haɗa da yi wa mutum zafi ko ka ƙaiƙayi tare da ɗan kumbura a daidai inda ya fitowa mutum. Idan mutum ya kamu da duk wani cutar ƙuraje wanda bai san da irinsa ba, ya yi ƙoƙari ya garzaya zuwa wurin likita domin ya duba lafiyarsa.

    Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Azzakari Ko Al’aura

    Abubuwa da dama kan janyowa mutum ƙurajen al’aura/azzakari daga cututtuka da ake kamuwa da su musamman a banɗaki, waɗannan cututtukan a kan kamu da su ta hanyar jima’i ko kuma ta matsalar rashin isasshen ƙarfin sinadarin kariya a jikin bil-adama wato autoimmune disorders. Ga kaɗan daga cikin Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Al’aura:

    Cutar Kaiƙayin Al’aurar mace (VAGINAL Yeast Infection):

    Irin wannan ƙurajen yakan addabi mata ne a al’aurar su musamman idan suna da wata matsalar infection, yana sa ƙaiƙayi, a kan fata ya yi ja, yakan sa fatar gaba ya kwaye sannan yakan sa mace ta rinƙa fitar da wani irin farin ruwa a gabanta.

    Cutar Molluscum Contagiosum:

    Wannan cutar yakan addabi fatar mutum, ƙurajen kan fito ƙananun zagayayyun kuraje a al’uarar ɗan Adam. Wani lokacin sukan yi ƙaiƙayi sannan kuma ta yi wa mutum zafi.

    Cutar Balantis:

    Wannan yakan fito a fatar al’aurar ɗan Adam ko a bisa kan alƙalamin azzakirin, Abun da yakan kawo irin wannan cutar shi ne rashin tsabta. Yana kawo ƙaiƙayi, yakan sa fatar wurin ya yi ja tare da saka al’aura ta fidda wani irin farin ruwa.

    Domin karanta Larurar Gaggautowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

  • Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi Da Maganin Sa

    Akwai hanyoyi da mace za ta bi domin rabuwa da wannan mugun ciwon.

    Shawarar farko game da wannan ciwon za ta bi; ko da ma ba ki da wannan ciwon in har an kusa auranki tom ki guji tsarki da ruwan sanyi sannan ki rinƙa yawan yanke farcenki kina wanke hannunki; ko da zai kai ki sosa gabanki kin ga datti ba zai shiga ba.

    Ki samu waɗannan haɗin ki rinƙa wanke gabanki da su;

    • Gishiri
    • Ganyen magarya
    • Ganyen lalle
    • Kanunfari

    Waɗannan za ki rinƙa dafa su ki samo flask ki rinƙa kama ruwa da su a kodayaushe. Sannan pant ɗinki ki rinƙa dafa shi da ruwan zafi da gishiri da Dettol kina wankewa ki sanya a rana ya bushe ki goge su, sun zama sababbi kenan.

    Maganin Ciwon Sanyi

    Ki nemo waɗannan itatuwan ki dafa su dan kawar da ciwon sanyi, musamman ki fara yin su two months kafin bikinki. Da yardar Allah kin rabu da ciwon sanyi, in kin gan ki da shi to sai dai a jikin mijinki kika samu. Shi ma namijin zai iya waɗannan haɗin dan ya rabu da shi.

    Ga abubuwan da za a nema kamar haka;

    • Sayen zogale ma’ana saiwarsa
    • Kanunfari
    • Jema
    • Jar kanwa
    • Gogamaso
    • Kaimin ƙadangare ko kuma ciyawar wutsiyar ƙadangare
    • Cini da zuga, wasu na cewa bini da zugu

    Waɗannan su ne za a tafasa su sosai sai sun fita hayyacinsu sai a tace a zuba a kofi; a sa zuma a sha sau biyu a rana. In Sha Allah za a rabu da matsalar sanyi kowanne iri ne.

    Don karanta cikakken bayani akan Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection) danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

  • Amfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.

    Amfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.

    Amfani zaitun a jikin ɗan Adam wanda ya kamata mu sani, Shi dai zaitun itaciya ce mai albarka da kuma ba da cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa, zaitun abu ne mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninsa a cikin ALKUR’ANI MAI GIRMA

    haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
    An karɓo daga sayyadina Umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce ku yi abinci da man zaitun kuma ku shafa shi a jikinku, domin haƙiƙa shi yana daga a cikin bishiya mai albarka. tirmizi ne ya rawaito
    Daga Cikin aikin da man zaitun yake a jiki
    CIWON CIKI 
    Duk mutumin da yake ciwon ciki, sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali, ya hada da garin habbatussauda ya cakuɗa, ya sha safe da yamma. Ya samu kamar sati ɗaya yana sha ko kina sha, insha Allah zai samu lafiya.
    CIWON KAI
    Duk mutumin da yake ciwon kai, to sai ya samu man zaitun, yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali ɗaya da safe da rana da dare, insha Allah zai samu lafiya.
    CIWON HAKORI

    Duk mutumin da yake ciwon haƙori, sai ya samo ganyen zaitun da ‘ya’yan habbatussauda, ya saka su a cikin garwashi, ya buɗa bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.

