Masana da dama sun soki alaqar tarihin Bahaushe da zuwan Bayajidda, domin Bahaushe yana rayuwa a yankinsa tun kafin zuwan Bayajidda a 900s.
Bayajidda ya tarar da Hausawa da garuruwansu Daura, Garun Gabas, Gaya, Gobir da Katsina. Misali, Katsinawa suna da tarihi tun shekaru 3,500 baya, tun zamanin Adawa wanda aka bayar a cikin Alqur’ani Mai girma (Suratul Fajr, 89:6). Zamfarawa na rayuwa a yankinsu tun kafin kafuwar Daular Gobirawa. A Masarautar Daura kuma,
kuma an yi magajiya goma sha bakwai (17) da suka yi mulki kafin zuwan Bayajidda.
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
A yankin Saltolo, Bayajidda ya tarar da garin Gaya, sannan Bagauda xan Gobir ta qasar Gobir (ta jihar Niger a yau) ba, a’a, yanki ne mai daula da ta shuxe da ta haxa da yankin Hausawa (Maguzawa) na yau tun kafin zuwan addinin Musulunci.
Bawo jikan Bayajidda a yankin ya tarar da garuruwan Adirani, Shemi da Barka ta qasar Kazaure tun kafin ya ya sari wuri a Saltolo, wato Kano a yanzu (Gusau, 2008).
saboda waxannan da ma wasu dalilai, masana tarihin qasar Hausa ke ganin rashin ingancin tarihin Bayajidda, wasu na xaukarsa a matsayin ‘tarihihi’ (jirkitaccen tarihi), saboda kasa tantance qarya da gaskiyar dake cikinsa (Yahaya da wasu, 1992).
Bayajidda asalin sunansa Sa’id Abdurrahman ana masa laqabi da ‘Abu Yazid’ xan Sarkin Baghada Abdallah da sarauniyya Zida/Zidams (Palmer, 1928), ya samu sunan Bayajidda daga kalmomin ‘ba ya ji da’, ma’ana, a da ba ya jin harshen Hausa. Aigbokhai (1971) Bayajidda mutumin Baghadaza ne (Iraqi) ne da ya yi hijira tare da mutanensa saboda savani da ya samu da mahaifinsa. A wata ruwayar, wani Sarki ne Ziyxuwa ya yaqi Bagadaza, ya fatattake su, sai Bayajidda da mutanensa suka taho kudu, wato Afrika (Adamu, 1997).
A wata ruwayar kuma, Bayajidda Babar ne, an haife shi 884 a birnin Gao, Tademekket ta qasar Tunusia, asalin sunansa Makhlad ibn Kaidad al-Zanati. Bayajidda ya shigo yankin Nubiya da Misira, tafkin Chadi, Ngala, sai kuma sauqa a Borno, a lokacin ba a ce mata Borno, sai Gazargamu.
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Mai mulki Barno a lokaci ya ji labarin zuwansa yankinsa, domin ya kuvuta daga sharri kwace masa gari, sai ya gabatar masa da auren ‘yarsa Magaram (Palmer, 1928). Zaman Bayajidda da tawagarsa a Borno ya taimakawa Mai Borno sosai wajen cin wasu garuruwa da yaqi. Bayan wasu shekaru, sai Mai Borno ya yi shirin kashe Bayajidda saboda tsoron kar ya kwace masa mulki. A nan wani bafade ya sanar da Magaram abin dake shirin afkuwa da mijinta, ita kuwa ta sanar da shi don ya gudu.
Bayajidda ya gudu a tsakiyar dare tare da matarsa da wani hadimi guda xaya, ya yi yamma, inda ya yi tafiyar wata takwas. Bayajidda ya yada zango a Kunar Yadagammu ta Garun Gabas (da ke Masarautar Haxejia a yanzu). Zaman Bayajidda a Garun Gabas, ya kafa makarantar allo a arewa da gari, amma bai jima sosai a Garun Gabas ba saboda ya ji labarin Mai Borno ya sa a nemo shi, a kamo shi, ko a kashe shi, sai ya fice daga Garun Gabas a tsakar dare, ya bar matarsa Magaram da ciki. Bayan tafiyarsa ne Magaram ta haihu a nan Garun Gabas, aka sa wa xan suna Biram.
Alasan (1932 – 1996) Bayajidda ya doshi yamma, har ya isa garin Gaya (ta Kano a yanzu) ya tarar da mutanen Abagiyawa (wurin da asalin mutanen Kano suke da), ya tarar da suna sana’ar qera makamai, a nan aka qera masa takobi wanda da shi ya kashe maciyar rijiyar kusugu.
Bayan wasu kwanaki a garin Gaya, Bayajidda ya qara gaba, ya doshi yamma har ya isa garin Daura a daddare ta kofar gabas. Da Bayajidda ya iso zo garin Daura, ya tarar har an rufe qofar, sai ya kama bishiya, ya dirqa, ya buxe qofa ya kaxa dokinsa ya shiga gari, har ya isa gidan wata tsohuwa, mai suna Ayana, ya nemi ta ba shi ruwa; sai ta ce masa ba a samun ruwa, sai sati-sati, ana wasu waqe, saboda dodanniyar macijiya4da take hana mutane xibar ruwa, duk wanda ya sava dokar xibar ruwa, takan fito ta sari mutum, ta kashe shi.
