Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wani mutum da ke garin Yamutsawa ya je gidan Sarkin garin ya ce yana so zai ba Sarkin ‘yarsa ya aura. Shi kuwa Sarkin Yamutsawa ya daɗe da matansa biyu. Da Sarki ya ji haka sai ya sanar da shi cewa ba zai ƙara aure ba, idan ma ya auri mace ta uku, to kuwa zai gille mata kai.
Sai mutumin ya ce: “Na ji, na yarda ka aure ta ko za ka gille mata kan.” Shi kuma mutumin daman malami ne ɗanbaiwa. Shi ke nan, Sarki ya aure ta. Kamar yadda Sarki ya faɗa, washe-garin ranar da amarya ta yi kwanan farko a gidansa, sai ya sa aka fille mata kai. Amma kuma kullum idan an fille kanta jim kaɗan sai ga wani kan ya fito.
Ana nan, sai matan Sarki biyu suka sami ciki, amma ita ba ta samu ba. Ganin haka sai uban amarya ya sauya mata kama ya umarce ta da ta bi Sarki lokacin da zai fita farauta. Sai ko ta sami juna biyu a wannan lokaci. Bayan ‘yan watanni ciki ya fito, Sarki ya tambaye ta: “A ina kika sami ciki?”
Ba ta tsaya wata inda-inda ba sai kawai ta ce: “Kai ne ka yi min.” Shi kuma ya musanta. Amma sai ta yi masa bayani dalla-dalla cewa ai ta sauya kama ne sanda suka haɗu, lokacin da ya je farauta. Da Sarki ya ji haka sai ya ce: “Ai mai waɗancan kamannin da kika faɗa ta fi ki kyau.” Da ta ƙara yi masa bayani, sai ya amince lallai shi ne mai cikin.
Bayan wani ɗan lokaci kuma, sai Sarki ya tara matan nan su uku ya ce: “Kowacce ta je ta haihu a gidansu.” Sai kowaccensu ta kwashe kayanta, ta tafi gidansu. Ba da daɗewa ba kuwa sai ɗaya daga cikinsu ta haifi Ɓera, ɗayar kuma ta haifi yaro Ƙadangare, ita kuma amarya ‘yar mallam, ta haifi ɗa kuma ya yi kama da ubansa, watau Sarki.
To daman ita wadda ta haifi Ɓera ta haihu ne a cikin toka. Wadda ta haifi Ƙadangare kuma ta haihu ne a daji. Ita kuma ‘yar malami, ta haihu ne a gidan ubanta, shi ya sa ta haifi mutum. Bayan sun gama wanka, jikin kowacce ya yi ƙwari, sai kowacce ta koma ɗakinta, watau gidan Sarki.
Bayan ‘yan kwanaki da komawar matan Sarki, sai ya ƙ kulawa da amaryar domin shi har yanzu bai yarda da cewa ita ce ta haifi yaron nan ba. Sai ya yanke shawarar cewa a kai yaron reno gidan danginsa, kuma kada ɗaya daga cikin matan ta sake ganin sa har sai ya girma sai a kawo shi ya nuna uwarsa da kansa.
A kwana a tashi, yaro ya girma, sai Sarki ya sa aka tara mutanen garin domin su ga abin da zai faru. Ya sa matansa su uku suka fito, ya tura a zo da ɗan. Yaro ya zo a kan Doki. Manufar taron dai ita ce yaron ya fidda wadda ta haife shi daga cikin matan Sarki. Sai kawai aka ji ya kama wannan waka: ”
Wace ce uwata?
Tambaya nake, Wace ce gyatuma ta?
Wace ce iyata, wo-wo.
Ina kara tambaya, Wace ce mahaifiya ta?”
Sai matar Sarki wadda ta haihu a daji ta karɓi waƙa:
“Ga ni, ga ni, ni ce, ɗana,
Ga ni, ni ce mahaifiyarka,Ya kai ɗana.
Ga ni, ni ce gyatumarka, wo-wo,
Zo in rungume ka, Ya kai dana.”
Da yaron ya ji bayanin da ta yi masa a cikin waƙar, kuma bai gamsu ba, sai ya rera wata waƙar yana cewa: “A a, a ina kika haife ni? Gaya mini, a ina kika haife ni? Aina kika haife ni, wo-wo?”
Da mutanen gari da Sarki sai duk suka yi shiru, suna jira su ji abin da za ta ce, ko zai tabbatar ita ce uwarsa, ko kuma ba haka ba ne. Sai ta kashe murya wadda ta fi ta da zaƙi tana cewa: “Ai a daji na haife ka, A Dajin Ƙarangiya na haife ka. Kai Yarima, Ai a daji na haife ka, Ni a daji na haife ka, wo-wo.”
Ba tare da wani ɓata lokaci ba, sai kawai ya ce: “Je ki gaba, Ki yi gaba, Ba ke ce mahaifiya ta ba. Je gaba,Ba ke ce mahaifiya ta ba Wo-wo, Ba ke ce mahaifiyata ba.” Haka ta kare, ta wuce tana jin haushi. Wadda ta haihu a toka ma ta zo, ita ma ya ce ba ita ce uwarsa ba.
Da aka zo kan mahaifiyarsa, wadda ita ce ta ƙarshe da ta faɗi inda ta haife shi, sai ya yi wani gwauron tsalle don murna har sai da ya shallake rimin da ke kusa da fada. Jama’a ma suka ɓarke da sowa, sai ɗan Sarki ya je ya rungume uwarsa don murna. Shi kuma Sarki saboda jin haushin matansa sun yi masa ƙarya dangane da haihuwar magajinsa, sai ya sa aka fiffille musu kawuna.
Ya sa aka raba ƙasarsa biyu. Shi ya ci gaba da mulkin rabi daga fadarsa, ɗaya rabin kuma ya mallaka wa ɗan. Malamin nan kuma uban matar Sarki ya riga ya tsufa. Jikansa ɗan Sarki kuma ya gina masa gida a ɓangaren ƙasar da uban ya mallaka masa. Labarin wannan abin mamaki ya wuce garin Yamutsawa domin ya gama ko’ina a garuruwan da suke kusa da shi. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Wajibi ne shugaba ya yi kyakkyawan bincike kafin ya zartar da kowane hukunci don ya kauce wa yin kuskure.
- Son zuciya ɓacin zuciya.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Biri Da Kare
Edita@rumasau-kallamu