    CIWON HANTA

    Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo, sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali ɗaya da safe ɗaya da rana ɗaya da dare.

    CIWON DADASHI 

    Duk mutumin da yake ciwon dasashi, sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.

    CIWON SUKARI 

    Duk wanda ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana haɗawa yana sha, kafin ya kwanta barci insha Allah

     CIWON ASMA 

    Duk mutumin da wannan ciwon ya kama shi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turarawa.

    CIWON KODA

    Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana. insha Allah.

    CIWON BAYA

    Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaɓa ya dinga shafawa a bayan insha Allah.

    CIWON RAMA

    Duk mutumin da ya ga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zai yi ƙiba.

     ZAZZAƁI MAI ZAFI 

    Duk mutumin da ya kamu da zazzabi mai zafi, to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa a ciki, yana shafe jikinsa da shi insha Allah.

    KARFIN MAZAKUTA 

    Duk mutumin da ya samu kansa a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa a cikin ruwan ɗanyan ƙwai, sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum insha Allah zai samu ƙarfin mazakuta sosai.

    Kada ka gaji duk wani magani da ka gani ka gwada za ka dace insha Allah.

     KYAWUN FUSKA

    Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, ta yi fari, wanda ba zai cutar da shi ba, to, ya dinga shafa man zaitun da na habbatussauda, in zai kwanta barci, bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo, zai yi mamakin yadda fuskarsa za ta koma.

     ZUBEWAR GASHI. 

    Duk matar da gashinta ba ya fitowa sosai, ko in ya fito sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi, ta wanke kanta da shi, sannan bayan ya ɗan bushe, sai ta zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kanta da shi gaba daya kullum.

    ƘARANCIN JINI

    Duk mutumin da yake da ƙarancin jini a jikinsa, to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana.

    BASIR

    Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan gida, wani ma sai ya yi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaɓa sai ya tura shi a cikin duburarsa.

    CIWON MARA GA MATA

    Duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara, saboda fitar jini, in tana so ta samu sauƘin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana haɗawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da za ta yi haila ba zai mata ciwo ba.

    SANYIN ƘASHI

    Duk wanda ƙashinsa ya yi sanyi, ba ya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha, yana kuma shafawa a wajen insha Allah.

    KYAWUN FATA DA LAUSHINTA

    Duk mutumin da yake so fatarsa ta yi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa da shi, bayan ya yi wanka da ruwan ɗumi, zai yi mamaki yadda fatarsa za ta koma insha Allah

     ƘURAJEN ƘARZUWA

    Duk mutumin da yake da ƙarzuwa ko wasu ƙuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyen zaitun ya kirɓa shi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa a wajen har ya warke.

     CIWON KUNNE

    Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya bari in zai kwanta barci, sai a dinga haɗa man zaitun da na habbatussauda yana ɗigawa a kunnensa insha Allah.

     CUTAR KYASBI

    Duk mutumin da yake da KYASBI a jikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe. Ya daka shi, ya yi laushi sai ya haɗa shi da man zaitun ya cakuɗa, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta barci, sai ya wanke.

    SHAFAR ALJANU

    Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun, saboda aljanu ba sa son shi, shida habbatussauda. Don haka yana da kyau, mutum ya lazimci amfani da su a kowane hali, in da hali ma ya mai da su mansa na shafawa, amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu’a.

    CIWON KARKARE

    Duk mutumin da ciwon karkare ya same shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaɓa, sai a zuba man zaitun ɗin a cikin lalle a gauraya, sannan a karanta (AYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki, sannan sai a tofa a jikin wannan karkare insha Allah.

    CIWAN NONO

    Duk matar da take fama da ciwan nono, saboda rashin zubar, to ana haɗa man zaitun da garinsa, a barbaɗa  a kan nonon saboda samun damar zuba, don ƙofofin su bude.

    MOTSA SHA’AWA 

    Man zaitun yana motsa sha’awa, in an shafa shi lokacin da ake yin wasa.

    CIWON SAIFA

    Duk mutumin da yake ciwon saifa, sai ya haɗa man zaitun da garin habbatussauda da kuma zuma farar saƙa ya sha, insha Allah.

    TSUTSAR CIKI

    Duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaɓa su ya sha, wannan tsutsar za ta mutu.

    CIWAN HANJI (ULCER)

    Duk mutumin da yake da gyambon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali ɗaya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi ya jiƙa su ya dinga sha har sai ya warke.

