Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege da ƙawarsa Kura suka fita farauta. Suna cikin tafiya, sai suka tarar da inda hanya ta rabu biyu. Hanyar da ta yi dama, doguwa ce, wadda ta yi hagu kuma gajeriya. Sai Kurege ya ce da Kura: “Tun da ke ce babba, sai ki bi doguwar hanyar, watau ta dama, ni kuma ƙarami in bi gajeriyar, wadda ta yi hagun.”
Kura ta ce: “A a, kai ƙarami ka bi babbar hanya, ni zan bi ƙaramar.” Sai ya ce: “To, shi ke nan mu tafi.” Kowa ya kama hanyarsa. Kura da ta bi gajeriyar hanya ba ta sami komai ba, sai wani ɗan ƙanzo. Da lokacin da za su haɗu ya matso, sai ta je inda suka shirya za su haɗu da Kurege, ta tsuguna tana jira.
Shi kuwa Kurege mai doguwar hanya, sai ya yi ta tafiya har ya gaji. Sai ya sami inuwar wata bishiya ya zauna yana hutawa. Da sanyin inuwa ya ratsa shi, sai ya ce: “Kai, amma wannan inuwada daɗi take.” Sai kawai ya ji bishiya ta ce: “Ai ma sai ka ɗanɗana ganyena ka ji irin daɗinsa!” Sai Kurege ya tsinki ganyen bishiyar nan ya sa a baki ya tauna.
Sai ya ce: “Kai, amma wannan ganye da daɗi yake!” Sai bishiya ta ƙara da cewa: “Ai don ma ba ka ɗanɗana cikina ka ji ba?” Sai Kurege ya tambaye ta ya ce: “Yaya zan yi in ɗanɗana cikinki?” Sai ta ce: “Idan kana so ka shiga cikina sai ka ce: ‘Buɗe bus’ sai ka shiga.
Idan ka ce: ‘Rufe kif’ bayan ka sha zumar, za ta rufe.” Kurege ya yi godiya, ya matsa kusa da bishiya ya ce: “Buɗe bus.”Tana jin haka sai ta tsage, Kurege ya shiga ya tarar da zuma ya zauna ya sha, har ta yi masa karo. Ya ɗebi wata kuma ya cika jakarsa. Da ya fito daga cikin kogon bishiya, sai ya ce: “Rufe kif.”
Sai bishiya ta rufe, ya yi godiya, ya kama hanyar zuwa inda suka shirya za su haɗu da Kura. Da ya isa inda suka yi alƙawarin haɗuwa da Kura sai ya tarar da ita tana barci. Ya shure ta, ta farka. Sai ta gan shi yana tanɗar baki, alamun ya ci daɗi, ta tambaye shi, “Kai, me ka samo ne mai daɗi haka?”
A cikin yanga da burga, Kurege ya ce da Kura: “Na samo wani abu ne mai daɗi, ke kuma fa?” Cikin nadama da mairairaita ta ce: “Ni kam ban samo komai ba sai wani ɗan kanzo. Yunwa ma nake ji. Ɗan ba ni abin da ka samo in ɗanɗana mana.” Sai ya ce: “Idan na ba ki a cikin jaka, za ki cinye har da jakar, amma bari in dangwalo miki.”
Kurege ya sa tsinke ya dangwalo zuma, ya miƙa wa Kura; ta karɓa ta sa a baki sai ta lumshe idanu da zaƙin zuma ya ratsa ta; sai ta cinye har da tsinken. Nan take fa sai kwaɗayinta ya motsa, ta ce da Kurege: “Gaya mini inda ka samo wannan zuma mai daɗi domin ni ma in je in samo.” Sai ya yi mata kwatancen bishiyar da ta ba shi zuma; Kura ta kama hanya.
Da ta isa ko hutawa ba ta yi ba, sai kawai ta tsunki ganyen bishiya ta sa a bakinta. Sai daɗi ya sa ta ce: “Amma wannan ganye da daɗi yake.” Da bishiya ta ji haka sai ta ce: “Ai wannan ma kaɗan ne, ba ki ɗanɗana abin da ke cikina ba.” Kura ba tare da ta tambayi yadda ake shiga cikin bishiyar ba, sai kawai ta ce: “Buɗe cikin in shiga in ci daɗin da kika faɗa.”
Nan take bishiya ta buɗe wa Kura cikinta, ta shiga ta fara warwason zuma, tana sha. Da daɗin zuma ya kwashe Kura sai ta fara wannan waƙar: “Buɗe bus, Rufe kif, Mu sha zaƙi, Kurege ba wayo, Nafi shi shan zuma, Zuma mai daɗi, Ke bishiya rufe kif.” Sai ko bishiya ta rufe.
Bayan wani ɗan lokaci sai ta ce da Kura: “Ki yi maza ki gama, masu ɗakin nan fa sun kusa dawowa.” Amma saboda wauta irin ta Kura, sai ta ce da bishiya: “Ba komai ko sun zo, ai ina da ƙarfin da zan kore su. Idan sun gan ni ma za su gudu.” Sai ta ci gaba da shan zuma. Ta sha ta ƙoshi, amma kuma ta mance abin da za ta faɗa ƙofa ta buɗe.
Tana cikin wannan hali ne fa kudan zuma suka dawo daga cin furanni. Suna shiga saƙarsu da ke cikin kogon bishiya suka tarar da Kura; nan take suka far mata da harbi, tana kuka da kugi irin wanda aka san ta da shi. Ta ruɗe, ta rinƙa cewa: “Kif, bishiya kif” maimakon ta ce: “Bus.” Can dai ta yi sa’a ta ce: “Buɗe bus.”
Bishiya ta buɗe, Kura ta fito da ƙyar, duk jikinta ya kumbura saboda harbin zumar da ta sha; sai ta kama gudu, tana haɗawa da waiwaye, ta doshi inda Kurege ke jiranta. Da Kura ta matsa kusa Kurege ya ga yadda jikinta ya zama, sai ya nemi sanin abin da ya faru.
Sai ta kwashe labari ta gaya masa; shi kuma ya ce da ita: “Kin cika mantuwa.”Haka dai Kura ta koma gida tana jinya.Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Rashin yin abu da kyakkyawar niyya shi yake sa yin nadama.
- Yin abu da zuciya ɗaya zai kawo taimakon Allah.
- Haɗama da rashin godiya ga Allah sukan sa a yi da-na-sani.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Tatsuniyar Sarkin Maƙera Da Dodo
Edita@rumasau-kallamu










