Tatsuniyar Wata Mata Da Aljani

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wata mata a wani ɗan ƙauye, wadda ta jima tare da mijinta, amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan buƙata ba, sai suka dangana.

Ana nan, ana nan, wata rana matar ta je gona tana noma, sai ta ji kukan yaro a gindin wata bishiya. Da ta matsa kusa, sai ta ga wani jariri a cikin tsumma, sai ta ɗauke shi ta goya, ta kuma ɗauki fartanyarta, ta koma gida.

Da mijinta ya dawo sai ta ɗauko jariri ta kawo masa, tace da shi: “Da man ina da kwantaccen ciki, shi ne yanzu ka ga na haihu a gona.” Mijin ya yi shiru, yana tunani, sai ya ce: “Anya kuwa ke ce kika haifi jaririn nan?” Ta dage cewa ita ce ta haife shi.

Sai ya ce: “To mun gode wa Allah.” Suka ci gaba da renon yaro, amma duk sanda suka je gona da shi sai ya riƙa kuka ya hana su aiki. Da matar ta ga haka na faruwa kullum, sai ta je cikin danginta ta ɗauko ƙanwarta domin ta riƙa renonsa a gida idan sun tafi gona ita da mijinta.

Rannan mai gida da matar suka tafi gona suka bar yaro a hannun mai reno. Can sai mai reno ta ga yaron ya rikiɗa, ya zama babban mutum, sai ya yi aman ’yan mata goma sha biyu. Ya buɗe rumbu, kuma ya fito da hatsi suka sussuka suka niƙa, sai ya kwashe garin ya barbaza shi a tsakar gidan; sai kuma ya haɗiye ’yan matan, ya rikiɗa ya koma ƙaramin yaro.

Can da mai gida da matar suka dawo, suka ga ɓarnar da aka yi musu, sai matar ta kama ƙanwarta da duka wai ta yi mata ɓarna. Yarinya tace ba ita ba ce, yaron ne. Sai yayarta ta ce: “Ta yaya wannan ƙaramin yaro zai buɗe rumbu, ya ɗebo hatsi, ya sussuƙa shi ya niƙe ya zubar?” Ba su dai yarda da bayanin yarinyar ba.

Haka dai, kullum idan sun fita sai ya yi wata ɓarna, kuma sai matar nan ta doki ƙanwarta. Wata rana matar ta kama ƙanwar tana duka akan ɓarnar da yaron ya yi, sai wata tsohuwa ta kira ta tacemata: “Wannan duka da kike yi wa ƙanwarki fa ba ta da laifi.

Wannan yaron da yake gidanku ba ki sani ba tsohon aljani ne kika kawo gidan.” Mamaki da tsoro suka kama matar, amma sai tsohuwar ta ci gaba da bayaninta tana cewa: “Idan kina son ki tabbatar, gobe kada ku je gona; bayan gari ya waye ku fita ku ce za ku gona; sai ku zo ku ɓuya a gidana, za ku ga komai da idanunku.”

Sai ta ce: “To. Allah ya nuna mana goben.” Da gari ya waye mijin da matar suka shirya, kamar za su gona. Da suka fita sai suka ɓuya a gidan tsohuwa. Bayan wani ɗan lokaci sai suka ga yaron ya rikiɗa, ya zama babba; suna gani ya buɗe bakinsa ya yi aman ’yanmata goma, nan da nan ya hau rumbu ya buɗe ya ɗebo hatsi, nan take ’yan matan nan kuma suka sussuƙe hatsin, suka niƙe shi, suka shiga watsar da garin a cikin gida, suna yi suna waƙa.

Da matar ta ga abin da yaron ya yi sai ta gaya wa mijinta gaskiya da cewa, ai da ma ba ɗanta ba ne, kuma a gona ta tsince shi. Sai mijin ya ce: “Tun farko daman na yi shakka, ga shi ta tabbata ƙarya kika yi mini.” Sai ta faɗi tana kuka, ta shiga hurwa tana ba shi haƙuri, tace: “Ai da wannan ɗa, gara mu zauna babu.”

Da tsohuwa ta ga abin da ke gudana tsakanin mijin da matar, sai ta ce: “Yanzu abin da za ku yi domin ku rabu da wannan masifa shi ne, ku samo akuya da ƙwaikwaye guda
bakwai, sai ku ce za ku je ganin gida. Bayan kun kama hanya kun shiga daji, sai ku sami gindin tsamiya ku ce za ku huta.

Idan kun shimfiɗe yaron sai ku ajiye ƙwaikwayen nan bakwai a gefensa ku ɗaure akuyar a jikin tsamiyar. Can sai ku ce kun yi mantuwa.” Ta ce da su: “Kuna jin abinda nake faɗa?” Suka ce: “Muna ji sarai.” Ta ci gaba da ce wa matar: “Ki ce za ki koma gida ki ɗauko abin da kika manta.

Daga nan kada ki dawo. Jim kaɗan shi ma mijinki sai ya ce zai bi sawunki saboda kin daɗe. To idan kun tafi kada ku koma; da zarar ya ga kun daɗe zai tashi ya tafi abinsa”. Sai suka yi wa tsohuwa godiya suka koma gida. Da gari ya waye sai matar nan da mijinta suka ce za su ganin gida, sai suka samo duk abubuwan da tsohuwa tace su nemo.

Da lokacin tafiya ya yi sai suka kama hanya har suka isa gindin wata tsamiya, sai mijin yace ya kamata su huta a nan; suka ɗaure akuya a gindin bishiya suka zauna, can sai mijin ya ce: “Kash!, mun yi mantuwa.”Sai matar ta ce: “To bari in je in ɗauko.”

Mijin ya ce: “To gara ki yi sauri.” Bayan matar ta tafi, sai ya ce ta daɗe, bari ya bi sawunta. Shi ma ya tashi ya bar wurin. Da ya yi nisa sai ya ɓuya. Yana nan yana kallon gindin tsamiya, can sai ya ga yaro ya rikiɗa ya zama tsoho tukuf da sanda; sai ya kunce akuyar, ya riƙe a hannunsa; kuma ya ga ya ɗebi ƙwaiƙwayen nan bakwai ya kama hanya ya shiga ƙungurmin daji.

Da mijin nan ya ga haka, sai shi ma ya juya, ya kama hanyar gida. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
  • Ƙarya da ha’inci masifu ne da ke iya ɓata zamandaakadaɗe cikin amana.
  • Neman afuwa da lafiya su ne kaɗai ke iya magance matsala a zaman amana.
  • Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa.
  • Ƙarya fure take, ba ta ’ya’ya.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Makauniya Da Ɗanta
labarin da ya wuceTatsuniyar ‘Yar Mowa Da ‘Yar Bora
Labarin na GabaTatsuniyar Marayu Biyu
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.