    FITSARIN KWANCE

    Duk yaron da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Da na habbatussauda a zuba a nono a dinga ba shi yana sha, zai daina. Insha Allah

    MUTUWAR JIKI(KASALA)

    Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa, to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zai ji ƙarfin jikinsa.

    YAWAN ZAZZAƁI

    Duk mutumin da yake yawan yin zazzaɓi. To sai ya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaɓa da ruwan zafi. da kuma zuma marar haɗi, ya dinga sha. insha Allah

    CiWON GAƁOƁI

    Duk mutumin da gaɓoɓinsa suke ciwo, to sai ya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gaɓoɓi.

    KWARKWATA

    Duk matar da take fama da kwarkwata, kuma har take son rabuwa da ita. to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaɓa, sannan sai ta bari sai rana ta take, sai ta zuba wannan man a kan nata, ta bar shi ya yi kamar minti (20), sannan sai ta wanke insha Allah za tai ban kwana da kwarkwata.

    CIWAN TARI

    Duk mutumin da ya kamu da kowane irin tari, to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da  citta da tsamiya da zuma. sai ya haɗa su guri ɗaya, ya cakuɗa, ya dinga ci insha Allah.

    MAJINAR ƘIRJI

    Duk mutumin da yake yawan majinar ƙirji to sai ya samu man zaitun. da garin habbatussauda ya haɗa ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma.

    TARIN FUKA

    Duk Wanda yake tarin fuka to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya kullum.

    DOMIN KARIN BAYANI A KAN MAGUNGUNA  DA AMFANIN SU DANNA KOREN RUBUTUN NAN

  • Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Cututtukan Da Ba Su Da Magani

    Aya ta (68) Allah (Subhanahu Wata’ala) ya ce:

    Cikin suratul Yaasiin “Duk wanda muka tsawaita rayuwarsa,tabbas za mu tauye shi a halitta, shin ba sa hankalta ne?”.

    Don haka, duk wanda shekarunsa suka zarce shekarun ganiyar ƙarfi (wato shekara arba’in (40) ), to fa ba ya zai rinƙa yi ba gaba ba.

    An karɓo hadisi daga usamatu ɗan Sharik Allah ya yarda da shi ya ce: “Ƙauyawa sun ce: Ya Manzon Allah! Ko ma yi magani? Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; I, ku bayin Allah ku yi magani, haƙiƙa Allah bai sanya wata cuta ba, face sai da ya sama mata waraka (da magani), sai dai ciwo ɗaya, suka ce, “Wane ciwo ne?” ya ce, “Tsufa.” Ahmad, Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Hulba Wajen Kariya Daga Ciwon Siga (Diabetic Mellitus)

    Hulba Wajen Kariya Daga Ciwon Siga (Diabetic Mellitus)

    Hulba wajen kariya da kuma maganin ciwon siga (Diabetes Mellitus)

    Tabbas! Amfani da hulba na kawo ƙarancin glucose a jininmu.

    Yawa yawan magungunan ciwon siga nada illoli ga lafiyarmu, babbar illar ita ce kaiwa ga matakin ƙarshe na ƙarancin glucose a jininmu, wanda kan iya haddasa jiri, rawar jiki da kuma ruɗewa/rikicewa wanda kan iya sababin rayuwar mutum.
    To ,hulba na taka muhimmyar rawa ga wadanda suke ɗauke da ciwon siga.
    Ita hulba na ɗauke da sinadaran fibre sosai da yake taimakawa wajen rage,
    Sannan ƙwallon na taimakawa ta yadda jiki zai amfani da sikari da kuma haɓaka adadin insulin ɗin da ake saki.
    A wani bincike na masana ya nuna cewa wasu mutane da suke ɗauke da ciwon sikari (type
    sun ci garin hulba adadin 15grams (3.6tsp) ya rage tashin glucose a cikin jini, bayan cin abinci. Daga ƙarshe bincike ya bunciko cewa adadin 10grams (2.4tsp) ya kamata a ci, a abinci ko a jiƙa a ruwan zafi a sha, a rana ga masu ɗauke da cutar ciwon siga ko a waɗanda suke cikin hatsarin kamuwa da cutar.

    Domin sanin yadda ake yi wa namiji mai shiru shiru danna nan

  • Mene Ne Tab Priton Chlo-Pheniramine

    Mene Ne Tab Priton Chlo-Pheniramine

    (Piriton) Ana shan priton sabo da abubuwa da dama, kamar irin su mura, toshewar hanci, ƙaiƙayin jiki da kuma  attishawa.

