Kalmar Bahaushe tana da ma’ana ta fuskokin harshe, al’ada ko gado, siyasa, addini, wurin zama (muhalli) ko xabi’ar mutum.
Ta fuskar harshe, shi ne wanda harshensa na farko (L1) Hausa ne, kuma ba ya jin kowanne harshe sai Hausa, ita ce harshensa na mu’amalar yau da gobe (Bunza, 1990).
Ta fuskar gado, shi ne wanda iyayensa da kakaninsa Hausawa ne, koda shi ba ya jin Hausa (Bunza, 1990).
Ta fuskar siyasa, Bahaushe shi ne wanda ya zauna ko aka haife shi a qasar Hausa na sama da shekara ashirin, koda iyayensa da kakaninsa ba Hausawa ne. Wannan jimawar za ta ba shi damar amfani da harshen, da xabi’a irin ta Bahaushe. Ta wannan fuskar, sauran qabilu ma na iya zama Hausawa (Manby, 2016).
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
Ta fuskar addini, wasu na ganin wanda ba ya addinin Hausawa, ba Bahaushe ba ne, shi ya sa Hausawa kan cewa ‘yan uwansu da ba su karvi addinin Musulunci ba da suna: Maguzawa (jam’i), Bamaguje (namiji), Bamagujiya (mace) (Bunza, 1990).
Ta fuskar muhalli (wurin zama), Bahaushe shi ne wanda yake zaune a qasar Hausa (Bunza, 1990 da Adamu 1978) Smith (1970) duk mutumin da yake rayuwa a qasar Hausa daga a qarni na 15th a lokacin garuruwan Hausa sun kafu shi ne Bahaushe, sannan harshen Hausa ne babbar alamar da za a iya gane Bahaushe da shi.
Ta fuskar xabi’a, Bahaushe shi ne wanda ya tasirantu da al’adun Hausawa suka yi tasiri a rayuwarsa ta yau da kullum, koda ba Bahaushe ba ne (Bunza, 1990 da Adamu 1978).
Wasu kuma na kallo Bahaushe da fuska uku, Have, Hausa-Fulani (Kaxo) da Banza. Havawa su ne asalin Hausawa waxanda suka haxa da qabilun Gobirawa, Kabawa, Rumawa, Adarawa da Maouri sune masu mulki qasar Hausa kafin zuwan Jihadin Fulani da Shehu Usman Xanfodiyo (Omniglot, 2015)
Hausa-Fulani, asali mutanen kudancin Nijeriya ne suka qirqiro kalmar, don dunqule al’ummar Hausawa da Fulani saboda alaqar kut-da-kut tsakanin Bahaushe da Fillace. Fulani na zaune a qasar Hausa ta dalilin auratayya, kiwo, kasuwanci ko neman ilimi tun kafuwar Daular Sokoto. Waxannan Fulanin suna jin harshen Hausa sosai, kuma sun xabi’antu da xabi’ar Bahaushe, daga cikin qabilun Fulani akwai; Jovawa, Dambazawa, Mudubawa, Mallawa da Sulluvawa da suke da asali daga Futa Toor, ko Fouta Djallon ko Wolof (yanki da ke tsakanin Senegal da Mauritania a yau).
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Su kuma Banza jikokin Karaf-da-Gari ne mazauna garuruwan da jikokin Bayajidda suka kafa. Su Hausawa ne da suka haxu da wasu qabilun mazauna Illorin (tare da Yarbawa), Gwarawa, Ajawa, gere, Bankal da wasu. Sune idan suka yi magana da karin harshensu ake ce musu ‘gwarawa’, ko ‘bagwari’.
A yau, abu ne mai wuya a samu asalin Bahaushe, saboda autayayya tsakanin wasu qabilu, hakan na nufin sauyin halitta, yanayi da kama, Bahaushe ya yi auratayya da Fulani, Nupe, Kanuri, Shuwa, da sauran qabilun Kudancin Nijeriya. Bahaushe a yau, haxuwar qabilu ce daban-daban, da ke rayuwa Arewacin Nijeriya, Kudancin Nijar, da sauran sassan duniya (Malumfashi, 2018).