Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wani mutum a wani ɗan ƙauye yana da mata da ’ya’ya. Ana nan, sai ɗaya daga cikin matansa ta haifa masa yarinya kyakkyawa. Bayan kwana bakwai sai ya raɗa mata suna Kwambal. Sannu a hankali, kwanci-tashi, yarinyar ta girma, kyanta ya ƙara bayyana, har ya kasance duk garin ba mai kyau kamar nata.

Da ta isa aure sai mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa neman aurenta, wancan ya zo, amma sai ta ƙi, haka aka yi ta fama amma babu wanda ya yi nasarar samunta. Kwatsam sai wani yayanta, wanda suke ’yan turaka, mai suna Dawi ya ce zai aure ta. Da Kwambal ta ji niyyarsa, sai ta ƙi ta ce yaya za ta auri wanda suke ubansu ɗaya da shi?

Shi ko Dawi da man ɗan baiwa ne. Wata rana sai ya ɗauke ta a kan raƙumi suka tafi cikin wani ƙungurmin daji ihunka banza, inda babu mutane. Ashe da man ya ja ta dajin ne domin ya nuna mata hatsabibancinsa ko ta ji tsoro ta aure shi. Da fari ya rikiɗa, ya zama wani babban baƙin maciji, mai gemu da jajayen idanu da ’yan kunne.

Sai ya fasa kai, ya ƙura mata jajayen idanunsa masu kama da garwashi, ya ce ta yarda ya aure ta, ko kuma ya cinye ta. Ita ko da kafewa, sai ta ƙeƙasa ƙasa ta ƙi. Da ya ga haka, sai ya zama wani dodo mai haƙora gatso-gatso da farata masu tsawo da kaifi da kofatai a ƙafafunsa. Yana cikin wannan hali ya sake cewa ta yarda ta aure shi, ko kuma a bakin ranta.

Ita kuma ta sake kafewa faufau, ta ƙi. Haka dai ya rinƙa rikiɗa, yana fito mata a kamanni da halittu daban-daban masu ban tsoro don ta ji tsoro, amma ta ƙi yarda, har ya gaji. Sai ya dube ta ya sanar mata da aniyarsa ta komawa gida ba tare da ita ba, watau zai bar ta a dokar dajin nan tun da ta ƙi yarda.

Yana gama gaya mata haka, sai ya kwantar da raƙuminsa, ya ɗare, ya karya akala, raƙumi kuwa ya kama tafiya. Da ta ga ya bar ta, sai ta gyara muryarta tattausa, mai daɗin sauti da ratsa rai, ta kamawaƙa tana cewa:

“Dawi ɗan’uwana,

Ɗora ni a kan raƙuminka.”

Da ya ji wannan waƙa, sai ya mayar da waƙa yana cewa:
“Ki ce ni mijinki ne,
In ɗora ki a kan raƙumi.”

Sai ta mayar masa a cikin wannan baitin:
“Ba ni iya faɗa, Kai dai ka ɗora ni a kan raƙumi.”

Duk da waƙoƙin da suke yi, bai tsaya ba, ita kuwa ta rinƙa binsa tana yi masa waƙa da magiya ko ya ɗauke ta ya kai ta gida, amma sai ya ƙi, ya yi tafiyarsa shi kaɗai. Da ta gaji, sai ta zauna a gindin wata bishiya tana kuka. Can sai wani dodo ya ɓullo. Tana ganin dodo ta razana, ta yunƙura za ta tashi ta gudu.

Da dodo ya ga haka sai ya buɗe bakinsa mai feshin wuta da hayaƙi ya ce da ita: “Idan kika gudu zan cinye ki yanzun nan.” Tana jin haka sai ta tsaya. Da dodo ya ga kyawunta sai yace mata: “Idan kin amince kika aure ni, zan kai ki gidanku, amma idan kika ƙi zan cinye ki.” Da ta ga ba mafita, sai ta yarda ya aure ta.