    Ana shan priton (1) kullum da rana (2) kullum idan mura ta same ka za ka iya shan priton ko kuma kana fama da ƙaiƙayin jiki, za ka sha priton (1) Kullum a dare kafin kwanciya barci, bugu da ƙari, idan ka yi tafiya a kan abin hawa ko mashin ko mota iska ta bige ka, za ka ji hanci na ƙaiƙayi ko za ka ji kunnanka yana ƙaiƙayi ko ka ji maƙogaronka yana zafi ya bushe ko kuma ka ji kamar za ka yi amai, a irin wannan yanayin da ka tsinci kanka, a lokacin za ka ɗauki priton (1) Tablet ka sha, in ka sha bayan wasu yan lokuta kamar minti talatin za ka ji duk wannan matsalar ta rabu da kai.

    (DOKOKI)

    Priton yana sa barci ko mutuwar jiki
    (1) Idan za kai tuƙin mota ƙar ka sha priton, har sai ka sauka daga titi.
    (2) Idan za kai aiki ko na office kar ka sha priton har sai ka dawo gida.
    (3) Ba a so a ba wa yaro priton ɗan ƙasa da shekara shida (6)
    (4) Idan za ka ajiye priton, kada ka ajiye inda rana za ta daka, ko kuma inda ƙananan yara za su ɗauka.
    (5) Sannan mace mai shayarwa idan ɗanta yana ƙasa da wata shida (6).
    Kar ta sha priton har sai ta je da su ga likitan dake kusa da ita.

    MATSALOLIN CUTARWA KO ILLOLI(SIDE EFECTS)

    Yana sa barci mai nauyi. Sannan alamun jin amai yana busar da yawun baki
    Ko kuma jiki ya kama tsananin ƙaiƙayi, Kuma yana sa ciwon ciki ko kuma mutum ya fita hayyacinsa ya rasa mai yake.

    Wannan ɗan taƙaitaccen bayani ne, kada a manta, duk lokacin da ba a da lafiya, likita ya kamata a tuntuɓa, domin samun magani da ya kama, ba yanar Gizo-Gizo ba. Mun samar da wannan bayinin domin wayar da kan al’umma.

    Domin karanta mene ne Maleria ko taifud danna koren rubutu

  • Amfanin Nonon Raƙumi A Jikin Ɗan Adam

    Amfanin Nonon Raƙumi A Jikin Ɗan Adam

    CUTUTTUKAN DA NONON RAƘUMI YAKE MAGANI A JIKI

    A wasu lokuta da suka shuɗe a  baya, mutane na ɗaukar nonon raƙumi a matsayin abinci ga ‘ya’yan raƙuma ko ga masu kiwon raƙuma kawai. Sannu a hankali sai gashi bincike ta 6angaren magunguna sun kai ga gano alfanun nonon raƙumi.
    Akwai wani lokaci a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da wasu mutane suka je Madina, sai rashin lafiya ta kama su, mai nasaba da cutukan ciki, sai Manzon Allah (S.A.W) ya umurce su, da su gauraya nonon raƙumi da fitsarinsa, sannan su sha.
    Suna sha kuwa, nan take sai suka warke. Hadith:Bukhari(2855) da Muslim (1671).
    Wannan wani dalili ne babba da za mu yi amfani da shi, wajen kafa hujja cewa tabbas nonon raƙumi na ƙumshe da magani.
    A bincike na kimiyya, an tabbatar nonon raƙumi na ɗauke da wasu ɗimbin sinadirai masu amfanar jiki, kamar su na Vitamin C wanda ya ninka Vitamin C din dake a cikin nonon saniya fiye da sau goma. Sai sinadiran calcium masu ƙarfafa karfin ƙassa da haƙora (bones and teeths). Ga su Sodium,Vitamin A da vitamin B2, sinadiran iron,copper,magnesium,phosphorus,selenium,potassium da dai makamantansu.
    Da ɗimbin sinadaran dake a cikin nonon raƙumi da kuma anti microbial properties din da yake ɗauke da su, sun ba shi damar kasancewa magani sosai, dama kariya ga wasu cutuka, inda yake ƙarfafa garkuwar jiki (immunity).
    1-Yana taimakawa wajen kaiwa da kawowar jini a cikin jijiyojin jiki (proper blood circulation)
    2-Yana maganin kumburin ciki dama ciwon ciki.
    3-Yana sa girman jikin ɗan Adam.
    4-Yana kare cutukan dake yi wa ciki da hanjin cikin dameji (celiac disease)
    5-Yana aiki dan tabbatar da lafiyar zuciya.
    6-Yana maganin ciwon suga (diabeties).
    7-Yana maganin ƙazuwa.
    8-Yana kare ƙoda daga kumburi (kidney imflammation) ya kuma kare mafitsara da sauwake fitar fitsari ba tsaiko (renal protection)
    9-Yana maganin cutukan daji wato (cancer) kama daga kansar mama, ciki, huhu, ko ta fata waton (skin cancer)
    10-Masu fama da kumburin ciki da yawan rugugin ciki da tashin zuciya da bayan gari mai wahala, sai su rinƙa shan nonon raƙumi.