Tatsuniyar ‘Yar Mowa Da ‘Yar Bora

0
3

Ga ta nan, ga ta nanku.

A wani gari an yi wani mutum mai mata biyu da ’ya’ya biyu, ’yan mata; ɗaya sunanta ’Yar Mowa, ɗayar kuma ’Yar Bora. Suna nan, ran nan sai mijinsu ya rasu. Bayan ɗan wani lokaci kuma sai uwar ’Yar Mowa ta rasu, ta bar uwar ’Yar Bora kaɗai. To da ma kafin ta rasu, ta kira kishiyarta tace mata: “Don Allah ga amanar ’yata nan; ki kula da ita.”

Sai tace: “To.” Amma da ta rasu sai uwar ’Yar Bora ta fara ganawa ’Yar Mowa azaba. Kullum ita ke yin hidimar gida, ba ta da lokacin hutawa. Wata rana da gari ya waye sai aka ga ’Yar Bora ta yi fitsarin kwance, amma sai uwar ’Yar Bora ta ce ai ’Yar Mowa ce ta yi. Saboda haka ta matsa mata sai ta je Rafin Bagaja ta wanke shimfiɗar da aka yi wa fitsari.

To Ruwan Bagajar nan kuwa yana cin mutane. Amma tunda ba yadda ta iya, sai ta ɗauki shimfiɗa ta kama hanyar rafi. Tana cikin tafiya a daji da ta ga rafi sai ta kama waƙa tana cewa:

“Kogi, kogi,

Ko kai ne Ruwan Bagaja,

Bagajar kauye da ’Yar Sarki,

Da ’Yar Bora ta yi fitsari,

Aka ce ni ce,

Sai na wanke

A Ruwan Bagaja.”

Tafiyar ‘Yar Mowa Sai kogi ya ce: “Ni ba ni ne Ruwan Bagaja ba. Ni Ruwan Madara ne. Idan za ki zauna ki sha to.” Sai ta ce ta gode; taci gaba da tafiya. Can sai ta tarar da wani ruwan, sai ta sake maimaita waƙar da ta yi. Sai kogi ya ce mata shi Ruwan Zuma ne. Idan tana so ta zauna ta sha. A nan mata ce ta gode, ta ci gaba da tafiya.

Sai ta tarar da Kogin Shinkafa da Kaji, sai ta rera waƙar nan, kogi yace mata: “Ni Kogin Shinkafa da Kaji ne. Idan kina so ki zauna ki ci.”A nan ma ta yi godiya, ba ta ci ba; ta yi gaba. Jim kaɗan kuma sai ta tarar da Ruwan Jini. Bayan ya ji bayaninta a cikin waƙa, sai ya ce: “Ni ba Ruwan Bagaja ba ne. Ni Ruwan Jini ne. In za ki sha to.”

Sai ta ce ta gode ta yi gaba. ’Yar Mowa dai ba ta gaji ba, ta ci gaba da tafiya har ta tarar da wani ruwan. Da ta yi irin waƙar da ta saba sai yace: “Ni ne Ruwan Bagaja; amma ke kuwa wannan yarinya me ya kawo ki wurina inda ba a zuwa?” Sai ta feɗe masa biri har wutsiya a kan abin da ya faru da irin halin da take ciki bayan rasuwar mahaifiyarta.

Da Ruwan Bagaja ya ji sai ya ce: “To ai sai ki wanke a nan.” Nan take ta yi godiya, ta tsuguna ta wanke shimfiɗa, amma kafin ta gama har dare ya yi. Da ta gama, ta tashi za ta tafi sai kuma ga hadari ya taso, amma kuma ga babu wurin fakewa. Can sai ta hango wata ’yar bukka, ta ko nufi wurinta ta fake.

Tana zaune a ciki, sai ta ga wata fitila ta kunna kanta da kanta, mamakin wannan ya kama ta, sai kuma ta ga cinya a gefeɗaya. Kafin ta gama mamaki sai kuma ta ga kai shi kaɗai a gefen cinya yana motsi. Sai cinya ta ce da ita: “Kai yanayi miki maraba.”
Can kuma sai cinya ta yi nata motsin, sai kai yace da ita: “Cinya ma tana yi miki maraba da zuwa.”

