Hukunce-hukuncen Raino

0
662

Idan aka samu saɓani tsakanin miji da mata, har ya kai ga rabuwa ga kuma ƙananan yara to akwai hukunce-hukunce na musamman da Suka haɗa da:

1- Lallai ne uwa ta ɗauki rainon ‘ya’ya in babu wacce za ta yi sai ita.
2- Amma idan akwai wata kuma ‘ya’yan ba za su cutu ba in an raba su da uwarsu, to ba za a tilasta mata ta raine su ba.
3- Bai halatta ba uba ya ƙwace ɗa daga hannun uwa ba, ba tare da wani dalili na shari’a ba. Yin aure ko rashin lafiya ko rashin tarbiyya yana daga cikin waɗannan dalilai.
4- Uwa ita tafi cancantar ta yin raino, sai kaka, ta ɓangaren uwa, sai innar ɗan, sai kaka ta ɓangaren uba, sai yar uwa, sai gwaggon ɗa, sai ‘yar ɗa, sa mai riƙo sai asibi.
5- Lallai ne mai raino ta kasance musulma, baliga, mai hankali, mara aure, wacce ta cancanci ta yi tarbiyya managarciya mai adalci.
6- Ya wajaba uba ya biya uwa ladan raino in ba tare suke ba.
7- Lokacin raino yana ƙarewa daga balagar namiji da aurar da mace.
Ina ba da shawara ga ‘yan’uwa da za su karanta littafin
“Tuhfatul Maudud” na Ibnul Ƙayyim (R.A).

Domin karanta cikakken bayani a kan Siffofin Masu Ba Da Tarbiyya danna nan.

Wannan bayani an  ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar ( Shehu Mansur Dala ) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHukunce-hukuncen Ƙananan Yara
Labarin na GabaSiffofin Masu Bayar Da Tarbiyya