SHUGABANCI A WURIN HAUSAWA

0
5060

Shugabanci na nufin riƙon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan waɗannan.

Shugaba shi ne ƙololuwa a tsakanin al’umma, wato shi ne yake saman kowa, umarninsa ake bi, shi ne mai zartar da hukunci a tsakanin al’umma. A Ƙasar Hausa kuwa, akan samu sarki a matsayin shugaba, sai kuma ‘yan fadarsa waɗanda su ne masu taimaka masa wajen tafiyar da al’amuran jagorancinsa.

Shugabanci ta ɓangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali, inda maigida yake kamar sarki a gidansa, wanda shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zaɓi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jarumtaka da dauriya.

Wasu dalilai kamar halin ƙunci a cikin gida ko buƙata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani wuri na daban, kamar gona ko garke. Ta haka ne iyali kan yaɗu su yawaita su haɗa wani ƙauye. Saboda haka ne sai a ƙara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan ƙauye.

Wannan shi ya haifar da muƙamin Mai Unguwa, kuma shi zai rinƙa tsara musu dokoki.

Ƙauye yakan bunƙasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka, sai a ƙara zabar wani mutum a matsayin Mai gari (dagaci) domin kula da wannan gari. Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka ƙara yawaita, sai aka samar da muƙamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Mai gari aƙalla guda biyar, don ya kula da su. Da tafiya ta yi tafiya, sai aka samar da muƙamin Sarki, inda ake haɗa wa Sarki masarautar Hakimai aƙalla biyar ko fiye, domin ya shugabance su, ya kuma shimfiɗa musu dokoki domin zaman lafiya.

DOKA A ƘASAR HAUSA

Game da ma’anar doka kuwa, Neil Skinner (1980), ya bayyana cewa “Doka wata tsararriyar hanya ce da akan gindaya ta ga mutanen gari, da kuma horo ga duk wanda ya ƙetare ta don samar da tsaftatacciyar rayuwa ga wannan al’umma”.

RABE-RABEN TSARIN DOKA A ƘASAR HAUSA

Dangane da rabe-raben doka kuwa, masana sun raba su zuwa gida uku kamar haka;

  1. Doka a ɓangaren cikin gidan Hausawa.
  2. Doka a ɓangaren shugabanni.

iii. Doka a ɓangaren masu sana’o’in gargajiya.

Waɗannan su ne manyan rukunai ko azuzuwan da doka ta kasu gare su. Ga yadda bayanansu yake.

DOKA A ƁANGAREN CIKIN GIDAN HAUSAWA:

A gargajiyance, gidan Bahaushe yakan ƙunshi maigida da matansa, da ‘yan’uwansa, da kuma ‘ya’yansa. Iyali shi ne ainihin ginshiƙin da aka kafa al’ummar Hausa a kansa. Daga iyali ne jama’a kan faru, har su zama ‘yar ƙungiya, daga nan kuma su haɗu, su samar da ‘yar unguwa, waɗannan unguwoyi  su ne suke haɗuwa su kafa ƙauye, daga nan kuma sai garuruwa su samu.

A zaman iyalin Bahaushe, babba ne kan yi ƙoƙarin sadaukar da kansa, ya kyautatawa na ƙasa da shi. Shi kuma ƙarami ya yi masa biyayya, da kaucewa duk wani abu da ka iya kawo raini ga na gaba. To akasari za ka tarar irin wannan gida, gida ne na gado, wato wanda aka gada tun kaka da kakanni, kuma ba a raba shi ba. Sau da yawa irin wannan gida a tukunya guda ake girka abincin da za a ba wa kowanne.

A wani ɓangare kuwa, Kaka na wajen uwa ko na wajen uba, shi ne mai yin hukunci na farko a tsakanin danginsa, kuma shi ne zai faɗi abin da za su yi. Idan ka ga an jingine Kaka, to ya tsufa ne ko kuma ba shi da cikakkiyar lafiya, ko ta Allah ta kasance a kansa (ya mutu).

A wannan ɓangare ana yin amfani ne da doka, tana gaba da kai, don haka dole abin da na umarce ka, shi za ka bi, ƙi da so. A lokacin da maigida ba ya nan, wansa ko ƙaninsa, shi zai zama a makwafinsa, kuma ko mahaifi (Maigida) yana nan zai iya zama a makwafinsa, misali zai ce “Kai wane mun samu labari kana neman auren ‘yar gidan wane, ba za ka aure ta ba”.

Shi kenan ba ka da ta cewa, don yana cikin masu faɗa a ji a cikin danginku. Kuma sannan waɗannan ‘ya’ya, ba za su zama manya ba, ko da kuwa an yi musu aure, har sai sun hayayyafa. Kun ga kenan na gaba yana wucewa na baya na maye gurbinsa, shi ma wancan kakan a da jika ne na wani, ya zama ɗa, ya zama uba, kana ya zama kaka. Don haka, Kaka shi ne tsani na farko da za a taka wajen bin doka ta cikin gida.

Idan muka juya ɓangaren aure kuwa, Hausawa suna da al’adar wanda duk aka ba wa yarinya ta bayu, ko tana so ko ba ta so, dole ne su zauna tare. Haka shi ma mijin ba kasafai ake bari ya zabi wacce yake so ba, yana yin uhn! Za a ce “Kai! Da ubanninka za ka yi jayayya?.

Ko kuwa wannan ba ƙanin ubanka ba ne? Wato ba shi da iko a kanka kenan?”. Haka nan a kan dole zai zauna da wannan mata, in da rabo ma sai ka ga sun hayayyafa. Su ma idan suka tashi aurar da ‘ya’ansu irin wancan auren da aka yi musu (na zumunta) za su yi wa ‘ya’yansu.