Duka dai yarinya tana amsawa da cewa: “Na gode da wannan maraba.” Suna nan zaune, sai kai ya yi wani motsi, sai cinya ta ce da yarinyar: “Wai yunwa yake ji; ki ɗauki
wancan kwanon ki ba shi abinci.” Ba tare da wani musu ba, ’Yar Mowa ta tashi ta zuba masa abinci, ta zauna kusa da shi da abincin a kan cinyarta har ya ci ya ƙoshi.

Sai ya sake yin wani motsin, sai cinya tace da yarinyar: “Wai ki ba shi ruwa.” Nan da nan ta ba shi ruwa. Suna zaune a haka, can sai ga wani wafcecen kumurci ya shigo, amma kuma ba ta ji tsoro ba. Jim kaɗan sai ta ga macijin ya fara aman ƙwaiƙwaye. Ya amayar da uku ƙanana, daga baya ya yi aman wasu manya uku.

Da ya gama, sai cinya ta yi wani motsi, sai kai ya ce: “Wai idan gari ya waye za ki tafi, ki zaɓi ƙwaiƙwaye uku ki tafi da su, kuma kada ki fasa sai kin isa kusa da garinku.” Ta ce: “To. Na gode, Allah ya kai mu goben.” Da gari yawaye, sai ’Yar Mowa ta tsuguna ta zaɓi ƙwaiƙwaye uku, amma kuma ƙanana ta zaɓa. Ta kama hanya tiryan-tiryan, ta doshi garinsu.

Sakamakon ‘Yar Mowa 

Da ta isa bayan gari, sai ta fasa ƙwai ɗaya, sai ta ga ingarman doki da adon kayan ƙawa da sauran kayan alatu iri-iri. Da ta fasa ƙwai na biyu kuma, sai ta ga ’yan mata gomiya goma suna ɗauke da kayan ado da kayan sa wa iri-iri. Da ta fasa ɗayan, sai ga dukiya har da gida ƙerarre, da duk abin da za a nema don jin daɗin duniya a ciki.

Sai ta yi godiya ga Allah, ta taka ta hau dokin nan, ba ta zame ko’ina ba sai a ƙofar gidansu. Da kishiyar uwar da ’Yar Bora suka gan ta da dukiya da kwalliya kamar sarauniya, sai kishiyar uwar ta nemi sanin yadda ta sami wannan abu haka. A nan ta ba ta labarin zuwanta Ruwan Bagaja, har zuwa inda ta fasa ƙwaiƙwayen nan guda uku. Sai uwar ’Yar Bora ta ce ita ma sai ’yarta ta je washegari, ita ma ta samo nata.

Tafiyar ‘Yar Bora

Washe-gari tun da duku-dukun safiya, uwar ’Yar Bora ta tura ta wai don ta je ta wanke shimfiɗa a Ruwan Bagaja. Ita kuwa ta kama hanya. Da ta je Ruwan Madara sai ta yi
waƙa kamar yadda ’Yar Mowa ta yi. Sai ruwan yace, “Ni Ruwan Madara ne, ba Ruwan Bagaja ba. Amma in kina so, ki zauna ki sha.”Sai ta ce: “To.”

A nan ta zauna, ta sha madara har sai da ta ƙoshi. Ta tashi ta yi gaba, ko godiya ma ba ta yi ba. Da ta tarar da Rafin Shinkafa da Kaji, sai ta yi masa waƙa. Sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, Ruwan Shinkafa da Kaji ne; idan za ta ci, ta zauna ta ci. Sai ’Yar Bora ta ce: “Ai ko ba ka faɗa ba zan ci”. Sai tazauna ta ci har ta ƙoshi.

Ta sami ruwa ta kwankwaɗa, ta yi gaba. Da ta isa Ruwan Jini sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, shi Ruwan Jini ne. In za ta sha to. Sai ta yi masa gatsine, ta bugi cinya irin yadda masu tsiwa kan yi, tace: “Me zan yi da wani ruwan jini?” Sai ta tofa masa yawu, ta wuce. Da haka dai ’Yar Bora ta ci gaba har ta kai ga Ruwan Bagaja.

