Ga ta nan, ga ta nanku.
A can wani daji an yi wata raƙumar dawa mai suna Muwa. Ba ta da ɗa ko ɗaya. Kullum in ta dawo daga kiwo, sai ta yi ta kuka saboda rashin haihuwar nan. Cikin ikon Allah rannan sai ta haifi ‘ya’ya huɗu. Saboda murna ta raɗa wa babban cikinsu suna Muwa Muwa, mai bi masa kuma Caccikarimba, na ukunsu kuma Malaladumba.
Amma sai ta ƙi raɗa wa na huɗun suna, don ya fito a rame, ba ta son sa. Saboda yawan son ‘ya’yanta nata uku, sai ta gina musu ɗaki, ta saka su don kada ruwa da ƙura su taɓa su, amma sai ta bar ƙaramin a waje, ko ya mutu, ko ya yi rai, babu ruwanta.
Kuma sai ta ce wa ‘ya’yanta ukun: “Idan kun ji muryata, ku buɗe ƙofa; idan ba muryata ba ce, to kada ku buɗe.” Kullum idan ta dawo daga kiwo sai ta ce: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai su fito su sha, su koma.
Wata rana, Kura ta zo wucewa sai ta ji raƙumar nan tana cewa: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai suka fito suka sha, suka koma. Bayan uwarsu ta tafi, sai Kura ta zo bakin ƙofar da ƙatuwar murya mara daɗi ta ce:
“Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai yaran suka yi ihu, suka ce: “Ba muryar mahaifiyarmu ba ce.” Sai wannan abu ya sa Kura ta ji haushi ta bar wurin, tun kafin raƙumar ta koma wajen ‘ya’yanta.
Kura na tafiya sai ta haɗu da wani Biri mai ba da magani. Sai ta ce idan dai gaskiya ne yana ba da magani, to ya mayar da muryarta kamar ta raƙumar dawar nan. Sai Biri ya nuna mata yin haka abu ne mai sauƙi a gare shi, amma da sharaɗin ba za ta ci komai a hanya ba, domin idan ta ci, muryarta za ta koma kamar da.
Kura ta ce ta yarda. Sai Biri ya ba ta magani, da ta yi magana sai ta ji muryar kamar ta Muwa. Kura ba ta doshi ko’ina ba, sai wurin ‘ya’yan Muwa. Daga zuwanta sai ta ce: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.”
Sai suka buɗe ƙofa, sai Kura ta yi wuf ta cinye su, ta tafi abinta. Ashe ƙaramin da uwar ba ta so, watau ramammen nan, yana ganin ta. Can da raƙumar ta dawo ɗakin ‘ya’yanta sai ta yi kamar yadda ta saba: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.”
Sai da ƙaramin ya bari ta gama kiran su baki ɗaya, sai ya dube ta ya ce:”Muwa, Muwa ba ya nan, Caccikarimba ba ya nan, Malaladumba ba ya nan.” Sai uwar ta ce: “To, kai ɗin ma zo ka sha.” Sai ya je ya sha nononta, kuma daga wannan rana ta shiga son sa, har ya zamana in za ta fita kiwo sai su fita tare. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Bai kamata a nuna bambanci tsakanin ‘ya’ya ba, domin Allah kaɗai ya san mai amfani cikinsu.
- Wuya maficiya ce.
- Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
- Bora ya koma mowa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi
Edita@rumasau-kallamu