DOKA A ƁANGAREN SHUGABANNI

Shugabanci a Kasar Hausa ya danganci riƙon ragamar al’amuran jama’a, wanda ya haɗa har da ba su umarni, da kafa musu doka, da sulhunta tsakaninsu da sauran haƙƙoƙinsu na yau da kullum. A ƙarƙashin wannan aji na ɓangaren masu mulki, muna da Sarki da Hakimi, da Dagaci (Fagaci) da kuma mai unguwa. Ga bayanin yadda kowanne daga cikinsu ke zartar da doka a ɓangarensa.

  1. MAI UNGUWA:

Shi ne sabon shugaban da talakawa suka zaɓa a yayin da suka fuskanci sun soma yawa, dole tafiyar sai da jagora, daga baya ne abin ya zama gado. To shi mai unguwa yana cikin masu kafa doka a bi dole, ko ya hana don ƙarfin mulkinsa, sai fa idan abin ya fi ƙarfinsa ne zai tura shi gaba.

  1. DAGACI (FAGACI):

Shi ne mutumin dake mulkar unguwannin dake ƙarƙashin masu unguwanni kamar biyar ko fiye, ana kiran sa Maigari saboda yankinsa ya fi ƙarfin unguwa. To shi ne mai zartar da hukuncin da ya gagari masu unguwannin dake ƙarƙashinsa.

  1. HAKIMI:

Ya samu wannan suna ko muƙami ne a yayin da aka  samu ci gaba, kuma garuruwa suka ƙara yawaita. Sai aka ba wa Hakimi garuruwan Fagaci aƙalla guda biyar don ya kula da su. To shi ma Hakimi idan abu ya ɗaure masa kai, yakan tura shi kai tsaye ga shugaban ƙasa na gargajiya (Wato Sarki).

  1. SARKI:

Shi ne shugaban ƙoli ga dukkan mahukuntan da aka yi bayaninsu a baya, shi ya sa ma wasu ke yi wa sarki kirari da “Bango madafar bayi”

DOKA A ƁANGAREN MASU SANA’O’IN GARGAJIYA:

Al’umma tamkar jikin ɗan Adam take, wanda baya ga aikin da kowace gaɓa ta yi don tabbatar da rayuwarta cikin inganci, akwai kuma gudunmawar da take bayarwa don kasancewar ɗan Adam ɗin jiki guda.

Ga kuwa sauran aikace-aikace da suke da muhimmanci fiye da saura, waɗanda in ba a yi su ba, sai ta kai ga katsewar rayuwa. Wannan siffa ta al’umma, ta tilasta wa kowa daga cikin jama’arta yin wani aiki, domin tabbatar da wanzuwar al’ummar, ba ya ga wasu aikace-aikace da suka zama dole ga kowa, domin rayuwarsa shi kansa.

Sarakuna a kowanne gari, sun bai wa shugabannin sana’o’i da manyan bokaye, da jarumai har ma da dattijan gari matsayi na musamman, wajen gudanar da mulkinsu. A haƙiƙa ma, bincike ya tabbatar da cewa waɗannan rukunonin jama’a ne suka zamo mataimakan Sarki, wajen tafiyar da mulkin yankinsa.

Don haka, a gargajiyance ana zaɓar dattijon da ya fi kowa yawan shekaru da ƙwarewa a kan sana’ar da mazauna wurin suke yi. Irin sana’o’in da ake da su a wancan lokaci sun haɗa da Noma, Kiwo, Ƙira, Jima, Saka, da sauransu.

Bisa ga tsarin zama na gargajiya, Hausawa sun amince da zaman cude-ni-in-cude-ka. Kowane mai sana’a, yakan yi la’akari da cewa, kamar yadda yake buƙatar wasu abubuwa don nasarar sana’arsa, haka ma wasu ke buƙatar wani abin daga gare shi.

Wannan fahimtar tasa kowanne mai sana’a yakan yi fiye da abin da yake buƙata, ta yadda zai iya amfana daga abin da ya saura, don mallakar wasu abubuwa da ba zai iya yi da kansa ba.

Misali, Manomin dake bukatar wuƙa, ko fartanya, ko lauje, sai ya ɗauki hatsinsa ya kai ga Maƙeri. Haka shi ma maƙerin zai ba da garma ko takobi don a yi masa yaɓe ko jinka ko ɗinki. Da haka sai ka ga kowa ya samu biyan buƙatarsa, kuma rayuwa ta sauƙaƙa, wannan, nau’in ciniki shi ake kira cinikin furfure.

Amma ko ba a faɗa ba, irin wannan rayuwa, tana buƙatar kowa ya yi aiki tuƙuru, tare da nusar da mutum zuwa ga yin tsimi da tanadi na abin da ya yi saura don gaba. Wannan ya sa tsarin tattalin arziƙin Hausawa ya ginu a kan sana’o’insu.

To idan kuma ya kasance a ɓangaren sana’a kamar ga mahauta ne, wani ya ci bashin dabbar wani ya ƙi biya, to shi wanda aka ci bashin nasa, ba zai ja wancan da rigima ba, a’a sai ya tafi wajen Sarkin Fawa ya yi ƙararsa.

Shi kuma Sarkin Fawa, zai tura ɗaya daga cikin fadawansa su yi kiran wanda ya ci bashin, a nan za a kashe rigimar, ko Sarkin Fawa ya biya, ko a yi wa wanda ake bi bashi lamuni ya kawo. To, haka ma abin yake ga sauran masu sana’o’in gargajiya da suke da sarakuna.

Domin karanta cikakken bayni akan Hausawa da al’adunsu ko kuma asalin kalmar Hausa da ma’anarta danna koren rubutu nan

labarin da ya wuceASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA
Labarin na GabaYadda Ake Wankan Soyayya