Suka tafi gidan dodo, ta dangana, ta zauna da shi. Suna nan, har dodo ya tambaye ta irin abincin da takan ci, sai ta ce nama ta fi so. Duk yayin da ya fita farauta sai ya kaso namun daji ya kawo mata nama da yawa. Duk dare ’ya’yan dodon sai su fara cewa suna jin warin mutum, kuma suna so su ci naman mutum.

Ita tana can inda babansu ya ɓoye ta. Da zarar ta ji irin wannan magana ta ’ya’yan dodo, sai ta wurga musu irin naman da ubansu ya kawo, sai su ɗauka su tafi. Kullum haka take fama da su. A can gidan su Kwambal kuwa, baƙin cikin duniya ya dami mahaifiyarta, kuma tuni ta shiga cigiyarta, har wata rana ta haɗu da tattabara.

Bayan sun gaisa da tattabara, sai ta tambaye ta ko ta ga ’yarta Kwambal? Da tattabara ta ji wannan tambaya, sai ta kaɗa fuffuke, ta dubi gyatumar Kwambal ta kaɗa baki ta ce: “E, na ganta amma tana gidan dodo suna zaman aure.” Jin wannan labari ya ƙara tayar da hankalin uwar, nan take ta ɓarke da kuka.

Can dai ta daina kukan, ta share hawaye ta dubi tattabara ta ce da ita: “Akwai kuwa yadda za a yi a kuɓutar da ita daga hannun dodo?” Tattabara ta ce: “E, akwai wata dabara. Tun da dodon yana da gashi, a aika wa Kwambal cewa ta gaya masa za ta yi masa kitso a gindin kuka.

”A cikin ƙagara uwar Kwambal ta ce: “To daga nan fa?” Sai tattabara ta ci gaba da bayani: “Idan ta yi ƙananan tsoraye sai ta nuna masa daga nan kuma sai ta ɗebi gashinsa mai yawa ta ɗaure shi da shi a jikin kuka. Idan ta ɗaure shi bajau, sai ta tashi ta kama hanyar gari da gudu”

Da uwar Kwambal ta ji wannan shawara sai ta ji daɗi, ta yi wa tattabara alƙawari idan ’yarta ta kuɓuta za ta ba ta tukuici mai yawa. Sai tattabara ta tashi sama ta kama hanya har gidan dodo, ta sauka a kan ɗakin Kwambal, ta fara waƙa tana kiran sunan Kwambal tana cewa:
“Kin yi tagumi ’yar auta,

Ki daina kuka ’yar autar iya,

Idan ya dawo ’yar auta,

Ki kai shi gindin kuka ’yar auta,

Ki yi masa kitso ’yar auta,

Ki kitsa ƙanana ’yar auta,

Ki nuna masa ’yar auta,

Ki ɗebi mai yawa ’yar auta,

Ki ɗaura a jikin bishiyar kuka ’yar auta,

In ya ɗauru ki kama hanyar gida.”

Ta rinƙa maimaita waƙa har Kwambal ta fara jin waƙa sai ta fita. Ta saurari waƙar tattabara da kyau sai ta fahimci bayanin tattabara. Washegari da dodo ya zo ɗakinta sai ta ce za ta yi masa kitso amma a gindin kuka, sai ya yarda ya fara jin daɗi matarsa za ta yi masa kitso.

Suka tafi gindin bishiyar kuka ta fara yi masa kitso, idan ta kitsa ɗan siriri sai ta nuna masa sai ya ji daɗi, idan ta ɗebi gashi mai yawa sai ta ɗaura a jikin bishiya har ta gama yi masa kitso. Da ta ga daɗin kitso ya sa ya fara gyangyaɗi, sai ta yi sanɗa ta janye jikinta ta fara gudu ta kama hanyar gari.

Da ya farka sai ya hangi matarsa na gudu, idan ya yunƙura zai tashi sai ya ji kansa a ɗaure a jikin bishiya. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kuɓuce amma sai abu ya gagara. Ita kuwa Kwambal tana ta sheƙa gudu ba ta tsaya ba har ta isa gida. Haka ta bar dodo ɗaure a gindin bishiyar kuka yana ta birgima. Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • So amanar zuciya.
  • Sabo da maza jari.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)
Labarin na GabaTatsuniyar Dagaci Da Malaminsa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.