Bayajidda ya matsa mata da sai ta ba shi abin xiban ruwa, dattijuwa ta ba shi, ta nuna masa inda rijiya take. Bayajidda ya kama hanya ya je, tare da dokinsa. Ya ce ana qiran maciyar da ‘Doddanniyar Kusugu’.
leqa rijiya, sai ya ga macijiya a ciki, sai ya ja da baya, ya xaure dokinsa, ya jefa abin xiban ruwa, macijiya ta kama abin xiban ruwa, sai ya zaro takobi yana jiran macijiya ta fito, tana leqo kai, ya sare mata kai, ya cire shi ya sa a burgaminsa, ya koma gidan Ayana, ya bata ruwa, ya ba ta labarin macijiya (Alasan & Palmer, 1932: 136)
Da gari ya waye, mutane suka fito aka tadda macijiya a waje nan-da-nan labari ya karaxe gari, ganin ba ita ce ranar fitowarta ba. Sarauniyya Daurama ta haxa mutane za a je a ba wa Doddanniyar Kusugu haquri, aka taho ana kaxa Dajinjin (ganga), ana waqe. Suna isa wurin, sai suka tarar, ashe ma kashe ta aka yi, har an cire mata kai.
A nan Sarauniyya Daurama ta bada sanarwa, duk 5da ya kashe maciyar nan, ya bayyana kansa, za ‘qauran’ ta raba garin Daura biyu, ta ba shi ya mulki rabi. Mazaje suka fita daji suna ta farautar macizai suna zuwa da kawunansu, duk wanda ya zo aka gwada, sai a ga bai yi daidai da kan macijiyar ba.
A qarshe Ayana ta zo, ta labarta musu cewa, Bayajidda; wani mutumi ne da ‚ya hau sa‛ (doki) ne ya kashe macijiya. Daga nan wasu ke ganin aka samo kalmar ‘Hausa’. Sarauniyya ta sa a qirawo shi, ya zo da kan maciji, aka gwada, aka ga shi ne.
Sarauniya Daurama ta ce za ta ba shi rabin gari, shi kuma ya ce ita yake so da aure, ba rabin gari ba. Da farko, sarauniyya taqi amincewa, saboda a al’ada, sarauniyya ba ta aure6(Smith, 1970). Sai Daurama ta ba
shi kuyangarta Azna, har suka haihu da Bayajidda, Azna ta roqi Bayajidda ya sa wa xanta suna ‘Karaf-da-Gari’, Daga nan aka samu laqabin sarautar Qaura a qasar Hausa in ji Alasan xan Sarki Abdurrahman (1912 – 1966). Miji yana iko akan mata, ita kuma Sauraniyya kowa qasana yake Smith (1970).
Ma’ana, xan kuyangar gari, ya zo zai karve gari. Ba xauki lokaci mai tsayi ba, ita ma Sarauniyya ta haihu, sai ta sa wa xanta suna ‘Bawo’, ma’ana; mai dawo da gari.
Bayajidda ya zauna a Daura a matsayin mijin Sarauniyya ne, ba sarki ba. Ya kuma mutu a shekarar 947 Miladiyya a garin Daura, yana xan shekaru 63. Bayan kwanaki ita ma Daurama ta rasu, sai xanta Bawo ya karvi sarautar Daura, ya gaji mahaifiyyarsa. Bawo shi ne magajin garin Daura namiji bayan shafe shekaru mata suna mulki.
Domin Karanta Asali Da Muhallin Bahaushe Danna Nan
Yadda aka kafa garuruwan Hausa kuma, a lokacin mulkin Bawo an sami matsanarciyar yunwa, har ta kai mutane na qaura zuwa yankin Santolo (Kano a yanzu) domin neman abinci. Kasancewar a yanki ba wani kyakkyawan jagoranci, an sami ta’addanci sosai, mai qarfi ke da ikon kwace, da muzgunawa mutane.
Sai aka kai magana gaban Bawo, ya yi fidda tsarin jagoranci domin kula al’amura, sai Bawo ya naxa ‘ya’yansa guda shida domin kulawa da yankunan. Gunduwa a Zazzau, Bagauda a Kano, Kumayo a Katsina, Uban Doma a Gobir, Gazori a Daura, Zaman Kogo a Rano da kuma yayansa Biram a yankin gabas (Garun Gabas ta masarautar Haxejiya a yau), wannan shi ne silar samun garuruwan Hausa-Bakwai.
Su kuma ‘ya’yan Karaf-da-Gari, an tura su yankunan da ake qira da Banza-Bakwai, sune yankunan: Kabi, Yawuri, Zamfara, Illorin, Nupe, Kwararrafa (Jukun) da Gwari (Adamu, 1997). An ce, daga sunan mahaifiyyar Karaf-da-Gari ‘Azna’ aka samu kalmar ‘arna’, shi ne ake cewa masu bin addinin gargajiyya na jikokin Azna, da ‘ya’yan arna.
Wannan shi ne tarihin Bayajidda a taqaice.