Tatsuniyar Wata Mayya Da Danta

0
13

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wata mayya a wani gari, tana zaune da mijinta, har ta sami rabo. Daga ƙarshe ta haifi ɗanta namiji aka sa masa suna Malgwi. To da man tun tana da cikinsa ubansa ya rasu, ya bar dokinsa, wanda yaron ya gada. Uwar ta kula da dokin har Malgwi ya girma, ya zama saurayi kyakkyawa.

Wata rana sai wata ƙawar uwar Malgwi ta ziyarci gidansu. Sai ita da baƙuwa suka zauna a tsakar gida suna hira. Sai ƙawar tace da ita: “Ya kamata ki san yadda kika yi da ɗanki tun da ya girma ya kai a cinye shi.” Sai uwar ta ce: “E, ai ina shiri, kuma a daren yau zan gama da shi, na ga ya fara shige-shige.”

Ashe Malgwi yana bakin ƙofar ɗaki yana jin duk abin da suke faɗa; sai ya fita waje ya sami wuri ya zauna, ya kama kukan zuci yana cewa ashe uwarsa mayya ce bai sani ba? Kuma ƙila ma ita ce ta cinye babansa, yanzu kuma za ta cinye shi. Nan dai ya yanke shawarar barin garin; sai ya je ya kwance dokin da ubansa ya mutu ya bari, ya ɗaura masa sirdi ya hau ya kama hanya, ya bar garin.

Da uwar Malgwi ta fito daga ɗaki ta ga an kwance doki, sai ta fita tana tambaya ko an ga wanda ya kwance doki. Sai waɗanda suka gani suka gaya mata cewa ɗanta ne ya wuce a kan dokin, ya bar garin. Sai ta koma gida ta sa rigar maitarta, ta fito bin sawun Malgwi. Duk sanda ta yi taku ɗaya sai ta je kusa da shi, shi kuma sai ya ƙara zaburar doki, yana sulalewa yana waƙa yana cewa: “Dokin baba kai ni gari ba kusa ba.”

Ita kuma uwar tana ba shi amsa tana cewa: “Ga ni nan Malgwi, ga ni nan ɗana.” Haka dai tana gudu ɗuwawunta biyu suna motsi suna waƙa suna cewa: “Ka tumbuɗe ka durje, Da ka faɗi bakin maza.” Ita kuma tana cewa: “Ga ni nan Malgwi, Ga ni nan dana.” Haka ya ci gaba da sukuwa a kan dokin nan.

In sun haɗu da mutane sun tambaye shi abin da ya sa shi gudu haka sai yace:
“Abin da ke bayana fi ƙarfin kowa, ku ba ni hanya.” Yana cikin wannan gudun ceton rai, sai wasu mutane suka sake tsai da shi, amma sai ya ƙi tsayawa har dai ya kai gaɓar wani babban gulbi; sai dokin ya tsaya.

Da Malgwi ya ga dokin ya tsaya, sai ya fara waƙa yana cewa: “Dokin baba kai ni gari, ba kusa ba.” Da doki ya ji waƙa sai ya faɗa cikin ruwa yana ninƙaya har suka haye, kuma suka shiga cikin wani ƙungurmin daji wanda ke cike da aljannu da manyan namun daji. A nan ne fa shi da dokin suka yi cirko-cirko, suka kasa yin gaba, balle kuma baya.

Da ƙurar hanya ta lafa, sai ga wasu manyan namun daji a tsugune suna kallon Malgwi da dokinsa. Sai suka tambaye shi labarin halin da yake ciki, sai ya yi musu bayani. Da suka ji bayaninsa, sai suka ba shi izini ya sami wuri a gindin wata bishiya da ke kusa ya zauna ya huta. Da ya ɗan zauna yana hutawa, sai namun dajin nan suka ce masa za su taimake shi.

Ya ɗaure dokinsa, ya yanki ciyawa ya sa a gabansa, doki kuma ya fara ci. Can Malgwi ya fara hutawa, har da ɗan gyangyaɗin gajiya, sai ga uwarsa ta iso inda yake a guje, tana haki da waƙa. Sai ɗaya daga cikin namun dajin nan ya buɗe bakinsa, wanda ya fiƙofar gari girma. Ita kuwa idanunta sun rufe, ga shi ta doshi Malgwi gadan- gadan za ta yi masa rungumar mutuwa irin ta mayu, sai ta faɗa bakin babban naman dajin nan, ya haɗiye ta.

Bayan ya haɗiye ta, sai ya sami ruwa ya sha, ya yi gyatsa kuma cikinsa ya ɗan ɗaga kaɗan, amma fa bai ƙoshi ba, saboda ya daɗe bai ci komai ba. Sai namun dajin suka dubi Malgwi suka ce masa: “Mun yi maka maganin mayyar nan. Idan ka ga dama sai ka kama hanya ka koma garinku.”

Da Malgwi ya ji haka, sai ya yi musu godiya; ya kwance dokinsa, ya ɗaura masa sirdi, ya hau, ya haye ruwa, ya kama hanyar garinsu, bai tsaya ba har gida. Ƙurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Makusancinka na iya zama makashinka:
  • Ana zaton wuta a maƙera, ashe tana masaƙa:
  • Mai rabon ganin baɗi, sai ya gani:
  • Ceto daga Ubangiji yakan zo ta kowane hali:
  • Zarmewa wajen kula da yaro takan janyo masa bala’i ta fuskar da ba a zata ba.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Awa Da Dawi

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Awa Da Dawi
Labarin na GabaTatsuniyar ‘Yan Bakwai Da Aljana
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.