Da ta tambaya ya ce shi ne Ruwan Bagaja, sai shi kuma ya tambaye ta abin da ya kai ta neman Ruwan Bagaja. Sai ta ce ta zo ne ta sami irin dukiyar da ’yar’uwarta ta samu a nan. Sai Ruwan Bagaja yace: “To ga shi kuwa yanzu dare ya fara yi.” Kafin ma ya gama yi mata bayani sai hadari ya taso. Da ta hango wata bukka sai ta je ta shiga ta fake ruwa.

Can sai fitila ta kunna kanta, sai ta ga cinya a gefe. Sai ta yi kururuwa, a gefe kuma sai
ta ga kai ya ce da ita: “Kada ki ji tsoro.” Daga nan sai cinya ta yi motsi, sai kai ya ce: “Wai sannunki da zuwa.” Da ta ji haka sai ta yi tsaki, irin wanda ta saba yi wa mutane, ta ce: “Mene ne kuma na wata cinya tace tana gaishe ni?” Da cinya ta ji haka sai ta yi motsi.

Sai ta dubi yarinyar tace: “Kai ya ce wai ki ba shi abinci yana jin yunwa, ga abincin can ki ɗauko ki ba shi.” A nan ma sai ta sake yin tsaki ta ce: “Kamar ni in ba shi abinci?” Sai ta tashi ta ɗauko abincin. Da ta ga ƙafafun kaji ne da kifi da naman rago da alkaki da nakiya, sai ta zauna ta cinye. Tana cin wannan abinci, sai cinya ta sake yin motsi.

Shi kuma kai sai ya ce: “Wai ki ba shi ruwa.” Sai ta ce: “Amma fa cinyar nan da raini kike.” Da ta ɗauko ruwan sai kawai ta shanye, ta bar kai bai ci ba, kuma bai sha ba. Suna nan zaune, sai ga ƙaton kumurci ya shigo, sai ’Yar Bora ta ƙwalla ihu. Maciji bai kula ba, ya fara aman ƙwaiƙwaye shiɗa. Uku manya, sauran ukun kuma ƙanana.

Sai cinya ta yi motsi, sai kai ya ce: “Wai idan za ki tafi gobe ki ɗebi ƙwai uku ƙanana, in kin je bayan garinku sai ki fasa.” Da ta ji haka, sai ta karkace kai irin na marasa kunya tace: “Yau na ji wani abu, ku za ku gaya mini in ɗiba? Ai koba ku faɗa ba zan ɗiba.”

Sakamakon ‘Yar Bora

Da gari ya waye, sai ta ɗebi ƙwaiƙwaye uku amma manya, ta tafi. Da ta fara ’yar tafiya sai ta ce: “Yanzu wai har ma sai na je gida zan fasa kayana?” Sai kawai ta fasa ƙwai
biyu tare. Tana fasawa sai ga jakai da kutare da ƙudaje suna bin ta. Sai ta fasa na uku, sai ga tarkacen shara da tsummokara tili-tili. Sai kutaren nan suka ɗora ta a kan jaki, suna raka ta.

Kudaje na bin su har gida. Da uwar ta ga ’yarta, sai ta gudu. Da ’yar ta ga uwar tana gudun ta, sai ta ce da ita: “Tsaya mana, ni ce ’yarki fa.” Sai uwar ta ce: “A’a, yau na rabu da ke, ba ni ba ce.” Sai ta gudu ta bar ta da kutarenta da jakan nan da ƙudaje suna ta zaga gari. Mutanen ƙauyukan kusa da su da suka ji labari suka yi ta tururuwa suna zuwa kallo. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Yi wa yara kyakkyawar tarbiya shi ne babban jarin da za su juya don samun kyakkyawar rayuwa.
  • Rashin tarbiya mai kyau shi ne jigon kaiwa ga rashin nasara.
  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Makauniya Da Ɗanta

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Mai Haƙan Ɓera
Labarin na GabaTatsuniyar Wata Mata Da Aljani
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.